← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 180

Sashe 23

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen karfe hudu na yamma Khaleesat ta tashi daga baccin da take, bandaki ta shiga ta wanke baki sannan tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tun wayewar gari babu abinda ta ci har zuwa sannan, rabonta da abincin kirki zae yi kwana uku yau tun dai faruwar incident din few days ago, bayan ta idar da sallah ta shirya cikin kaya marasu nauyi ta fito parlor ta tafi kitchen ta hada shayi kawai sannan ta koma dakinta, laptop dinta ta jawo ta kunna zata saka movie ko zata
an samu nutsuwar abubuwan dake damun ta a rai ta hanyar kallon film, daga karshe ma ta fasa kallon ta dauko takardunta ta fara karatu, nan ma taji bata fahimtar komai a karatun, rufe takardan tayi ta kwantar da kanta gefen gado ta lumshe ido with different thoughts running her mind, it's not as if she is disturb don Abdul bai daga kiranta ba ko bai kirata ba, kawai dai bata ma san abinda ke damunta bane in particular, bayan lokaci me tsawo ta sauke ajiyar zuciya ta bude idonta ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, status taga Abdul yayi updating few hours ago, ta bude hoton da yasa taga har ya ma koma Nigeria cause a field din kwallo yayi hoton da abokansa dukkansu sanye da jersey, ko kadan bata yi mamakin komawarsa Nigeria ba don zai ma iya abinda yafi hakan, da taji shiru har kwana uku dama ta zargi ya koma, dai dai nan taji an bude dakin that is opposite her's, sosai gabanta ya fadi don tun ranan sae yau Housemate din nata ya zo gidan, ta kalli agogon wayarta taga karfe biyar har ya gota, ta ajiye wayar ta dago kanta, tana ta zaune har bayan 15 mins da shigarsa daki sai kuma ta mike tsaye tana jin jikinta ba karfi ta dau gyalenta tana tafiya a hankali ta nufi kofarta ta bude ta fito corridor, sai kallon kofar dakin nasa take gabanta na faduwa, ta rasa courage din karasawa bakin kofar, she stood der for some minutes daga karshe ta lumshe ido ta bude tana tafiya slowly ta isa bakin kofar nasa ta tsaya, ta kai hannu tayi knocking a hankali kamar tana tsoron kofar, komawa gefe tayi kamar mara gaskiya waiting for his response, jin shiru bai amsa ba ta sake knocking din a hankali, ta jira for like a minute again taga dai ba a amsa ba, babu abinda yayi crossing mind dinta sai ko yana bacci ne, but bacci da yamma haka? handle din kofar ta kai hannu gently without thinking twice ta bude kofar tana kallon cikin dakin with throbbing heart, a edge din gadon dakin ta gansa a duke yana operating laptop dinsa da alamar abinda bai gama ba ranan da ya bar gidan yake karasawa, ya daga kai ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abinda yake yi, she felt really really bad, ashe yana ma jin tana knocking din, da tasan yana ji ya kyaleta da bazata fara bude kofar dakin nasa ba, ya mike tsaye yace "Good evening Halysaah" Taki amsawa kuma taki yarda ta kallesa, da kyar tace "Dama kana ji kaki amsawa?" Har muryarta ya fara rawa, ya
an bude ido yace "To na sani ko saurayinki ne Halysaah?" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta juya ta bar bakin kofar ta kullo masa dakin ta koma nata, dukawa yayi ya ci gaba da abinda yake yi a laptop, tana komawa daki ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, she felt really hurt kuma tayi da ta sanin zuwa dakin nasa, tana nan a yanda take har shidda saura sannan taji yayi knocking kofar dakinta gently, daga kai tayi tana kallon kofar sai kuma ta hade rai, lkci daya ya bude kofar tare da sallama, sai dai daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta yace "I was trying to finish a power point Housemate, how are you doing?" Ta sauke idonta a takaice tace "It's fine" Yace "Baki je makaranta ba yau?" Ta gyada masa kai looking toward a different direction, yace "Why?" A takaice tace "Ba komai" Yace "Ok, hope everything is okay?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa sai kuma ta dauke kai don kar ma ta fara kukan dake taruwa idonta, bayan like 10 seconds yace "Saurayin da ke maki fada a waya ne guy din nan ko?" Ta kasa cewa komai at first, sai kuma muryarta na rawa tace "Kayi hakuri da abinda ya faru" Ya
an buda ido yace "No it's fine Halysaah, ai ba ma abinda ya faru, but where did you know him from?" Tayi shiru ta kasa cewa komai tana share hawayen idonta, yace "I am intruding ko?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "Ohk can we talk if you are comfortable Halysaah" She kept mute Kamar me nazari, can kuma a hankali tace "Ohk" yace "Then meet me at the parlor" Daga haka ya juya ya fita, ko da Khaleesat ta fito parlon bata tarda sa ba a ciki, ta zauna kan kujeran parlon tunani iri iri na yawo a kanta har ta rame a kwana ukun nan, bayan some minutes sae gashi ya fito daga kitchen with a cup of coffee, ya karaso cikin parlon ya zauna yana kallonta yace "You look pale Housemate, are you okay?

Ko ya maki wani abun ne?" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tace "He left immediately u left too" Yace "Oh really?

That's weird" Ita dai tayi shiru, ya
an yi murmushi ya ajiye coffee din hannunsa yace "Amma baki ci abinci ba" Nan ma tayi shiru tana kallonsa, yace "Naga kamar its been a while da kika yi girki a kitchen, so me kike ci a gidan?" Ta sauke idonta, he could see tana cikin damuwa sosai, yace "Tun ranan da ya tafi bai dawo ba kenan?" Tace "Um" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "Do u mind me taking u out for dinner?" Kallonsa Khaleesat take babu ko kiftawa kuma bata ce komai ba, ya mike yace "Get ready, let me get my car key" Yana fadin haka ya mike ya tafi dakinsa ta bi sa da ido, Khaleesat ta fi minti uku zaune parlon tana contemplating on weather to go out with him or not, what if Abdul bai bar kasan ba kawai old picture yayi uploading a status dinsa?

The thought of this sent her quivers all over, Tana cikin wannan tunanin sai gashi ya fito daga dakinsa, yana shigowa parlor ta mike ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce dakinta, canza kaya tayi ta dau veil dinta ta yafa sannan ta zauna gefen gado tana tunane tunane iri iri, bayan 15 mins da shigowarta dakin taji yayi knocking yace "Baki shirya ba Halysaah?" A hankali ta mike ta dau wayarta ta nufi kofa ta bude ta fita, ta samesa har ya koma parlor yana jiranta, tana isowa parlon yana kallonta yace "Where u contemplating inside the room?" Bata san sanda ta dan yi murmushi ba bata dai ce masa komai ba, yace "To mu je, this is after 6 already" Shi ya fara nufar kofar fita living room din sannan ta bi bayansa, yana tsaye bakin kofar bayan ya fita ya jira har ta fito daga parlon sannan ya kulle kofar yana kallonta yace "Why this much Deodorant Housemate?" Ta wani kallesa tace "Ni nace maka na sa?" Bai bata amsa ba ya nufi garage tana biye da shi a hankali, ita dai bata sa turare yanzu ba sai tun wanda ta saka da tayi wanka daxu, sai in ko kamshin kayanta yaji amma ba dai ita ba, bude mata motar yayi tun bata karaso ba sannan ya zaga ya shiga motar yana jiranta, bayan ta shiga suka bar Garage din, wani babban restaurant sananne ya kai ta a Baltimore, bayan yayi parking ta dinga kallon restaurant din da ta ga an rubuta The Capital Grille, sai da ya fara sauka daga motar sannan ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga ciki, shi yayi offering dinta seat bayan ta zauna shi ma ya zauna ya dau food Menu dake saman table yana nuna mata na kusa da ita yace "Ki duba abinda za ki ci" Ita dai bata dau Menu din ba, yace "I am talking Halysaah" Without looking at him tace "Ko ma meye zan ci" Yace "Ohk" Tana danna wayarta yayi masu ordering abincin, mamaki Khaleesat ta dinga yi ganin amount of different type of foods that he ordered kamar za ayi karamin feast a wajen, abinci kuma masu tsadan gaske, da yawa cikin abincin da aka kawo masu sai a ranan ta fara ganinsu, duk da dai abincin turawa ne, drink ma ya kusa kala hudu ya siya masu, ta daga kai ta kallesa a karo na farko tace "Su waye za su cinye duk wannan?" Orange Crush ya dauka yana sha bai ce mata komai ba, after a while ganin bata fara cin abincin ba shi kuma sai cin abinda zai ci yake ya daga kai ya kalleta yace "Ko babu abinda kike so a nan ne?" A hankali ta dau Tacos daya, shi ko ya ci gaba da cin abincinsa,
asa
asa Khaleesat take kallonsa, ta lura yanda baya wasa da bacci haka baya wasa da abinci, because he didn't even mind she was in front of him abincinsa kawai yake ci sosai, ganin ko kallonta baya yi ta abincin gabansa kawai yake yasa ta
an saki jiki kadan ta fara cin abincin duk da ba sosai ba, ta ci iya abinda zata iya ci ta dau drink tana sha a hankali, sai a sannan ya daga kai ya kalleta after almost finishing his food yace "Ko dai a maki packaging abincin ki ci a gida, naga kamar kina kunyan ki ci abinci cikin mutane, or should i give u privacy?" Tana kallonsa a hankali tace "Privacy in an open restaurant?
Chapter 23 · 0% Book details