← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 180

Sashe 76

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

In dai daga gidan radio da talabijin ku ke ni dai na amince ku zo ku dau muryata da fuskata in nemi taimakon al'ummar musulmai ku watsa ni duniya ta gan ni ina jawabi, kilan gwamna ma in ya gani yaji tausayina ya saka baki a sakar min
a na" Jay yace "Ba sai anyi haka ba Kaka, ina tabbatar maki nan ba da dadewa ba zai dawo gida in sha Allah" Nenne tace "To daga ina ku ke?

Ko dai kungiyar kare ha
in en Adam ne" Jay ya
an yi shiru, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun yi cirko cirko a tsakar gida suna gwale ido suna kallon Jay, Jay yace "Makarantar mu daya da Halysaah a can Amurka, shi ne muka samu labarin abinda ya faru mu ka zo" Nenne ta mike da sauri tace "To ai yau kusan sati daya kenan ana neman ta ko sama ko kasa, wallahi bamu san inda take ba, ita uwar ta na daki tana jimamin ta, ni kuma ina nan ina jimamin
a na, haka muka raba abun, amma tun da yarinyar nan ta samu labarin daurin aurenta da annoban nan Awdul ta shiga duniya, wallahi bakina da nata tace min bata son sa bazata iya auren sa ba, tun da uwata ta haifeni ban ta
a ganin inda ake auren dole ba" Nenne na kai wa nan ta fasa sabon kuka, Jay dai ya ma rasa abinda zai ce mata, beside baya ma son yayi magana gaban su Mama Zubaida da suka wangale kunnuwa suna saurare, kawai ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu ashirin din da yayi saura, yaje har gaban Nenne ya mika mata da ladabi yace "Ga wannan Kaka, in sha Allah za mu shigo gobe" Nenne ta daga hannu da sauri tace "A'a, gwara ku hada kawai ku kai furson a sako min
a na, don yafi min ko wani kudi a duniya" Jay yayi murmushi yace "Ki amsa kaka, na maki alkawarin za a sako sa nan ba da dadewa ba in sha Allah" Nenne ta amshi kudin da hannu bibbiyu tana sa masa albarka cikin rawan murya tace "In ma Allah ya sa kun zo gobe ba ku sameni a nan ba ku sa a raka ku gidana babu nisa daga nan" Yana murmushi yace "In sha Allah Kaka" Daga haka yayi mata sallama sannan ya fita daga gidan su Mama Zubaida suka bi sa da kallo babu fara'a ko wacce da abinda ke yawo a ranta, Nenne ta kulle kudin a habar zaninta ta soke tace "Dama gobe da asuban fari zan je gun Malam Na ta'ala, Allah ya sa in samu kwale kwalen da zai tsallakar da ni da sassafe" Dakin Umma ta nufa tace "To ke Salame kike ko wa?

Ki fito mana ki shigar mata da dukiyar nan dake bakin kofa kar a faki ido a sungume mata wani abun, kayan abinci ai dukiya ce me zaman kanta a yanxu, Allah kadai yasan dubu dari nawa suka kashe wajen siyo kayan abincin nan...." Maman Salame ta fito daga dakin Umma ta fara shigar da kayan abincin ciki, Mama Shatu ta shige dakinta fuska a murtuke, Mama Zubaida ma ta tabe baki ta shige nata dakin ta sako tsumman labulenta dake rataye da kyauren dakin.

Jay na fita waje ya tarar da Ajay cikin mota yana zaune a kujera me zaman banza ya kwantar da seat din kujeran idonsa a lumshe, Jay ya bude driver seat ya shiga yana kallon Ajay jin yanda ya kure AC din motar gaba daya, Ajay ya gyara zamansa yana kallonsa, Jay dai yayi murmushi ya fara driving motar Ajay ya nuna masa hanyar da suka bi suka fita ranan da yayi dropping Khaleesat, motar dake bayan su ma ya bi su, Ajay sai sake kare ma unguwan kallo yake with distress har suka isa main road, bayan sun hau saman titi ya kalli Jay yace "In za a samu gida ko na 30M zuwa 50M ne a siya pls su bar wannan vicinity din" Jay yace "I think that will be okay idan anyi releasing mai gidan but not now" Ajay yace "Duk daya ne Bruh, plss kayi ma Salisu magana a fara duba gidan daga yau zuwa gobe, that house isn't healthy for a living thing, ta yaya me rai zai dinga rayuwa a gida irin wannan?

This is so pathetic, or am i exaggerating pls?" Jay yace "But haka kawai baza mu yanke decision without the release of the head of the House ba, so kake mu kara triggering saurayin nata bayan har yanxu ba mu yi achieving ko abu daya ba, we are following everything step by step Ajay, we will reach der in sha Allah" Ajay bai sake cewa komai ba, amma da gaske hankalin sa ya tashi kwarai ganin condition din cikin gidan most especially the compound, in ba dole ba shi kam babu abinda zai sake kai sa gidan nan, it's not about the house structure or where it's located but the hygiene of the house, sai kace cikin prison, ji yake kamar har ya kamu da cholera don har wani zazzabi zazzabi ya fara ji, ya kai hannu ya rage Ac din motar, shi dai Jay driving dinsa kawai yake.
Chapter 76 · 0% Book details