← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 180

Sashe 75

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Jay na zaune tare da Ajay a office din lauyansu suna sauraron sa, lauyan yace "He is trying to re-litigate a case already resolved in court, don an riga an rufe case din a kotu tunda yace ya yafe, har lauyoyinsa sun yi filing notice of discontinuance kuma kotu tayi approving sannan ta kulle case din ta yi releasing debtor dinsu from any further liability, but like seriously ban san wani irin lauya bane
an sa, don har da written confirmation of debt forgiveness da suka yi a kotu duk yana nan, why let them arrest the man again?

Ko dai
an nasa bai gaya masa consequences din hakan da yayi bane cause this is pure abuse of process and malicious prosecution" Jay yace "To yanxu meye abun yi Barrister?" Lawyern ya ajiye pen din hannunsa yace "Za mu yi Filing motion to dismiss the already forgiven case, and we will plead abuse of process, sannan muyi Raising estopped from pursuing the debt again in near future, just that za mu yi presenting documentation of the original debt forgiveness and court records to the court, wannan ma ai sun yi breaching court order ne kuma hakan laifi ne me zaman kansa" Ajay yace "That is because suna ganin ba shi da wanda zai tsaya masa ko shekara nawa zai yi a kulle, his family have no voice to do so, that was why the breached the court order for their selfish interest" Lauyan yace "Babu matsala in sha Allah za mu shigar da kara kotu, and the man will be bailed out while the case is going on, they will even have to pay him damages...." Bayan la'asar Ajay yayi parking a kofar gidansu Khaleesat, dai dai inda yayi parking ranan da suka yi dropping dinta da daddare, a bayansu kuma wata mota ce ita ma tayi parking, Guard uku ne suka fito daga cikin motar dukkansu suka yi tsaye jikin motar da suka sauka, shi dai Jay kallon unguwan kawai yake, Ajay ya bude mota ya sauka, ya jingina da motar ya rungume hannunsa, Jay ma ya sauko sannan ya zagayo inda Ajay yake tsaye yace "Where is the house?" Ba tare da Ajay ya k
allesa ba yace "Gashi nan kana kallo" Jay ya kalli gidan dake opposite dinsu, wani almajiri ne ya zo wucewa Ajay ya kirasa, yaron ya taho da sauri Ajay yace "Shiga cikin gidan can kace ana sallama da Maman...." Sai kuma ya kalli Jay alamar ya fadi sunan, Jay na kallon almajirin yace "Kace ana sallama da Maman Halysaah" Almajirin yace "Toh" Da sauri ya nufi gidan, Ajay yace "Meye kuma Halysaah?

How is that even a name?

In zaka kira sunanta na asali kawai ka kira" Jay na kallonsa yace "Meye sunan nata na asali?" Ajay bai kallesa ba har sannan yace "Ka fi ni sani ai, tunda ka fi kusa da ita" Jay ya
an yi murmushi bai sake ce masa komai ba, Nenne ce ta leko kofar gidan tana zazzare ido kuma bata yarda ta fito waje ba, tana yin ido hudu da su Jay sannan ga wasu samudawa da ta gani har uku tsaye jikin wata motar ta juya ta koma cikin gidan da sauri har tana tuntube, sai ga Mama Zubaida tana gyara gyalenta da ta yafa akan daurin kirjin da tayi, Mama Shatu na bayanta tana kokarin saka hijabinta ta bai bai, tsaye duk suka yi daga cikin gidan suna leko su Ajay da samudawan dake jikin mota a tsaye, Mama Shatu tayi karfin halin cewa "Ina wuninku?" Jay ne ya karasa har inda suke tsaye, shi dai Ajay na rungume da hannunsa yana kallon ikon Allah, Jay ya gaishesu duk suka amsa kamar munafukai suna gwale ido, Jay yayi kasa da kai yace "Mahaifiyar Halysaah mu ke son gani" Da sauri Mama Zubaida tace "A'a to ku shigo mana, Bismillan ku ai tana ciki, fakewa kawai suka yi da cewar bazata iya fitowa ba bata da lafiya, lafiyarta lauz ku shiga har dakin ku sameta" Duk tunaninsu an zo tafiya da Umma ne kamar yanda aka zo aka tafi da Malam Ali, Jay ya juya ya kalli Ajay dake jin duk conversation din su daga inda yake tsaye, ko ba a gaya masa ba yasan stepmom din Khaleesat ne matan, ya kulle motarsa yana kallon wa enda ke tsaye jikin mota yayi masu alamar da cewar za su fito in 5 mins sannan ya karasa har inda Jay ke tsaye yana jiransa su shiga gidan, su Mama Zubaida kuwa har sun koma tsakar gidan sun tsaya cirko cirko suna jiran su ga yanda za a shigo a fitar da Umma, da hannu suka nuna ma Jay da Ajay hanyar dakin Umma, Jay ne yayi sallama bakin kofar dakin, shi dai Ajay na tsaye a gefe yana kallon white t-shirt dinsa to be sure ruwan ta
on da yayi gaja gaja a compound din bai fallatsar masa a jiki ba, Mama Shatu da Mama Zubaida a tsakar compound din suke zubar da duk wani ruwan da suka yi aiki haka ma yaransu, sun maida compound din kamar na mahaukata, gashi simintin da aka masa duk ya dagargaje ya kusa komawa kasa, shi yasa in suka zubar da ruwa sai ya cabe, kudaje sai safa da marwa suke ta ko ina, ga kwanuka gaja gaja, igiyoyin gidan kuwa duk an rataye kaya, Ajay na ganin Jay ya shiga dakin Umma shi ma ya shiga ciki da sallama, dukawa Jay yayi daga bakin kofar ya gaida Umma da Maman Salame dake dakin, Ajay ma yayi hakan ya gaishe su, ganin haka Maman Salame ta tashi da sauri ta shimfida masu darduma a kan ledan dakin tana masu sannu da zuwa, duk tunaninta ita ma zuwa aka yi za a tafi da Umma amma sai bata ga alamar hakan a tattare da su ba duba da yanda suka yi gaisuwa cikin girmamawa, Jay ne kawai ya zauna kan darduman Ajay kuwa ya kasa zama ga wani zafi da yake ji a duk jikinsa, ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan goshinsa, Mama Salame ta dau mafici ta mika masa, ya
an yi murmushi ya amsa yace "Nagode" Mama Salame ta dage labulen dakin tana cewa "Yau mun fi sati biyu basu kawo wutan ba, ance tiranspoma tayi bindiga" Nenne dake makale kofar bandaki rike da buta ta dinga leka dakin Umma bayan Maman Salame ta daga labulen, haka su Mama Zubaida da suka ji shiru ba a taso keyar Umma an fito da ita ba, Jay na kallon Umma dake zaune don ko ba a gaya masa ba yasan ita ce mahaifiyar Khaleesat duba da kalan fatarta sannan babu ta inda Khaleesat ta bar ta, ba karamin kama Khaleesat ke yi da mahaifiyarta ba a nan ta samo asalin kyanta, Yayi kasa da murya yace "Ya jikin Umma?" Cikin sanyin murya Umma tace "Alhamdulillah da sauki" Ajay ma yayi mata ya jiki ta amsa tana kallonsu gaba daya don jira kawai take taji me ke tafe da su, in ma cewa za su yi tafiya suka zo yi da ita dama a shirye take tunda hijab dinta na jikinta, shiru ne ya biyo baya a dakin, don Jay bai san ta inda zai fara introducing kansa ba ma, haka ma Ajay da yayi shiru zafi na neman hallaka sa, after few seconds Ajay yayi karfin halin breaking silence din a hankali yace "Makaranta daya mu ke tare da Jidderh a can America, so kawarta ta sanar mana abinda ke faruwa shi ne muka nemi ta bamu address mu zo nan duba ki" Sosai hankalin Mama Salame ya kwanta jin abinda Ajay yace, Mama Salame tace "Allah yayi maku albarka, kuma mun ji dadi mun kuma gode da zuwan da ku ka yi" Jay ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Umma kuma ki kwantar da hankalinki, muna tabbatar maki in sha Allah komai zai wuce nan ba da dadewa ba, don za ayi duk abinda ya kamata, mahaifinta ma in sha Allahu za mu yi abinda ya dace a sakesa a yan kwanakin nan, ita kanta Halysaah zata dawo gida in sha Allah" Maman Salame ta daga hannu sama cike da farin ciki tace "Alhamdulillah ya Allah, gaskiya mun ji dadin jin hakan daga gare ku, don bamu da wanda zai tsaya mana sai Allah, Alhamdulillah" Ita dai Umma kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ajay yace "Zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Mama Salame tace "To Allah Ubangiji ya kai mu goben lafiya, mun gode, mun gode" Mikewa Ajay yayi ya kara yi ma Umma sallama sannan ya fita daga dakin kar yayi suffocate, heat wan finish prince, don in akwai abinda baya shiri da shine zafi, baya son zafi ko yaya yake, Nenne na ganin Ajay ya fito daga dakin Umma ta sake komawa cikin bandaki da sauri, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi sa da kallo har ya fita daga compound din, to su waye wannan kuma su da suka baza ido da kunne su ga an fito da Umma tana kuka, bayan fitar Ajay da few minutes sai ga almajirai suna shigowa gidan da buhun shinkafa biyu, carton din taliya biyu, carton din indomie biyu, manyan gallon na manja da mangyada, da carton din maggi duk kuma aka dinga dire su a kofar dakin Umma, daga Nenne har su Mama Zubaida haka suka saki baki suna kallon ikon Allah, Maman Salame ta taso zuwa bakin kofa tana kallon kayan abincin da mamaki tace "Ikon Allah, har da uban hidima haka??" Jay ya ajiye ma Umma 100k yace "Gashi Umma ayi cefane da wannan, in sha Allah gobe za mu shigo da izinin Allah" Bai jira cewar Umma that was speechless and shock ba ga hawayen dake sauka idonta kawai ya fita daga dakin.....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
*Hmm don't even know where to start from
Khaleesat's Citadel ku sani Billah ina yinku
Nagode Nagode da abun arziki, Allah Ubangiji ya bar mu tare, Allah ya kara maku arziki ta yanda bakwa zato, Allah ya raya maku zuri'a ya baku zaman lafiya da mazajenku, wa enda basu da auren cikin ku Allah ya fiddo maku da mazaje na gari, yanda ku ka faranta min yau ku ma Allah ya faranta maku, thank you soo much Meenah parrot for bringing about the idea and the wonderful Souls that supported it, Allah ya kara mana hakurin zama da juna yan Citadel dina
HALYSAAH 37
Jay na fitowa dakin Umma, Nenne dake tsaye tsakar gida bayan ta fahimci ba yan sanda bane ta rushe da matsanancin kuka ta nemi er kujera ta zauna tana kallonsa tace "Da wannan uban kudaden da ku ka kashe na siyo kayayyakin abincin nan ai da belin
a na ku ka yi, wallahi maraya ne ba shi da kowa, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya rube a can, wancan karan ni kadai nasan wahalan da na sha na ganin an sako sa, babu inda kafata bata shiga ba wallahi, na dinga bi gida gida ina neman taimakon kudi" Jay ya kwantar da murya yace "In sha Allah za mu yi bakin kokarin mu na ganin an sako sa kaka, ki kwantar da hankalin ki" Nenne na matsar kwalla da gefen ha
ar zaninta tace "
an nan ina hankalina zai kwanta
a na na can furson?
Chapter 75 · 0% Book details