← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 180

Sashe 66

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

misaltuwa don tun dauke mahaifin Khaleesat dama ta fara alalan siyarwa don mu rufa ma kanmu asiri saboda an jarin da nake da shi nima duk ya karye bani da komai, kafin ma a dawo da mahaifin Khaleesat kano sau uku muna zuwa gidan Alhaji Musa a Nassarawa GRA domin mu basa hakuri ko zai dubi halin da muke ciki ya taimaka a sake mana Baban Khaleesat amma duk aka mana koran kare, na farko masu gadi ne suka kore mu, na biyu Matarsa ranan ta rako ba inta ta gan mu tayi mana cin mutunci ni da yayata da Baaba Gaje ta sa aka kore mu, na uku kuma an cikinsa Abdul wanda dama shi kadai ne namiji a 'ya yansa, ana haka aka shiga kotu ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka kawo Malam Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan, to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai na ganesa da na gansa a kotun don ranan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara tunda Malam Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, haka aka dage shari'ar zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa, Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotun tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama'an wajen kallonta suke, Alhaji Musa babban mutum ne kuma me kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani an jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke ara ce Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda bakin jama'a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abinda za ayi akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar kotu ranan rai babu dadi muka koma gida, bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake 'ya yan su maza kanana suna fita almajiranci suna ciyar da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna sana'a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shigo gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari, Baban Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa don shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat" *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 , it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500* Alhamdulillah!
Chapter 66 · 0% Book details