← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 180

Sashe 132

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Meemah ce ta shigo dakin Momy tana mika mata wayar hannunta hankali tashe tace "Momy kin gane wacece wannan kuwa?" Momy ta ajiye bowl din farfesun hannunta ta amshi wayar tana kallon screen din, can ta kalli Meemah tace "Wannan ba er matsiyatan can bace?

Khaleesat take ko wa" Meemah ta zauna gefen gado har sannan fuskarta dauke da tashin hankali tace "Ita ce Momy, ita da Aymaan" Momy ta ajiye wayar ta dau bowl din farfesunta ta ci gaba da ci tace "Waye kuma Aymaan?" Meemah tace "Aymaan din kuma kika manta yau Momy, Muhammad Aymaan
an mataimakin gwamna fa" Momy ta kalleta tace "Wai tsohon saurayin ki Muhammad?" Meemah ta hade rai tace "Tsohon saurayi fa kika ce Momy, Aymaan din ne tsohon saurayina?" Momy tace "To in ban ce maki tsohon saurayin ki ba ya zan ce, yaron da ba
aga kiranki yake ba yanxu, yaushe rabon ki da shi? kin ga kuwa ai sai in ce tsohon saurayin ki Meemah, dama ai a titin Instagram din ku ka hadu da shi, ba sai da na dinga hada maki da rokon Allah ba kika samu sassaucin son sa da kika dora ma kanki, dama su biyu zuciyarki ta makale ma da shi da wani
an sarki yake ko wa shi ma kullum sai kin isheni da zancensa bana ma tunanin kina da numbersa, duk samarin ki a Instagram din ku ke haduwa kuma a can ku ke rabuwa, ni na ta
a ganin wannan wahala" cike da damuwa Meemah tace "Wallahi mace ce ta shiga tsakaninmu da Aymaan Momy, amma ai ya so ni kamar ran sa, ki tuna har fa kano ya sha zuwa wajena" Momy ta tabe baki tace "Amma ai ba gidan ubanki yake zuwa ba sai dai yace ku hadu gidan cin abinci ko wani wajen, bai ta
a biyo ki yaga gidan ku ba, shekara kusan takwas ana abu daya in da gaske son naki yake me ya hanasa fitowa har yau, ni dama tun da Malam Tasi'u yace min bazai fa aureki ba na hakura da kashe kudina a iska, amma ai na kashe kudi kan wannan Aymaan din, bayan Malam Tasi'u ma akwai wani malamin da yace min mu hakura ba auren ki zai yi ba bata maki lokaci kawai yake, kuma uwarsa ma a tsaye take kyam" Meemah tace "Momy duk ba wannan ba, a ina yasan yarinyar nan har suka yi hoto tare?

Kinsan shi ma a Amurka yake kuma makarantar su daya amma ya gama degree dinsa tuntuni in dai ba masters ya koma yi ba, kuma wnn hoton daga gani a Amurka aka yi sa" Momy tace "Atoh kika san ko tsohon hoto ne, dama ai kin ce iskanci ta dinga yi a Amurkan don haka ba abun mamaki bane don kin ga hotonsu tare, yanxu kuwa ai sai dai tayi karuwancinta da yan Mariri" Meemah dai ta kasa cewa komai amma kana ganinta kasan hankalinta ya tashi sosai, Momy ta kalleta tace "Ai kun ma fi shekara biyu baku yi waya da shi ba ko?" Meemah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Yanxun ma ina ganin hoton na kirasa bai daga ba, amma ni abinda ya bani mamaki duk yanda yake da mace fa baya posting dinta ko a WhatsApp balle har Instagram" Momy tace "
an wani gari ne ma?" Meemah tace "Gusau" Momy tace "Abdul ya san sa ne?" Meemah tace "Oho, shi wannan ana sanin cikinsa ne, ni ban san ko sun san juna ba, kuma ai Abdul bai san ni da Aymaan ba tunda kinga ba wai ya ta
a zuwa gidanmu bane Aymaan din, sai dai su san juna a Instagram amma ba a sarari ba" Meemah ta kara Zooming din hoton da kyau tana kallon tsadadden Abayan jikin Khaleesat ga wani kallo da Aymaan ya kafeta da shi, ita kuwa tana dariya with her beautiful set of teeth, Meemah ta fice daga wajen hoton ta sake dialing number Aymaan amma har ya katse bai daga ba, mikewa tayi ta nufi kofa, Momy ta tabe baki tace "To ke banda abunki me zai yi da er talakawa aka ce maki, in kin bibiya hoton ya dade, yanxu kuwa ina taga hanyar zuwa Amurka, ai uwarsa ma ta fi mu
in talakawa bari ki ji in gaya maki, a zamanin yanxu dai ko wani me kudi ya waye baya yarda ya hada zuri'a da talaka, yanxu kwarya tabi kwarya kawai, haka abun yake" Ita dai Meemah ta fice daga dakin tana sake dialing number Aymaan with confusion.

Tana zaune usual spot din da suke zama a school tana jiran Safiyyah da taje kai ma wani coursemate dinsu laptop dinsa, tun daxu take zaune wajen tana danna wayar hannunta with full concentration, lkci daya ta dakata da abinda take yi a wayarta jin wani kamshin turaren da ta sani ya doki hancinta, waige waigen wajen ta fara yi suna hada ido bata san sanda ta saki wayar hannunta ba zuciyarta na bugawa tana kallonsa babu ko kiftawa, he was the least person she is expecting to see in her life, lkci daya taji wani courage ya zo mata ta dau wayarta fuskarta a daure ta mike da nufin barin wajen, ya fixgo gyalen jikinta yana kallonta da kyau yana murmushi yace "You think i will let you just like that Khaleesat?

Har kin samu masu ci gaba da sponsoring din ki an dawo dake America, ga shi har ana hoto dake ana dora ki a Instagram, u snapped a picture together with Aymaan har yayi posting din ki duniya ta gani, ko wani
an iskan gaye kin sani a Amurka and they are all ready to go through any mile for you, to ki sani na maida aurenmu da ke, you are still my wife...." A firgice Khaleesat ta farka daga baccin da take ta mike zaune jikinta na rawa, tun da uwarta ta haifeta bata ta
a mummunan mafarki irin wannan ba, ta sauka daga saman gadonta har sannan jikinta na rawa, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana ganin abun kamar ba mafarki bane gaske ne, ba karamin tashin hankali ta shiga ba ta fara karanto duk addu'an da ya zo bakinta tana kuka, duk yanda ta so ta samu nutsuwa hakan ya gagare ta, she was really shock, da kyar ta daure ta dauko wayarta ta kunna data hannunta na rawa, kawai taji she wants to speak with her Housemate, tana bude data taga Aunty Farida ta ajiye mata sako, ta shiga DM dinta taga hoton da suka yi da Aymaan ta turo mata tana tambayar wanene shi, kuma me yasa zata yi hoto da shi....

Tashin hankalin Khaleesat ya ninku akan wanda take ciki da, she was so confuse and shock, gashi jikinta sai rawa yake, a ina kuma Aunty Farida taga hoton nan, ta shiga uku, shikenan kilan Abdul ma zai gani kenan mafarkinta ya tabbata ya zamto gaskiya?

Ta fashe da matsanancin kuka tana jin zuciyarta kamar zai fito tsabar tashin hankali, ko reply din Aunty Farida bata yi ba ta fita daga WhatsApp din ta fara dialing number Housemate dinta da sauri, ta kirasa har sau biyu bai daga ba, rasa yanda zata yi tayi tana kuka, can kawai ta fara dialing number Safiyyah har sannan jikinta bai dena rawa ba, yana fara ring Safiyyah tayi picking, cikin rawan murya Khaleesat tace "Safiyyah baki ce ma mutumin nan ya goge hotona a Instagram ba dama??" Safiyyah tace "A'a na masa message ta WhatsApp he is not online fa, na kuma kirasa bai yi picking ba, kuka kike yi ko me?

Haba Khaleesat sai kace warce tayi wani mugun abu?

Get together fa kawai muka je aka yi hoto ba wai club ba, kuma shigar ki ta mutunci kika yi fa, Aymaan kuma left a reasonable distance tsakanin ku balle ace ko manne maki yayi a jiki" Khaleesat taki bata amsa tace "Kina da number Ya Junaid pls?" Safiyyah tace "Eh kamar ta numbersa Jawwad yayi min fowarding receipt din 10M da aka tura ma su Maman Abdul" Da sauri Khaleesat tace "Don Allah ki turo min yanxun nan" Safiyyah tace "Ohk bari in duba, amma ni dai wallahi ban ga abun damuwa ba don kawai Aymaan ya daura hoton ki a Instagram, sanannen Celebrity ne shi fa, kawai don bama Instagram ne shi yasa baza mu sani ba, kuma kawai don dai kina Iddah ne da ace kin gama so what??
Chapter 132 · 0% Book details