← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 180

Sashe 42

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama wani ne zai aure ki ba ni ba ashe?" Ta kasa ce masa komai lkci daya hawaye ya cika idonta, duk tsiyar da yake mata da yaga hawaye idont
Khaleesat ta kusa minti sha biyar a bandakin cikin tashin hankali da confusion, banda kuka babu abinda take yi, she can't even think straight tsabar yanda ta shiga tashin hankali, to ko dai kawai ta fita ta gudu ta bar gidan ne, ko kuma taje ta basa hakuri ya rufa mata asiri, ta ma san bazai ta
a sauraronta ba, da kyar ta mike daga durkushen da take hawaye sosai na zuba idonta har sannan jikinta rawa yake, gani take kamar the world have come to an end for her, hannunta na rawa ta wanke fuskarta tayi karfin halin bude kofar bandakin a hankali tana leka Bedroom dinta, zaune ta gansa edge din gado yana danna wayarsa, suna hada ido ta bude kofar ta fito, ya dinga kallonta daga sama har kasa, hakan yasa ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, Mikewa tsaye yayi yana mata wani kallo yace "So you just wasted my time all this while ba wankan kike ba dama?" tears was just rolling down her cheek tana girgiza masa kai muryarta na rawa tace "Don girman Allah kayi hakuri, kar kace zaka...." Dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu, tuni ta ja bakinta tayi shiru tana kallonsa a tsorace ganin yanda lkci daya yanayinsa ya canza, tana ganin ya nufota ta juya zata koma bandakin da gudu yayi saurin fixgota, ta rushe da kuka sosai tana cewa "Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri Ya Abdul" Yana mata wani kallo yace "You think i will just waste my time and money coming here at the end in kyaleki da childishness dinki in koma Nigeria?

You must be joking, In kika ga na kyaleki yau sai in faduwa nayi na mutu" Zuwa sannan Khaleesat bata ma san kalmomin dake fitowa bakinta ba ta dinga basa hakuri a rikice, ta dai san ko da wasa bazata ce zata yi kokuwa da shi ba, ta ina ma zata fara, da hannu daya in ya riketa ko kwakkwaran motsi bazata iya ba balle ta kwace kanta, Knocking kofar da ta jiyo a kunnenta ne yasa ta zaro ido bakinta na rawa tace "Wallahi Housemate dita ce ta dawo kuma bata da makulli nata ya
ata..." Yace "And so what?

Ita zata hanani abinda nayi niyya ne?" Hawaye na sauka idonta tace "Don Allah ka bar ni in bude mata kilan mantuwa tayi, she is not spending the night here" Saketa yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Remain here, i will open the door for her" Gyada masa kai kawai take zuciyarta na bugawa da karfi, ya dau rigarsa ya saka sannan ya nufi kofa ya fita, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana jin kamar numfashinta zai dauke tsabar tashin hankali, gashi sai knocking kofar parlon ake babu kakkautawa, da sauri ta mike jikinta na rawa ta bi bayansa tana shesshekar kuka at the same time tana tunanin to wa ke kwankwasa kofar Allah Ubangiji ya sa Housemate dinta ne, nan corridor ta makale don tuni har Abdul ya isa kofar parlon zai bude, ya murda makullin ya bude kofar, Khaleesat couldn't believe who she saw standing at the doorstep, ai bata san sanda ta karaso parlon da sauri ba hawaye na sauka idonta, Abdul dake kallonsa daga sama har kasa Calmy yace "How may we help you?

Who are you looking for?" Maimakon wanda ke bakin kofar ya basa amsa kawai ya bi gefensa ya shigo parlon yana kallonta yace "Why did you call my line?" Da mamaki Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta ta lumshe ido, bata san sanda wani relieve ya zo mata ba lokaci daya, ta sake jin muryarsa yace "Me yasa kika kirani?" Ta daga kai ta kalli Abdul ganin irin kallon da yake mata at the same time ya nufo inda take cikin zafin nama, ganin haka ta fara komawa baya cikin rawar murya tana kallon AJ tace "I need you to help me pls" Ko rufe baki bata yi ba taji Abdul ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta, AJ could not believe what he just saw cause bude baki yayi at first, ganin ya kara sauke mata wani marin cikin few seconds AJ ya isa gaban Abdul sending him double fist a fuska, he took Abdul unaware don bai gama recover daga fist din ba ya kara masa wasu ukun a jere, kan kace me ya fara punching dinsa kamar an aikosa, Rikicewa Khaleesat tayi da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku plss stop it" Tana matsowa kusa da su zata rike AJ da ya wani hankadata sai da ta fada kan kujera, Dai dai sanda aka bude kofar parlon Jay ya shigo, buda baki yayi ya jefar da wayar hannunsa saman kujera ganin Abdul a hannun AJ kamar ya samu punching bag, AJ gave Abdul no single space to retaliate, dukansa kawai yake kamar suna gidan dambe, Jay ya nufesu da sauri yana kiran AJ, da kyar ya samu nasaran rabasu yana ma AJ tsawa yace "Are you out of your mind Junaid?

Are you mad, Meye haka?" Jay bai rufe baki ba Abdul ya koma kansa da fist din da bai samu yi ma AJ ba, ai ko ya kara ja ma kansa wani dukan wajen AJ, Jay that was shock at the attack Abdul just attacked him ya bude baki yana kallonsu, kar AJ yaje ya ma Abdul illa su shiga uku ya sa Jay ya kara rike AJ, Abdul that was beaten blue black ya nufi kitchen kamar mahaukaci vowing to unalive AJ, Khaleesat tsabar shock ko motsin kirki bata yi a inda AJ ya wurgar da ita, Jay na ganin Abdul ya shiga kitchen yasan makami kawai yaje daukowa, ya kalli Khaleesat da sauri yace "Tashi ki tafi daki" Ai kamar jira take ko rufe baki Jay bai yi ba ta mike a guje tayi Corridor ta tsaya tana zare ido, Jay ya fara jan AJ su tafi daki amma AJ yaki yana cewa "Don babansa me yake takama da shi a Nigeria?

Who the F is he?

Kakkaryasa zanyi in karya banza wallahi, in ya cika shege mu hadu a Nigeria" Jay yaki biye AJ haka dai ya ja sa har corridor zai shigar da shi daki, sai ga Abdul da wuka ya nufo su kamar
an daba, ai ko karasa shigewa dakin basu yi ba Khaleesat ta riga su, tuni Jay ya sa ma dakin Key ya zare makullin ya saka a aljihu don tsaf yasan AJ sai yace zai bude kofar ga makami hannun Abdul, Abdul ya dinga bubbuga kofar saying all sort of abusive words at the same time yana alkawarin sai ya ma AJ illa, AJ ya tafi jikin window ya tsaya yayi crossing kafa yana kallon kofar dakin, Jay dai ya zauna gefen gado looking speechless and confuse, sai kuma ya dafe kirjinsa da ya fara masa ciwo saboda fist din Abdul, ita dai Khaleesat na rakube jikin gado hawaye na sauka idonta tana kuka a hankali, banda bugawa da karfi babu abinda zuciyarta ke yi, taji muryar Abdul na cewa "Ke kuma sai na maki abinda har ki koma ga mahaliccinki baza ki mance ba, i will make sure you become useless and miserable, i promise you this, kasar nan kuma kamar kin bar sa don karatun ki ya zo karshe" Khaleesat ta kara sautin kukanta, Ajay ya daka mata tsawa yace "I will fling you out of this room in baki rufe ma mutane baki a nan ba" Jay ya wani kallesa, ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba kukanta kawai take, after a while ko ina yayi tsit a gidan ko tafiya Abdul din yayi oho, da kyar Khaleesat ta mike bayan kusan minti goma zata dau hijab dinta, Jay ya bi ta da kallo, bayan ta saka Hijab din ta juya suka hada ido, sauke idonta da ya kumbura don kuka tayi, sai kuma ta tafi ta dau karamin towel da ta gani gefen gado seeing traces of blood in Jay's lips, bandaki ta tafi ta jika towel din da ruwan dumi sannan ta dawo dakin without looking at him ta duka gabansa ta dafa gadon ta fara goge masa lip dinsa a hankali, AJ ya wani kallesu sai kuma ya tabe baki ya kauda kai yana kallon outside of the window, Jay dake kallonta yace "Thank you Halysaah" Ita dai bata ce komai ba kuma bata yarda ta hada ido da shi ba ta mike ta tafi bandaki da towel din, AJ ya juyo yace "Kai Malam bani makulli in bude kofar nan in fita" Mikewa Jay yayi ya nufi kofar ya fara budewa a hankali, AJ ya bi bayansa incase of necessity, yana bude kofar AJ ya rigasa fita at the same time being very conscious of everywhere in the house, both angle and corner, a haka ya fito parlon Jay ma that was at alert na biye da shi a baya amma fa sai da ya kulle kofar dakin da makulli sbda Khaleesat, and they realized Abdul ya fice daga gidan, AJ ya juya ya kalli Jay yace "Dau wayarka mu tafi gida" Jay yace "You think i can just go and leave her in here?" AJ ya masa wani kallo yace "How sure are you u are safe being in this apartment tonight?
Chapter 42 · 0% Book details