Sashe 101
Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da an biye ta Farida da Zahra'u idan kin ganki a wannan gida haka Allah ya tsine min albarka, to sai me don kin gan ni kin kauda kai kinyi kamar baki ganni ba da sauran matan ubanki?
Ai babu komai" Khaleesat ta hade rai ta gaida su Mama Shatu dake zaune fuska duk babu walwala suka amsa mata babu yabo babu fallasa suna kare mata kallo, Nenne ta gyara zama cikin bacin rai tace "Banda matan ubanki da suka takura aje a san inda kike a ga halin da kike ciki sannan ni da na amshi sabon lambar Awdul wajen Farida nayi ta doka masa kira har yaje ya dauko mu ya kawo mu kin zata akwai wanda zaki gani a gidan nan ne?
Ita farida Allah Allah take ta koma Legas ta ci gaba da tuwo tuwonta a can, uwarki kuma ba sanin ciwonki tayi ba balle ta samar mana hanyar zuwa ganin halin da kike ciki, amma me? haka nan albarkacin Ali nace dole dole sai naje naga halin da kike ciki, haka nan na uzura ma Awdul da kira yaje ya dauko mu, kuma Alhamdulillahi ga ki nan har wani haske kika kara alamar kina cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da mijin ki, to meye zaki yi kamar baki ta
a sanin mu ba daga abun arziki dai" Mama Zubaida tace "To ai sai a zaga damu cikin gidan mu sa albarka tunda Allah bai yi mu za mu kawo amarya ba" Nenne tace "A'a, ba bin kwakkwafi da tsegumi ya kawo mu ba kaman en iska, tunda dai yarinya na cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya dama mu hakan ne kadai fatan mu, don haka babu me shiga mata ko ina a gidanta, in ma ce maku aka yi ku yi hakan don wata mugun manufa taku to baza ayi ba, don ni ban yarda da yanda ku ka dage sai an zo gidan Khaleesah ba tunda ni ba yarinya bace, dama kuma Ali yace ko minti sha biyar kar mu yi, da mun samu ganinta mu kamo hanya mu dawo tunda mu ba iyayen banza bane" Mikewa Khaleesat tayi ta tafi kitchen ta bude fridge ta dauko ruwa da drinks ta daura kan tray ta kai masu parlorn ta ajiye, ita dai Aunty Farida sai bin ta da kallo take don kana kallon fuskarta tasan akwai damuwa, gashi tana son kebewa suyi magana da ita amma tana gudun fitinar Nenne, Nenne na kallon Farida tace "Karfe nawa yanxu?" Farida tace "Uku da minti goma" Nenne na gyara mayafinta tana kallon Khaleesat tace "Toh kitchen za ki kai ni mu gana ko kuwa? in mun gama magana sai kije ki ce masa za mu koma ba zama muka zo yi masa ba" Aunty Farida ta dake ta mike tace "Kafin nan bari in
an yi magana da ita Nenne" Nenne ta kalleta da sauri tace "Ai ba kashe aure ya kawo mu ba Farida, in baza kiyi mata magana a gabanmu gaba daya ba to ki rike maganar ki kawai don ba alkhairi bane, haka kawai baza ki ja yarinya ki ke
e da ita ki kitsa mata tsiya da salon kashe aurenta ba" Aunty Farida ta dinga kallon Nenne, Nenne ta mike tana rike da babban jakarta tana kallon Khaleesat tace "Kai ni kitchen din" Khaleesat taji kamar tayi kuka bayan Nenne ta hana Aunty Farida tayi mata magana, rai babu dadi ta nufi kitchen Nenne na biye da ita a baya bayan ta jaddada ma farida a kunne kar ta bari su Mama Zubaida su shiga ko ina na gidan, su Mama Shatu da Mama Zubaida sai tabe baki suke, Nenne ta tura kofar kitchen din bayan sun shiga, tana kare ma kitchen din kallo tace "Maa sha Allahu kai kaji waje sai kace daki uku a hade, kuma iya girki kawai ake yi a nan?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Nenne ta zauna kasan tiles din kitchen din ta zuge jakarta tana kallon Khaleesat tace "To kin tsaya min kerere a kai" Dukawa Khaleesat tayi a gabanta tana kallonta, Nenne ta fito da wasu kulle kulle har
ashi biyar, ta dinga kwancesu daya bayan daya cikin nutsuwa, murya can kasa tace "Kin ga wannan?" Khaleesat dai kallon kullin da Nenne ke nuna mata kawai take, Nenne na magana a hankali kamar tana tsoron wani ya ji tace "Cikin ruwan wanka zaki dinga diba kadan kadan kina zubawa kiyi wanka, duk wani mugun abu da mutum zai maki ko kuma yayi maki to da izinin Allah zai koma kansa da zuri'arsa, sharrin zai lalace na har abada, Wnn kuma a kunu zaki dinga zubawa ki sha kayanki ke kadai, wannan girki zaki dinga yi maku da shi gaba daya ku ci, ba wani mugun abu bane kawai saboda zaman lafiyanku da kwanciyar hankalin ku babu kuma
an iskan da zai iya shiga tsakaninki da mijin ki, sai ki ga kanku ya hadu kuna ma juna nutsattsen soyayya bakwa son laifin juna, wnn na hayaki ne shima duk wani mugun abu idan an maki zai karye ya koma kan me shi da izinin Allah, da kyar aka tsam min wallahi, kin dai gansa
an mitsitsi ko Ali ban dibar ma ba tunda naga bashi da yawa na kawo maki ba don halin ki ba, wannan na karshen shi kuma na sha ne da wanka, in kinyi wankan sai ki kada shi ko cikin ruwan shayi ne ki dinga shan abun ki" Ita dai Khaleesat tayi shiru tana ta kallon abubuwan da Nenne ke mata bayaninsu sinka sinka cikin nutsuwa, Nenne ta gyara zama fuskarta a daure tace "Wallahi in kika sa nayi asaran lokacina da en kudadena kika ki amfani da wannan abubuwan da na shiga kauyuka takanas na samo maki to in na maki Allah ya isa sai ya bi ki tunda ni ba baiwar buzuwar uwarki bace, duk ita ya kamata ta maki wannan abun amma gantalalliyar bazata yi ba, dama kuma sari nasan ke da ita bakwa amfani da duk wani abun taimako da nake baku, wani lkcn matsalarku ce ma ke shafan
a na yayi ta wahala a duniya, to wannan in ma kinki yi wallahi kanki kika cuta don dangin Awdul ba mutanen arziki bane duk mun sani, kuma ba lallai su barki ki zauna lafiya a gidan mijin ki ba barin yanda suka dau
aran tsana suka dora ma ubanki saboda shi talaka ne, to ni dai gashi nan albarkacin ubanki na maki wannan wahala, haka nan na shiga wani kauye duk mayu na fito da kyar, to ya rage naki kiyi ko kar ki yi, in ma baki yi ba Allah ya isa" Khaleesat dake kallonta tace "Toh in ya gan su sai in gaya masa na menene su?" Nenne ta saki baki tana kallonta, a fusace tace "Ke dai sokuwa ce mahaukaciya, to uban wa yace maki a gabansa za ki yi?
Yau naga bala'i, wannan wace irin shashashar yarinya ce? dama ba sai ya fita ba zaki yi maza kiyi duk abinda zaki yi kafin ya dawo?
Ni da ban yi boko ba ma nafi ki hankali da wayo? wannan wace irin jaraba ce Zahra'u ta haifar ma Ali?