Sashe 122
Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Khaleesat na idar da sallan Asuba ta kwanta kasan carpet din dakin Mustapha don dakin da dumi saboda room heater dake kunne, amma hakan bai hanata dinga jin sanyi ba saboda wankan da tayi, babu yanda Safiyyah bata yi da ita ta kwanta saman gado ba amma Khaleesat taki tace kasan carpet din ya isheta, wayar Safiyyah ya fara ring, ta mike ta dauko handbag dinta ta ciro wayar, kallon Khaleesat tayi tace "Housemate dinki ne ke kira" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta zauna gefen gado sannan tayi picking call din tayi masa sallama tare da gaishesa, daga daya bangaren yace "How are you, naga baki yi replying message da na maki ba tun jiya" Safiyyah tace "Kawai bana son inyi stressing dinka ne probably kace zaka zo picking din mu a airport" Yace "Kuna ina yanxu?" Safiyyah tace "Muna gidan yayana, ga Housemate din ka nan, let me give her the phone...." Calmly yace "Ohk..." Safiyyah ta mike ta tafi inda Khaleesat ke kwance ta durkusa tana mika mata wayar, Khaleesat ta kasa amsan wayar, har sai da Safiyyah ta kai mata wayar kunne, daga daya bangaren Khaleesat taji yace "Halysaah...." Kasa ce masa komai tayi, lokaci daya taji hawaye masu zafi sun fara sauka idonta, a hankali yace "Can you hear me?" Muryarta na rawa da kyar tace "Uhm" Shiru yayi, after some seconds yace "I will come over later in sha Allah" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, kashe wayarsa yayi, ta ajiye wayar wasu hawayen na sauko mata, ita dai Safiyyah bata ce mata komai ba.
Karfe takwas na safe Safiyyah ta fito daga dakin Yaya Mustapha zata je kitchen ta duba menene available da zata girka masu ita da Khaleesat, ga mamakinta sai taga an ajiye makullin dakinta kan Centre table din parlon, dariya ma abun ya bata, ta karasa ta dauki makullin sannan ta koma dakin ya Mustapha da sauri ta kulle kofar, dariya ta dinga babbakawa Khaleesat na kallonta, tana nuna ma Khaleesat makullin hannunta tace "Kin ga er iskar ta ajiye min makullin kan Centre table saboda taga na tare dakin mijinta, ashe karamar er iska ce ita ban sani ba? ai wallahi boyewa zan yi inyi kamar ban gani ba don ni kam naga dakin zama..." Safiyyah na fadin haka ta bude zip din akwatin ta ta cusa makullin ciki, Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza kai tace "Don Allah tunda har ta ajiye maki makullin kiyi hakuri mu koma dakin ki Sophie" Safiyyah tace "Wallahi bazan koma ba for now, next time in ance ta boye min makulli bazata boye ba, ba tace ita er iska bace ni kuma zan nuna mata er daba ce ni, ina nan dakin sai naga abinda ya ture ma buzu nadi" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce komai ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "To ni ba na manta ke buzuwa bace" Khaleesat tace "A'a ni bafillatana ce, babana bafillatani ne" Safiyyah tace "To Umma fa?" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah ta nemi waje ta zauna tace "Ke kiji rashin kunya kiri kiri ta ajiye min makulli kan Centre table da taga ba sarki sai Allah, to da menene nufinta da ta boye makullin in koma garage da zama ko me?" Knocking kofar dakin aka yi Safiyyah ta mike ta bude taga Mustapha tsaye ya shirya alamar zai fita aiki yace "Zaki fito ki yi maku breakfast ne?" Safiyyah tace "Har yanxu duk jikina ciwo yake min wallahi Yaya" Yace "Toh bari ayi maku order" Ta gefen ido Safiyyah ke kallon Surayya da ta fito parlon daga dakinta idonta akan Centre table wato tana duba makullin da ta ajiye, Surayyah ta kalli Mustapha tayi mitsi mitsi da ido tace "Mustapha bayan Aslam ya tashi bacci na tambayesa makullin shi ne ya dauko min wani toy dinsa ashe ciki ya zura, na samu da kyar na ciro makullin sannan na fito na ajiye mata kan Centre table 30 minutes ago, to kaga dai yanxu babu makullin kan Centre table din sannan bata fito daga dakin ka ba, me hakan ke nufi??" Mustapha ya kalli kan Centre table din, can ya kalli Safiyyah da ta hade rai tana rike da waist dinta yace "Safiyyah kin dau makullin ne?" Safiyyah ta wani kallesa tace "Ban gane na dau makullin ba Yaya" Cikin daga murya Surayyah tace "Wallahi in baki fito min daga dakin miji ke da shegiyar kawarki ba duk abinda na maku ku kuka ja ma kan ku a gidan nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Toh ni kuma dakin yayana ne, ita kuma Khaleesat dakin yayan kawarta ne, kin ga kuwa baki isa ki ce mu fito ba bayan bamu da wani dakin da za mu zauna in mun fito" Rungume hannu Mustapha yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, Surayya ta yo kan Safiyyah a fusace Mustapha ya tareta yace "Kee baki da hankali ne??" Safiyyah tayi wani shewa tace "Ka kyaleta dai ta zo ta ta
a ni zan nuna mata da sabon dabanci na dawo daga Nigeria, wallahi sai na tuge mata gashin kanta gaba dayansa, ta zo ta ta
a ni ta ga ikon Allah" Khaleesat dai tayi tagumi duk jikinta a sanyaye tana jin su, Surayyah ta fashe da kuka tace "Wallahi Mustapha zan bar maka gidan nan kai da Safiyyah ku zauna don bazan ci gaba da zama da matsiyaciyar ba a gida daya, sai dai ka zaba ko ni ko ita a gidan nan" Safiyyah tace "Ke din banza, minti nawa ne ya canza ki amma ni bazai ta
a canza ni ba tunda jininsa ce ni, ke kuwa tsaf zai iya sakin ki ya auro wata" Surayya tayi wani kukan kura zata cafko Safiyyah, Mustapha yayi saurin riketa ya ja ta zuwa dakinta yana masifa kamar zai ari baki, Safiyyah ta koma daki ta dinga babbaka dariya har da rike ciki, Khaleesat dai sai kallonta take ta kasa cewa komai, after a while Mustapha ya sake knocking dakin, Safiyyah ta fito ta wani kauda fuska tana jiran jin abinda zai ce, nan ya fara lallabata yana cewa "Pls Safiyyah in dai kin san kin dau makullin kiyi hakuri ki kyaleta ki koma dakin ki, don ni zaki yi ai ba don ita ba, kin ga i am almost late for work, don Allah in kin dau makullin kiyi hakuri ko koma dakin ki" Safiyyah taki cewa komai tana girgiza kafa daya, haka ya dinga lallabata daga karshe ta kallesa tace "Na ji, amma wallahi ka ja mata kunne da kyau ta fita sabgata a gidan nan idan ba haka ba za mu yi batattciya da ita, don jahilci zan dinga nuna mata iri iri wallahi" Mustapha yace "Na ji, i will talk to her" Juyawa Safiyya tayi ta koma dakin, shi dai ya koma parlor ya tsaya yana jiran yaga fitowar Safiyyah.
Khaleesat felt relieve bayan sun koma dakin Safiyyah, sai sannan ne ma ta samu bacci ya dauketa don kasa bacci tayi a dakin Mustapha.