← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 180

Sashe 30

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amma ban san sunanki ba kawar Housemate" Safiyya tayi murmushi tana bude cookies din ta dau guda daya tace "Sunana Safiyyah Adam" Yace "Maa sha Allah, it's nice meeting you Safiyyah, i am Jawwad Ahmad, or you call me Jay" Safiyyah tace "Nice meeting you too Jay" ita dai Khaleesat wasa da gefen veil dinta kawai take kanta a kasa, Safiyyah ta bude handbag dinta saboda kiran wayarta da ake yi, tana dubawa taga Cousin brother dinta ne, ta mike tace "Let me pick a call pls" Jay yace "Alright Safiyyah" Kofa ta nufa ta bude ta fita sannan ta kullo masu kofar, ledan da suka shigo dakin dashi ya
an bude yace "You got me all this Halysaah" Khaleesat ta
an kallesa tace "Um" Yace "Ohk thank you so much i really appreciate" Tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin?" Yace "I am getting better gradually, daxu sai naji ina sha'awar wannan tuwon da kika yi some days back" Tana kallonsa tace "Na vegetable soup?" Yace "No, wannan da na kasa ci, the dark soup, I can't remember the name" Bata san sanda tayi murmushi ba tace "Ok miyan kuka?" Yace "Shi... kawai naji shi nake son ci sincerely" a hankali tace "Ohk zaka je can gida anytime soon ne?" A hankali yace "Idan na samu lafiya in sha Allah" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam idonsa na gun different direction, Ajay ne ya bude kofar dakin, kai tsaye ya shigo ya nufi Jay yana mika masa wayar hannunsa yana kallonsa, ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata kalli inda yake ba, Jay ya amshi wayar yana duba screen din, sauke
afafuwansa yayi daga kan kujeran da yake zaune ganin wanda ke kan layi, ya kai wayar kunne da ladabi yayi sallama hade da gaisuwa, sai kuma yace "Alhamdulillah Abba da sauki, wayar a silent yake ne shi yasa" Sai kuma ya daga kai ya kalli Ajay jin abinda Abban ke ce masa, a hankali yace "A'a ba haka bane Abba, i do eat... but not much, ba gaskiya ya fada ba" Daga haka yayi shiru bai sake cewa komai ba, after a minute yace "To in sha Allah Abba, Allah ya kara girma" Sai da ya jira Abba ya katse wayar sannan yayi wurgi da wayar saman gadonsa yana kallon Ajay, wani kallo Ajay yayi masa ta gefen ido ya juya ya tafi ya dau wayarsa a kan gadon sannan ya fice daga dakin, Khaleesat ta gama tura ma Safiyyah text din da take na cewa tayi masu ordering Lyft su tafi gida, sai kuma ta daga kai ta kalli Jay, ganin mood dinsa ya canza, a hankali tace "Baka cin abincin ne ko?" Yace "Ki kyalesa mana, i took cereal daxu da safe kuma a gabansa, shi in bai bata min rai ba baya jin dadi a rayuwarsa" Khaleesat tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can dai tace "To ai Cereal ba abinci bane, ka dai dinga ci ko kadan ne"
an murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace "Shikenan, za mu koma, Allah Ubangiji ya baka lafiya" Yace "Baza ki bari Salem ya dawo yayi dropping din ku ba?" Tace "Aa, Safiyyah nasan brother dinta ne ke kiranta a waya, kaga tun daxu muka gama lectures bata koma gida ba" Yace "Ohk ni bari in ajiye ku" Khaleesat ta zaro ido tace "Aa kai da baka da lafiya, za mu yi ordering Uber do not worry about us pls" Khaleesat ta mike, yana ganin haka shi ma ya tashi, amma sai da ya dafa kujera for sometime saboda juya masa da kansa ya fara yi, A hankali Khaleesat tace "Pls kar kayi stressing kanka, just lie down and rest" Ya dago kansa yace "No, let me see you downstairs" Juyawa tayi ta nufi kofa, ya bi bayanta, ga mamakinta sai ta ga Safiyyah tsabar samun waje tana zaune parlon dake upstairs tana kallo tana cin cookies ga lemo a gabanta, to a ina ta samo lemun da cookies, Safiyyah ta washe baki ganin Khaleesat sannan ta mike tace "Shikenan mu tafi?" Jay da ta hango ne yasa tayi tsit, Khaleesat ta nufeta suka fara sauka downstairs a tare amma gabanta faduwa yake kar su kara ganin karen daxu, hakan yasa ta bari Safiyyah ta shiga gaba, Jay na biye da su a baya har suka sauko downstairs, ai ko karen na ganinsu ya nufo su da gudu yana haushi, Khaleesat ta juya a tsorace zata koma sama ta ci karo da Housemate dinta dake bayanta, ya rikota da sauri yace "C'mon, are you afraid of dog Halysaah?" Bayansa ta koma zuciyarta na bugawa, Safiyyah kuwa sai kora karen take da jakar hannunta fuska daure, shi dai Ajay na zaune parlor tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai ya ci gaba da kallon Football da yake, sai da Jay ya kori karen sannan ya juya da gudu ya koma gun Ajay ya zauna saman kujeran kusa da shi, Jay ya juya ya kalli Khaleesat da ta marairaice ita ma tana kallonsa, ya
an yi murmushi yace "Ba abinda zai maku ai, bai san ku bane shi yasa...." ita dai bata ce komai ba, Jay ya jufi Ajay yace "Ajay ina makullin motana?" Ajay yace "Me zaka yi da makullin mota?" Khaleesat dai tuni ta nufi kofar fita parlon da sauri don ko kallon Ajay bata son yi, Safiyyah kam tana kallon Ajay tace "To sai anjima, Nagode sosai" Yace "Allah ya tsare" sallama tayi ma Jay shima sannan ta bi bayan Khaleesat, Jay yasan bazai basa makullin ba, hakan yasa ya duba aljihun Ajayn ya zaro few dollars sannan ya juya ya bi bayan Safiyyah, duk yanda yayi da Safiyyah ta amshi kudin taki amsa, Khaleesat tuni ta kusa fita daga gidan gaba daya, a haka Safiyyah ta bi bayanta.

Safiyyah na kallon Khaleesat bayan sun shiga Lyft har sun fara tafiya ta rike ha
a tace "Ke ashe wannan gayen da muka yi misunderstanding da farko da muka shigo gidan yana da kirki sosai, in gaya maki da na zauna parlon nan na sama ni kadai ya zo wucewa ya ganni sai ya tsaya yayi powering min TV, har da kunna min wutan parlon, ya kuma nuna min fridge in dau lemo in sha, wallahi i never expect such kind gesture from him duba da yanda ya amsa mana gaisuwanmu da muka shigo parlon da farko, ashe mun yi misperceiving dinsa ne" Khaleesat tayi kamar ma bata ji abinda Safiyyah ke cewa ba.
07087865788
Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
15.....

Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune parlor tana duba wani reading material dinta wayarta ya fara vibrate, daukan wayar tayi taga number Salem, ita dai kallon screen din kawai take at first, after some seconds ta daga ta sa Hands-free tayi shiru tana saurare, daga daya bangaren aka mata sallama, muryar Housemate dinta ta ji, ta amsa sallamar tare da gaishesa, yace "Ya kika je gida Halysaah?" Tace "Lafiya lau" Yace "How about Safiyyah?" Tace "Tana can gidansu" Yace "Good, thank you so much for the visit" a hankali tace "Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen Housemate" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayar, bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa ta ga Abdul ne, sai a sannan ta tuna damuwar da take ciki for days now, nan da nan mood dinta ya canza, tayi picking call din ta saka hands free sannan ta ajiye a gefenta tana ci gaba da duba reading material dinta a hankali ta gaishesa, yace "Didn't you see the money i sent to you?" Ta girgiza kai tace "Ban kula ba" yace "To ki duba" Katse wayar yayi ta jinginar da kanta jikin kujera with many thought running her mind....

Washegari da yamma bayan Khaleesat ta idar da sallah tana zaune tayi dialing number Salem, yana fara ring ya daga, bayan sun gaisa tace "Dama abinci ne zan ma Housemate dina yace min yana so, ban san ko zaka iya zuwa karfe biyar sai ka tafi masa da shi ba, that's if you are available and u don't mind doing so pls" Yace "Oops naje Pennsylvania daxu da safe, but za ki iya zuwa gidan ki kai masa ai, he is at home" A hankali Khaleesat tace "Ohk" Yace "Yeah, ki kai masa kawai can gidan" Tace "To nagode" a haka suka yi sallama ta ajiye wayar, Allah ya so bata dora girkin ba don ta san babu abinda zai sake maida ta gidan nan dai, tayi zuwan farko tayi na karshe.

Khaleesat na zaune tare da Safiyyah bayan sun gama lectures din su na ranan, Safiyyah tace "Are you checking on ur Housemate even if ta waya ne kuwa Khaleesat?" Khaleesat ta kalleta tace "I don't have his number ai" Safiyyah ta dinga kallonta da mamaki, can ta girgiza kai tace "Ni ban san me yasa kike haka ba, why won't u ask that guy Salem ya baki?
Chapter 30 · 0% Book details