← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 180

Sashe 62

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

You are safe" Ya gyara mata kujeran motar a hankali ta yanda zata
an kwanta yana kallonta, sai da ya jira for almost 10 mins yaga ta
an nutsu tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci yake kallon agogonsa saboda flight din da yayi booking, after a while ya
an duba fuskarta yaga kamar ta fara bacci, tada motar yayi ya bar wajen, still sai da ya kara tsayawa a p
harmacy ya siya mata magunguna, ko kashe motar bai yi ba don kar ta ma san yayi parking, har yaje ya dawo kuma bacci take, ya ja motar ya dau hanyar airport hoping jirgin bazai tashi kafin su isa ba, suna isa airport din bayan yayi parking yaga saura minti sha biyar kawai jirgin ya tashi kamar yanda suka sa a ticket, tapping din kujeran motar yayi gently don har lkcn bacci Khaleesat take, a tsorace ta farka kamar yanda tayi daxu a eatry tana ganinsa kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya bude ledan abincin da ya siya ya ciro mata takeaway din ya bata yace "Take a little before ur flight..." Ba musu ta amshi abincin tana kallonsa a hankali tace "Lagos din zan je?" Yace "In kin je zaki gani" Sai da ya hade mata rai sannan ta ci abincin cokali uku da kyar tana hadiyewa kamar magani, ya bude drugs dinta ya bata ta amsa ta sha da ruwan goran hannunta, without looking at her ya mika mata wayarsa yace "Saka min number mutumin nan" Zaro ido tayi tana kallonsa, yace "Ko bakya ji na ne?" Kamar zata yi kuka tace "Kiransa zaka yi?" Yace "Amsa ki sa min number sa nace" Hannunta na rawa ta amshi wayar ta saka masa lambar Abdul don tana da shi a kanta, ya amshi wayar yana kallon number sannan ya ajiye wayar yace "Dama an mashi alkawarin aurenki ne?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Um, tun shekara hudu da suka wuce" Shiru Ajay yayi yana kallonta, but because of how cautious he is with time kar tayi missing flight dinta kawai ya ciro Eye drop din da ya siya mata ya mika mata ta diga a idonta, tsoro ya sa ta kasa digawa don bata san wani kalan azaba zata ji ba, daga karshe ya fixge eye drop din babu yabo babu fallasa ya diga mata a cikin idon, tuni ya sauka daga motar yana jiran in ta gama kururuwan da take ta sauko, daga karshe ta sauko daga cikin motar tana rufe idon da Hijab dinta, dayan wayarsa ya mika mata wanda ticket dinta ke ciki, daga ita sai handbag din ta da wayarsa ta nufi cikin airport din tana waige waige kamar iska zai kadeta ta fadi, kana ganinta kasan ba dai dai ta ke ba, she is traumatized and stressed, tsoron Abdul kuma ya gama shigarta sosai, shi dai yana tsaye jikin motarsa yana kallonta har ya ga shigarta cikin airport din, komawa cikin motarsa yayi yana duba full name din Abdul ta true caller, wani number yayi dialing yana fara ring aka daga yace "Zan turo maka wata number yanxu, ina son kasa a bincika min location dinsa a cikin garin kano, i will be waiting for feedback" Bayan ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa da kujeran motar, yana nan zaune har bayan 20 mins just to be sure bata yi missing flight dinta ba kafin ya bar airport din, Khaleesat ta dinga bin cikin jirgin da kallo kamar idanuwanta za su fito jin anyi announcing za su tashi zuwa garin Abuja, Abuja kuma?

Ita wa ta sani a Abuja?

Hawaye ne ya cika idonta ta dinga waige waigen cikin jirgin, me yasa ya mata booking ticket din Abuja.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
HALYSAAH 31
Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka, gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah, Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace "Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta
an yi murmushi ta koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace "Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau" Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo.
Chapter 62 · 0% Book details