← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 180

Sashe 110

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dawowata daga Wudul kenan kusan mutane biyar suke gaya min haka a hanya tun ban karasa gida ba, wallahi buhun hannuna kawai na ajiye bayan na shiga gida na yo nan" Aunty Farida tace "To Allah ya sa mu dace" Maman Salame tana kallon Khaleesat cike da tausayinta tace "Garin yaya haka Khaleesah?" Khaleesat ta sauke idanuwanta bata ce komai ba, Maman Salame tace "To Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, in kuma auren bai kare ba Allah ya kaddara za ki koma sai ki ga an koma" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai saki uku ne Maman Salame" Maman Salame ta kasa cewa komai tana kallon Aunty Farida, kana ganinta kasan sosai jikinta yayi sanyi, ita dai Umma babu abinda tace a dakin, bayan kusan minti goma Maman Salame ta mike a sanyaye tace "Toh Allah ya sa mu dace, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu duka, sai na shigo da safe in sha Allah" Umma tayi mata sallama, Maman Salame ta fita daga dakin rai babu dadi, sarai Umma tasan kishiyoyinta ne suka baza labarin a garin, don ko Nenne bazata gaya ma kowa wannan labarin ba ita da ta tsani tonan asiri, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya don exactly tunanin da Umma take yi ita ma shi ne a ranta, Khaleesat ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty kina da number Safiyyah?" Aunty Farida tace "Ina da shi" Khaleesat tace "Ina son zan kirata ne" Aunty Farida tace "Babu kati a wayar, kuma yanxu dare yayi, ki bari gobe da safe sai kiyi magana da ita" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike tayi kwanciyarta saman gadon Umma, yaron Mama Shatu ne yayi sallama bakin kofar dakin Umma ya daga labulan yace "Wai Babanmu yace Khaleesat ta je" Umma da Aunty Farida dai sai kallon yaron suke, ya juya ya bar bakin kofar, Khaleesat ta mike zaune bayan taji abinda step brother dinta yace, tun dawowarta gidan ita ko haduwa da baban nata bata yi ba, ta sauka daga saman gadon tana gyara hulan kanta ta fita daga dakin Umma ta bi ta da kallo taji hawaye na taruwa idonta, Khaleesat na tafiya a hankali ta karasa har bakin kofar Babanta don yana zaune kan tabarma shi kadai a bakin kofar nasa, dukawa tayi daga gefen tabarman ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta gaishesa, maimakon ya amsa sai taji a hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, i failed you as a father, i caused you all this, but everything happened because I am a nobody, everything happened because...." Shirun da taji yayi ya sa ta daga kai ta kallesa taga hawaye a idonsa, bata san sanda ta fashe da kuka ba, yace "I am sorry for failing you daughter, albarkacin biyayyan da kika min baza ki ta
e ba in sha Allah, my wish for you since u were born was to give you the best of everything i could amma Allah bai nufa hakan ba kaddara ta fada min...."
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Read my book "HALYSAAH" on ArewaBooks, Platform available: "app only" :: https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
HALYSAAH 52
Washegari da safe har karfe goma saura Khaleesat bata tashi baccin da take ba, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya tasheta don duk sun san bata yi wani baccin kirki ba daren jiya, daga wayewar gari zuwa lokacin mutanen da suka shigo dakin Umma yi mata Allah ya kyauta da abinda ya faru sun fi goma, don gaba daya labarin ya gama bazuwa garin, Aunty Farida ta kalli Umma bayan wata makociyarsu da ta shigo jajen ita ma ta fita, a fusace tace "Don Allah ki dena tanka masu Umma, ki nuna ke baki ma san jajen uban me suka shigo yi maki ba, wallahi banda ke in ban ci kaza kazan mace ba ta sake shigo mana dakin nan ace ba ni ba, wannan ai iskanci ne" Umma tace "To ya kike son inyi Farida? kinga ai muna mutunci sosai da su shine har ya sa suke shigowa, duk warce kika ga ta shigo dakin nan to muna mutunci sosai ne da ita, kin ga ai bazan masu rashin mutunci ko wani abu ba, wanda ya ya
a labarin a garin ai shine vabvan munafuki ba wanda ya shigo jajenta maka ba, kuma naga dai ba kan Khaleesat farau ba mutuwar aure" Aunty Farida ta mike tace "Ban ta
a ganin inda ake shigo ma mutum jajen mutuwar aure ba sai a garin nan, kuma wannan ba komai bane banda salon gulma da munafurci" Daga haka ta fice daga dakin zata duba ruwan zafin da ta dora kan wuta, Umma ta kalli Khaleesat da tayi backing dinsu tana bacci, ta kai hannu ta dafata, tayi kasa da murya tace "Har yanxu baccin dai Khaleesat?" Juyowa Khaleesat tayi tana murza ido, sai kuma ta mike zaune, Umma na kallonta tace "Jiya da daddare baki ci abun kirki ba, ki je ki wanke baki ki zo ki karya, ga wainar shinkafa na sa an amso maki tun daxu, kar ya huce" Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta tafi gun akwatinta da ta dawo da shi daga America ta du
a ta bude jakar ta ciro Shower gel dinta da sponge, sai toothpaste da Brush, Umma dai kallonta kawai take har ta mike zata fita daga dakin Umma tace "Tunda wanka za kiyi kice Farida ta juye maki ruwan zafin, tana waje" Khaleesat tace "To Umma" Daga haka ta fita daga dakin Umma ta bi ta da ido, Khaleesat bata ko kalli inda kishiyoyin Ummanta suke ba da dukun dukun din zannuwan jikinsu kamar masu yin kuli kuli, ta jira Aunty Farida ta juye mata ruwan zafi a bucket ta surka mata sannan ta kai mata har bandaki, bayan ta shiga wankan Aunty Farida ta dora wani ruwan ta koma dakin Umma, Mama Zubaida ta ta
e baki tana murmushi ta kalli Mama Shatu tace "To kuma yanxu ko da uban me za ayi mana takama?" Mama Shatu ta kwashe da dariya tace "In kin tambayeni in tambayi wa?

Ba ke kike kokwanton maganar Malam ba da yace auren karkari ayi wata daya ya sakota, to kin dai ga kwalliya ta biya kudin sabulu, sai ki dena cewa kinyi asaran kudin ki, ji yanda hankalinki ya tashi ranan da muka je gidan da Nenne kin ga katon gida ta shiga dakin can ta fito ta shiga wancan ta fito kin zata watayawa take a gidan, ni dama ina kallon kwayar idonta nasan ubanta take ci a gidan, sam ban ga alamar kwanciyar hankali ba don duk a firgice na ganta" Mama Shatu ta sauke ajiyar zuciya ta rike ha
a tace "Ohhh....
Chapter 110 · 0% Book details