← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 180

Sashe 165

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

You weren't like this before, ko don nace zan aure ki?" Sunkuyar da kanta tayi alamar kunya, yace "To meye amfanin zuwa nan tunda baza ki saki jikin ki ba, i want us to have a quality time together amma kiyi ta sunkuyar da kai...." Tana murmushi a hankali tace "To ai kunya nake ji" Yace "To kalleni zaki dena jin kunyan" Taki dagowa tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Ni bazan iya ba" Bai sake ce mata komai ba, ganin haka ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta yake, murmushi yayi mata murya can kasa yace "You are specially made Halysaah" Rufe idonta tayi tana murmushi a hankali tace "Thank you" Yace "Kin dai ji me kawarki ta ce ko?" Khaleesat ta daga ido ta kallesa tace "Me ta ce?" Yayi kasa da murya yace "We will make beautiful Babies together...." Khaleesat ji tayi wani azababben kunya ya rufeta, yana murmushi yana kallonta yace "Ni ko guda daya kika bani me kama dake i will appreciate..." Kamar zata yi kuka tace "Ni dai mu tafi gida" Yace "A'a sai kin ban labari, kina ban labari ko daya ne sai mu tafi" Shiru tayi, sai kuma tana wasa da straw din drink din gabanta tace "Wani irin labari?" Yace "Ko ma wani iri ne, ko kuma ki bani labarin yanda ku ka hadu da Funny frnd dinki Safiyyah" Khaleesat tayi murmushi ta dago kai tace "Ohk...." Babu bata lokaci ta fara basa labarin farkon haduwarta da Safiyyah a school, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawan kirki baya yi, everything about Khaleesat is just beautiful and breathtaking, tsakaninta da Allah take ta basa labarin Sophie ashe ko sanin abinda take cewa bai yi ba ya kafeta da ido with many imagination running his mind, daga bada labarin Safiyyah kawai ta saki jiki a wajen, dama kuma haka yake so... kamar yanda ya so hakan ne ya faru don they had a wonderful time together, labari sai wanda ta manta ne bata basa ba a kan experience dinta a America tun daga shekaran da ta zo har zuwa yanxu, wani yayi dariya, wani yaji tausayinta wani ya ga wautan ta, babu abinda ya kara burgesa da ita tana basa labarin sai turancin ta, she was so vocal, duk da timidness dinta she was very outspoken kamar ba a unguwan nan da gidansu yake ta tashi ba, he never knows she speak so well sai yau, yayi kasa da murya yace "You know what Halysaah?" Ta girgiza masa kai tana kallonsa, a hankali yace "I love you so much" Rufe fuskarta tayi da sauri tana murmushi...

Sai wajen karfe bakwai suka bar park din, sai da suka fara dropping Safiyyah a gida before heading home, Jay na parking Khaleesat ta kalli motar Ajay dake parking Space, can ta kalli Jay tace "Is he waiting for you?" Jay yace "I don't think so, kinsan yana da aboki a Neighborhood din nan shi ma PhD yake, the frnd is at the far end of this street, External defense dinsu is around the corner...." Khaleesat tace "Ohk har da kai?" Jay yace "Yea in sha Allah, period din exam din ku ne Defense dinmu" A hankali tace "To Allah ya baku nasara" Yana murmushi yace "Ameen" Tace "To a ina zaka yi parking since he is occupying the space?" Yace "Zan je gida in dawo anjima" A hankali tace "To ni kadai a apartment din?" Yace "Ga motar Ajay kina gani, ai yana ciki kenan" Shiru tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Mu je in raka ki ciki to" A tare suka sauka daga motar ya rakata har cikin apartment din, yana kallonta calmly yace "Can i go now?" Jingina tayi da bango a kusa da shi ta langwabar da kanta kawai ta marairaice tana kallonsa, ya sauke idonsa daga kallonta trying to calm his self down, a hankali yace "I need to go Halysaah, ki kulle kofar" Daga haka ya juya ya fita daga parlon without looking at her, ta bi sa da kallo kafin ta kulle kofarta....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke
HALYSAAH 78
Bayan Khaleesat tayi karatun da zata yi ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan ta saka hijab ta fito daga dakin don tun da ta dawo bata ci abinci ba gashi har karfe goma ya wuce, downstairs take leke ko zata ga Housemate dinta, Ajay ta gani yana danna wayarsa, hannunsa rike da Can din soft drink, tana ta tsaye a corridor din don da ba don yunwan da take ji ba komawa dakinta kawai zata yi ta hakura da abincin, after a while ta fara saukowa staircase din trying not to make any sound, tun daga nesa take kallon screen din wayarsa ganin kamar hoton da suka yi da Jay daxu a park, tsaye tayi tana ta kallon wayarsa da mamaki, after some seconds taga ya fita daga hoton kasa gane inda ya samu hoton tayi, tasan dai Jay bazai tura masa pictures din ba, to kaddai a status Housemate dinta ya dora hoton, ta shiga uku, sosai taji gabanta ya fadi, lokaci daya Ajay ya juya bayan yayi sensing kamar mutum na tsaye bayansa, ta
an koma baya kamar munafuka tana kame kame tace "Kitchen zan je dama" Ajiye wayarsa yayi ya juya da kyau yana kallonta da mamaki, ta langwabe kai sai kuma ta nufi kitchen din da sauri tana
an waigen sa, ko da ta fito bata gansa a parlon ba, bayan ta koma daki ta ajiye shayin hannunta ta dau wayarta da sauri ta bude WhatsApp dinta, status din Housemate dinta ta bude taga hoton amma ya rufe fuskarta with the caption "Halysaah" da yayi ma hoton, to amma wanda ta gani a wayar Ajay fuskarta a bude yake, ta dinga kallon hoton duk da fuskarta a rufe yake, bata san sanda murmushi yayi escaping lips dinta ba don sun yi kyau sosai, har ta ajiye wayar sai kuma ta dauka tayi masa reply din picture din tace "What if gal frnd dinka ta gani" ajiye wayar tayi ta dau cup din shayin da ta ajiye tana juyawa a hankali, taji wayarta yayi vibrate alamar shigowar message, daukan wayar tayi taga ya mata reply yace "Ke ba Gal frnd dita bace?

Ai ke zabina ce, ita kuma zabin iyayena" Hmm kawai ta mayar masa sannan ta kashe data dinta ta ajiye wayar, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi tana maimata zabin iyayensa da yace a ranta, duk yunwan da take ji haka nan ta neme sa ta rasa shayin ma bata wani sha sosai ba, bayan ta gama shirin kwanciya ta dauro alwala ta fito sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, wayarta taji na vibrate ta jawo wayar a hankali tana dubawa taga Housemate dinta ne ke kiranta, sai da ya kusa katsewa tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, yace "Why did you go offline Halysaah?" Ta
an yi murmushin karfin hali tace "Na je nayi alwala ne zan kwanta" Yace "Ohk, kina da class gobe ne?" Ta
an yi shiru, duk da bata da shi tace "Eh ina da...." Jay yace "Yaushe?" Tace "Da safe" Yace "Ohk, na tsaya wani aiki ne a system dina shi yasa ban dawo ba, may be we will meet in school tomorrow in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen, Good night Halysaah, naga kamar kin fara jin bacci ko?" Cikin sanyin murya tace "Uhm, sai da safe" Yace "Allah ya kai mu lafiya" Daga haka ya katse wayar sa, Khaleesat ta ajiye wayar hannunta ta juya ta lumshe ido.
Chapter 165 · 0% Book details