← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 191

Sashe 99

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Karfe sha biyu saura taji hannu a forehead dinta, bude idonta da suka kumbura tayi a hankali don sosai kanta yayi mata nauyi, suna hada ido ta sauke idonta, Calmly yace "Ta shi ki shirya mu tafi shopping" Da kyar ta mike zaune tana kara rufe jikinta da duvet, sai kuma ta fara jawo towel din da ya cire mata daxu, shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, har cikin ransa he felt bad ganin yatsunsa kwance a fuskarta, cikin dubara ta daura towel din sannan ta mike tsaye lkci daya ta duka kasa da sauri tana runtse ido, yana kallonta yace "What?" Lokaci daya hawaye ya idonta, cikin rawan murya tace "Bazan iya ba, zafi nake ji sosai" Ya hade rai yace "Zafin me?" Ta kasa kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "Me na maki da za ki ji zafi?" Ita dai bata dago kanta ba gabanta na faduwa, mikewa yayi ya fice daga dakin ta bi sa da kallo, after a while Khaleesat taji fitar motar sa a gidan, ba karamin daurewa Khaleesat tayi ba ta tafi bandaki, sai da tayi sit bath sosai sannan taji ta samu sukuni, tayi wanka ta dauro alwala ta fito.

Karfe biyu saura tana tafiya a hankali tana dingishi ta fito parlor, ledan kayan da Momy ta bata ta gani a parlon, ta karasa ta bude ledan sai a sannan taga irin kayan da su Meemah suka siyo mata, a hankali ta daure ledan ta dau kayan walking slowly ta koma dakinta da su ta ajiye ta dawo parlon ta tafi kitchen don daura girki...

Momy dake zaune parlor tana kallon Meemah da wani expression tace "Bacci fa kika ce Meemah??" Meemah ta ajiye gyalen jikinta tace "Wallahi kuwa Momy" Momy tace "To baccin me take wajen karfe sha dayan safe??" Meemah tace "In kin tambayeni in tambayi wa?" Momy ta gyara zama tace "Toh baki tafi dakin kin dubo ba?" Meemah tace "In lafiyarta qlau ai kinsan taso ta zai yi ta fito ta gaisheni barin ma da nace masa kin bani sako in bata, sai ce min yayi magani ta sha tana bacci" a hankali Momy tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Meemah tayi wani murmushi tace "Kinsan Allah Momy, kawai jikina ni tun asali ya bani ba lallai irin wannan asirin yayi tasiri lokaci daya ba, bance bazai yi tasiri ba amma sai ya gama moreta tukun, kin ga in rabo ya shiga kafin nan kuma ai mun shiga uku mun lalace, hada iri da talaka ya tabbata" a fusace Momy tace "Ke dai a rayuwarki baki ta
a furta alkhairi sai sharri Amina?

Asirin kusan miliyan biyun kike ce min ba lallai yayi tasiri ba?

Ko kina hauka ne?" Meemah tace "A'a ni bance bazai yi tasiri ba Momy, cewa nayi..." Momy ta dakatar da ita rai bace tace "Bana son ki sake saka min mugun bakin ki a lamarina, ki tashi ki ban waje kar in yi mummunan bata maki rai wallahii" Mikewa Meemah tayi ta kyabe baki tace "Shi Abdul din da duk mun san yanda idonsa ke kan mata ne kike tunanin zai bar yarinyar nan su kwana gida daya babu abinda ya shiga tsakaninsu?" Wani zagi Momy ta kunduma mata tace "Baza ki tafi ki ban waje ba, me mugun alkaba'i kawai, duk ba ke kika ja mana wannan bala'i ba?" Meemah na tabe baki tayi tafiyarta sama, Mikewa Momy tayi ta fara zaga parlor tana jin zufa na keto mata duk da Ac dake kunne, sai kuma ta dau wayarta ta wuce sama da sauri.

Wajen karfe hudu da rabi Abdul ya dawo gida, Khaleesat ta idar da sallah tana zaune kan darduma ya shigo dakin ya ajiye shopping bags din hannunsa, ta mike a hankali tana kallonsa tace "Sannu da zuwa" Yace "Ki duba ko akwai abinda ba a siya ba" Tana kallon bags din ta karasa inda ya ajiyesu tana duba tsadaddun Abayan da ya siya mata kala kala, da takalma da handbags, irin dai quality din da yake siya mata a baya, duk wani abu da zata bukata sai da ya siyo mata, har da tsadaddun turaruka iri iri da man gashi, da na shafawa, kallon lube din da ta ciro a siyayyan ta dinga yi don at first tayi zaton na shafawa a fuska ne, sosai gabanta ya fa
i ta
an kallesa taga kallonta yake, da sauri ta dauke kai zata ci gaba da ciro sauran abubuwan da ya siyo ya mika mata hannu alamar ta basa lubricant din, ta mika masa ba tare da ta bari sun hada ido ba, juyawa yayi ya dau ledan kayan da Meemah ta kawo daxu ya fitar da shi daga dakin, a hankali Khaleesat ta zauna gefen gado nan da nan hawaye ya cika idonta, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana tuna azaban da ta sha daxu.

Wajen karfe takwas da rabi na dare Khaleesat ta gama dafa ma Abdul tea din da ya sa ta ta dafa masa, gaba daya tun daga sanda ya dawo har zuwa yanxu bata da sukuni a gidan, tana sanye da hijab ta karasa har inda yake zaune a dakinsa yana karatun Alqur'ani, ta durkusa ta ajiye masa shayin, zata mike ya jawota jikinsa bayan ya rufe qur'anin, yayi kissing goshinta yana kokarin cire mata hijab din har dai ya cire, lkci daya jikinta ya fara rawa tana son kwace kanta,
in saketa yayi ya riketa gam, tun tana ganin abun kamar wasa tunda a zaune yake, har sai da ta gansu saman gado ya rabata da komai na jikinta sannan idonta yayi clear, ihun da ta dinga masa tana kuka tana kokuwa da shi bai sa ya fasa abinda yake yi ba, upon yayi using lube da ya siyo amma kamar daxu yanxun ma dai bai iya yayi mata komai ba, after a while ya sake ta, fuskarsa a daure yace "Fita" Ta sauka kan gadon da sauri ta dau hijab dinta ta saka ta fice daga dakin jikinta na rawa, zaunawa yayi gefen gado ya rike kansa da yayi masa nauyi yana sara masa.

Throughout washegari Abdul bai bi ta kanta ba a gidan, ta dai gaishesa da safe ya amsa babu yabo babu fallasa, amma hatta breakfast da tayi bai ci ba balle lunch, sosai taji guilty conscience na damunta don tana tsoron kamun Allah, tunda tayi karatun addini tasan kuma meye aure, amma yanxu ita kanta tasan ba intentionally bane taki basa hadin kai, kasa daurewa tayi wajen karfe uku na rana jiki a sanyaye ta samesa a parlor ta durkusa daga gefensa a hankali tace "Don Allah Ya Abdul kayi hakuri idan nayi maka laifi" Shiru tayi don ita kanta tasan she sounds stupid, Babu yabo babu fallasa yace "Laifin me?" Ta sauke idonta ta kasa cewa komai, Yace "Ohk kinsan ma abinca kike yi kenan" Ta girgiza masa kai da sauri, kallonta kawai yake don duk yau ji yayi kamar an dauke masa sha'awarta, unlike before da ko me zata yi feeling din nan nata dai na nan a ransa, kawai ji yayi baya ma son ganinta kawai, Calmly yace "Tashi ki bani waje" A hankali ta mike ta bar parlon.
Chapter 99 · 0% Book details