← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 191

Sashe 5

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin bacci Khaleesat taji ana knocking kofar dakinta, ta mike zaune da kyar tana murza ido ta jawo wayarta tana kallon agogo taga karfe goma saura minti biyar, kallon kofar tayi da mamakin dalilin da yasa yake mata knocking by this time, can dai ta daure fuska tace "Waye wannan?" Taji yace "I could use ur help if u don't mind" Bluntly tace "I beg ur Pardon?" A takaice yace "Nayi misplacing makullina again" Da farko rasa ma me zata ce masa tayi don mamaki, she was mute for almost a minutes, taji yace "Hello" Sosai ta hade rai tace "I don't understand kayi misplacing makullin ka?" Yace "Look, ni fita zan yi yanzu idan na fita sai ki kulle gidan" Bata san sanda tace "Idan fita zaka yi ka fita mana, me yasa zaka tambayeni makulli? ko makullinmu a hade yake?" Shiru yayi at first, sai kuma yace "Ta yaya zan fita nace maki ban ga makullin kofa ba" Tace "But our keys are separate isn't it?" Yace "Sai yanzu da kika fada na sani ai, fito ki bude min kofa zan fita" Wani bakin ciki taji ya tokareta, yace "I am waiting at the parlor" Bata tanka sa ba, can tayi tsaki ta sauka daga kan gadonta ta dau hijab ta sa, ta bude handbag dinta ta dau makullinta ta nufi kofar dakin, fuskarta a daure ta bude ta fito ta karasa living room ta gansa tsaye bakin kofar parlon yana jiranta, ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma din wayarsa yake dannawa bai kalli inda take ba, ta karasa ta bude kofar parlon da makullin hannunta tace "You weren't given a needle as key da zai dinga
ata kullum, and i shouldn't be responsible always for someone else carelessness" Shi dai bai ce mata komai ba ya fita without looking at her yace "Na zata ai needle aka bani Housemate" Da ido ta bi sa har ya isa inda motarsa take, wato godiyar da zai mata kenan?

Ta gyada kai ta kulle kofar parlon a ranta kuma tayi vow bazata sake masa amfani da makullinta ba sai dai kar ya fita, banda ma rainin hankali me yasa baya misplacing makullin motarsa sai na gida, next time sai dai ya fasa zuwa inda za shi don bazata sake sharing key dinta da shi ba, fuska daure ta koma cikin parlor, sai kuma ta tsaya tana kallon plate din da ya ci abinci ya bari a parlon da container din soft drink ga goran ruwa, tsabar mamaki bata san sanda ta nemi waje ta zauna ba, is this guy okay?

After fetching her food without asking for permission he still have the mind to leave the plate for her at the parlor, anyway... she believe he didn't leave it for her, he left it for himself instead, don ko sati daya zai yi bai dawo gidan ba zai dawo ya tarar da plate din at that same spot don bazata daukesa ba, tashi tayi ta tafi daki fuskarta a daure.

Da safe Khaleesat ta gama shirin fita makaranta, har a lkcn bata dauke plate din da ya bari a parlon ba, amma fa zuciyarta kawai ta kai nesa don ta tsani ganin abu ba inda ya kamata ba, zata kai cup din da ta sha shayi kitchen taji ta taka makulli a kan ash carpet din parlon, dukawa tayi ta dau makullin tana kallo taga nasa ne, he is just careless, tabe baki tayi ta mike ta ajiye makullin nan kan kujera, ta kalli plate din jiya da ya bari, tsaki tayi ta dauke tare da gwangwanin soft drink din da na ruwa, ta hada da cup din hannunta ta tafi kitchen, bayan
an lokaci ta dawo parlor ta dauki handbag dinta tana duba wayarta, ganin Lyft din da tayi order ya kusa isowa ta nufi kofa ta fita.

Wajen karfe sha biyu Khaleesat na zaune tare da Safiyyah warce shigowarta makarantar kenan, Khaleesat na kallonta tace "Kun sha birthday" Safiyyah tace "Oho dai tunda ke baki je ba, yau me ku ka yi a aji?" Khaleesat tace "Nothing much" Safiyyah ta bude handbag dinta ta ciro cake tana mika ma Khaleesat tace "Gashi ba don halin ki ba" Khaleesat tayi murmushi ta amsa tace "Nagode" Safiyyah tace "Kun yi waya da Abdallan ne?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Sophie me kika ce masa ta chat?" Safiyyah ta dau wayarta tayi unlocking cikin few seconds ta shiga DM din Abdul sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amsa tana duba chat din, it was nothing worth taking personal Safiyyah ta gaya masa a chat din, Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba tana kallon wayar hannunta, Safiyyah tace "Me yace maki halan?" Khaleesat ta mika mata wayarta tace "Nothing, kawai yace min kin masa magana" Safiyyah ta tabe baki tace "Kin dai ga yanda yake amsa min chat din ma kamar wani
an sarki, wallahi Abdallah bai yi deserving dinki ba, u are too good to be Abdul's or to end up with him, Allah ya maki sauyi cikin ruwan sanyi ya kawo maki mafita" a hankali Khaleesat tace "Ki tashi mu je aji" Safiyyah tace "Oh baza ki ce Ameen ba??" Murmushi Khaleesat tayi tace "Wani mafita kenan Safiyyah?

Cewa zaki yi Allah ya canza min halayyarsa kawai...." Safiyyah ta tabe baki ta mike tace "Mu je" Khaleesat ta mike suka bar wajen a tare...

Khaleesat na sauka Uber din da ya dawo da ita gida ta nufi apartment dinta, dai dai sanda Co-tenant dinta ya fito daga cikin motarsa dake inda aka tanadar domin parking, sau daya ta kallesa ta dauke kai tana ci gaba da tafiyarta toward their apartment, ya bi bayanta yace "I've waited all day long, i forgot some paperwork a cikin gidan gashi zanyi Submitting tun daxu" Ba tare da ta juyo ba tana ci gaba da tafiya tace "Serves you right" Kallonta yake yana biye da ita, ta ciro makulli a jakarta ta bude kofar ta zare makullinta sannan tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta da makullin...

Bayan Khaleesat ta idar da sallah ta sauya kaya ta fito parlor don daura girki, bata gansa a parlon ba, kuma bata ji alamar ya shiga dakinsa ba, ta nufi tagar living room din tana leka parking space, ganin babu motarsa ta karasa gun kofa ta murda taji a kulle, kallon inda ta ajiye makullinsa daxu da safe tayi taga ya gani har ya dauke, wucewarta tayi zuwa kitchen.

Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta gama karatun da take ta jawo wayarta ta bude WhatsApp dinta don ganin ko Neighbor dinsu Aunty Sha'awa tayi replying sakon da ta tura mata amma sai taga bata yi reply ba har sannan kuma ta bude message din, ajiye wayar tayi ta mike ta dauke darduman da take zaune kai, ta dau hijab ta saka sannan ta fito parlor zata debi abinci, Zaune taga House mate dinta a parlon yana operating laptop dinsa, without looking at him ta tafi kitchen, after some minutes ta fito, ya daga kai yana dubanta yace "Can i have some of ur food if you don't mind?" Mamaki ma ya bata, har da baza ta tanka sa ba sai kuma ta tsaya tace "Duk na baya da kake diba gaya min kake halan?" Ya
an buda ido yana gyada kai yace "Haka ne kuma fa, i just decided to ask politely today" Bata sake bi ta kansa ba tayi tafiyar ta daki, in har sai tace ya diba to ashe bazai ci ba.
Chapter 5 · 0% Book details