← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 191

Sashe 188

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zan kuma yi adalci tsakanin su in sha Allah" Mami dai kallonsa kawai take yi babu ko kiftawan kirki, bayan kusan minti
aya ya daga kai a hankali ya kalleta jin she is still silent, ta
an yi murmushi ta ajiye counter din hannunta tace "Wannan ne maganar dama Jawwad" Sosai yaji gabansa ya fadi, ya dai yi shiru bai ce komai ba yana kallonta yana jiran jin abu na gaba da zai fito daga bakinta, ajiyar zuciya yaji ta sauke me nauyi, after few seconds cikin nutsuwa ta fara magana tace "Toh a yanxu dai i am speechless Jawwad, cause this is something I never saw coming, gaba daya kaina ya kulle, amma ita yarinyar a Amurkan ku ka hadu ko a ina ka santa?" A hankali Jay yace "Can na santa, she is schooling there also" Mami ta gyada kai tace "Ohk that's good, brief me a little about her, amma bana son karya Jawwad kuma kasan haka" Jay ya daga idanuwansa ya kalleta, murya can kasa yace "Mai martaba yasan da maganarta Mami, kuma har ya hadu da ita a can wani zuwa da yayi Maryland, shi ne ma ya bani shawaran hadasu su biyu for peace to reign, sannan yace In fara magana dake akan maganar tukuna" Mami tace "Ohk, er wace gari ce yarinyar?" Jay yace "Kano" Mami ta jinjina kai sannan tace "So shima Junaid ya goyi bayan ka kenan dai akan hakan?" Jay yace "Eh, yasan komai" Mami tace "Ba damuwa, er wace unguwa ce a Kanon?" A hankali Jay yace "Tudun Yola" Mami ta gyada kai tace "Shikenan, ni yanxu kwanciya zan yi Jawwad, idan na tashi anjima ma ci gaba da maganar" Jay yace "To Mami" kansa a kasa ya mike ya fita daga dakin Mami ta bi sa da kallo har ya kullo mata kofa, tana ta zaune saman darduman har bayan fitarsa da kusan minti goma sannan ta mike ta fita daga part din nata, bangaren Junaid ta nufa ta bude kofar parlorn ganin baya cikin parlor ta karasa har Bedroom dinsa, yana kwance yana danna wayarsa don tun da Jay ya shigo daxu ya tashesa bayan ya fita sai ga Mai martaba da Aunty, bayan su ma sun fita Ammi ma ta kirasa shi ne bai sake komawa baccin ba, duk idan ranan zagayowar haihuwarsa ta zo yakan je Abuja wajen Ammi ne amma wannan karan baya jin yana da strength din zuwa Abujan, ya daga kai yana kallon Mami da ta shigo dakin ko sallama babu, ya mike zaune ya ajiye wayar hannunsa tun kan ya gaisheta tana dukan tafin hannunta da yatsu biyu tace "Wato yanda kayi bakin jini cikin family ka zama kamar mujiya shi ne bari ka goga ma Jawwad shi ma a ki jininsa ko? duk wata salon mugunta da rashin mutunci ka san shi Junaid, to bari kaji in gaya maka... yanda ka ba Jawwad muguwar shawaran yayi fatali da auren Hadiyah yace shi wata daban zai aura ba ita ba haka tun muna mu biyu da kai zaka koma ka zaunar da shi ka sake basa shawaran ya bar wannan zancen, don ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba kai ne algungumin da ka zugasa Jawwad ba haka yake ba, wannan ba halinsa bane, sam bashi da tsaurin idon da zai zauna yace min shi baya son zabina yaga wata daban yana so, wallahi muddin ina numfashi a duniya babu wata yarinyar da Jawwad zai aura da ta wuce Hadiyah kuma daga ita babu
ari, ban haifar ma ko wace 'ya mace miji ba bayan Hadiyah, don in dai ita yake aure babu me rabani da shi ko ya nisanta ni da shi bayan iya shi kadai Allah ya bani, tarayyar ka da Jawwad kwata kwata babu alkhairi a cikinsa sai sharri, babu yanda zan yi ne amma na tsani ganin ku a tare har cikin raina don bakin jininka kake shafa masa ta hanyar dora sa a keken beran da kake yi, babu alkhairi a tarayyar ku sai sharri wallahi, don haka tun wuri muna mu biyu da kai ka koma ku warware wannan kullin da ku ka yi da shi don koma er uban wacece bazai aureta ba billahil azeem, sarai nasan wannan zugin ka ne ba na kowa ba tunda ka tsani ganin yana zaune lafiya da kowa, ci gabansa ma ai ba wani so kake ba, kuma muguntar ka da sharrin ka tsaff zai kare maka, Balle ni ko me zaka yi ma baya bani mamaki don kusan gado kayi....." Ajay ya sauka daga saman gadon ya shiga bandakinsa ya kulle kofar don in dai ya zauna ya ci gaba da sauraron maganganun karshen nan da take shirin yi tsaff zai mayar mata, Mami tace "To ai ba sabon abu bane, fitsara ai ba yau ka fara ba, kai da baka san darajan iyayenka ba ma balle na wasu, meye kuma baza kayi ba, in sha Allahu sai Allah ya kawo karshen alakarka da Jawwad don babu alkhairi cikinta sai sharri da hassada" Tana kai wa nan ta fice daga dakin rai bace ta tafi bangaren Aunty....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH 87
Mami ce zaune parlon Aunty cikin bacin rai ta kare maganar da take yi da cewa "Don haka nake rokon ki alfarman duk yanda za kiyi convincing Mai martaba ya rushe zancen ya nuna masa bai isa ya maida mu yara ba to kiyi, Mai martaba ya nuna masa ba wani yace lallai sai ya yi accepting auren Hadiyah da farko ba, kawai ni so nake a sace masa gwiwa a nuna maganar bazai ta
a yiwuwa ba, kinsan dai yana jin maganar mai martaba..." Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ba idan ina kokarin nuna maki illar alakar Jawwad da Junaid baki daukata serious ba, babu yanda banyi akan kiyi kokarin datse alakarsu ba amma kika ki daukar maganata da muhimmanci don baki son
ata ma Jawwad rai, ai ba shi ya haife ki ba yau in kika ce baki son yana mu'amala da Junaid kika yi masa jan ido dolensa yaji maganar ki, yanxu dai ga irinta nan, kuma kamar yanda kika fada babu me zugasa sai Junaid, ai bai son ci gabansa tun ba yau nake kokarin fahimtar dake haka, yanxu baki ga Walid ko ga maciji basa yi da shi ba" Mami ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ban sake tabbatar da Junaid
an iska bane sai yau Fulani, nayi da na sanin katse alakarsu da Jawwad da ban yi ba ta karfi da yaji" Aunty ta gyara zama tace "Bana mancewa shekarun baya har ce maki nayi ko addu'a ne ayi don farrakasu amma kika ki daukar hakan da muhimmanci" Mami tace "A'a ni duk wata sabgar shirka babu ni a cikinsa...." Aunty ta katse ta da sauri tace "Kai haba, meye kuma shirka ana zaune qlau Fulani, in aka ce addu'a ai bai wuce a ja carbi ba a roki Allah, ko kuma ka saka malaman zaure su saka ka cikin addu'ar su da bakunansu masu albarka, kai ma kuma kana yi ma kanka, amma nima ai kinsan babu ni a harkar sa
on Allah kwata kwata" Mami dai ko kallonta bata yi ba, shaff Aunty ta mance ta kawo ma Mami irin wannan maganar tsabar
in Junaid da take da kuma burin duk wani abu da zai tarwatsa sa, balle ko shirin kirki basa yi da Mami kamar yanda suke yi shekaru masu yawa da suka wuce a baya, Mami tace "To yanxu dai ke menene shawaran ki akan wannan mummunan lamarin Fulani?

Kina ganin kuwa Mai martaba zai saurarari uzurin da zaki kai masa har ma ya dauka?

Don Jawwad din fa har ce min yayi Mai martaba yasan da maganar tun ma a Amurka, kinga kuwa shi ma ya goyi bayansa kenan ai" Aunty tace "Ai ina ga mu ajiye batun yi ma Mai martaba magana tukunna, yanxu kamata yayi ma musan asalin ita yarinyar da yace maki yake so, Er wani gari ce ita, sannan waye ubanta a kasar nan, yaushe ma har ya hadu da ita ya fara son ta, informations dinta kawai ya kamata ace mun fara samu before anything else, ni ban so kin ma samu
an iskan Junaid din kin masa wata magana ba don kar ya koma ya gaya ma Jawwad, tunda kince baki nuna ma shi Jawwad din komai ba" Mami tace "Ae kuma kin san sa da shegen zurfin ciki da miskilanci, ba lallai ya ce ma Jawwad komai ba, kai bazai ma gaya masa ba" Aunty tace "Wannan gaskiya ne, a dai halinsa bazai gaya masa ba kam, yanxu kawai kara nuna ma Jawwad din zaki yi babu komai kawai yayi ta addu'a akan lamarin daga nan cikin siyasa ki bugi cikinsa mu san wacece yarinyar waye kuma ubanta a Nigeria" Mami tace "Ya ce min er Kano ce Tudun Yola" Aunty tace "Tudun Yola?

To ai can cousin sister na Bara'atu take da zama, nan gidan mijinta yake" Mami tace "Kin ga ya zo mana gidan sauki kenan" Aunty tace "Ai kuwa dai ya zo mana gidan sauki, abinda yayi saura yanxu ki lallabasa cikin dubara a san a ina suke a cikin Tudun Yola" Mami tace "Kinsan sa da kaifin tunani fa Fulani, yana jin tambayoyin sun fara yawa zai
ago wani abu" Aunty tace "In yasan wata ai bai san wata ba, number yarinyar kawai zaki nema a wayar sa bakin ki alekum" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan, bari in je koma ya ake ciki dai zaki ji ni" Daga haka Mami ta mike ta nufi hanyar fita babban parlon, Aunty tayi murmushi tana girgiza kafa a hankali, ai ko tana ga yanxu ne dai dai lokacin ma da ya kamata ta farraka Jay da Ajay don da ta dau alwashin duk wani tsabgar Mami bazata sake shiga ba, duk da Jawwad din ma ba wai sonsa take ba, amma gwara dai shi sau dubu akan Junaid, farrakasu da zata yi shi ne zai sa rayuwar Junaid ya kara daidaicewa yanda take fata a kullum.
Chapter 188 · 0% Book details