← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 191

Sashe 55

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Khaleesat na zaune gefen gado tana kallon Jay dake kulle mata akwatunan ta, yana dagowa ta juya a hankali tana kallon window dake dakin, ya dau boxes din biyu yace "Let me get them in the car" Daga haka ya fita daga dakin, ta jinginar da kanta jikin gadon dakin har ya dawo, yana kallonta yace "Hope you didn't forget anything Halysaah" Ta gyada masa kai, yace "Ok, you know what? in dai muka fita kika hadu da AJ thank him and tell him you are leaving" With a smile on his face ya kare maganar yana kallonta, ta sauke idonta tana wasa da fingers dinta a hankali tace "Ohk" Yace "Good gal, mu tafi" Mikewa tayi ta bi bayansa tana rike da karamin handbag dinta walking slowly, suna fitowa walk way din babban corridor din sama sai ga AJ ya taho daga parlorn dake nan sama, Jay ya kalli kayan jikinsa ganin iri daya suka sa kuma tun safe ba wai sun hadu bane kawai coincidence, tunda AJ ya kallesu sau daya ya ci gaba da tafiyarsa, Khaleesat ta
an kalli Jay, ya gyada mata kai sannan ya nufi stairs, ita dai tana tsaye ta jira har AJ ya iso kusa da inda take sannan ta sauke idonta a hankali tace "Good morning, i want to thank and appreciate you for everything, i will be leaving today in sha Allah" Without looking at her yace "Jay dai zaki ma godiya ni me na maki" Ta bi sa da kallo har ya fara sauka downstairs, sai bayan da ya sauka sannan ta tabe baki ta bi bayansa tana tafiya a hankali, parlor ta tarar da Jay zaune yana jiranta, Jay ya bi AJ da kallo yace "Flight din naka na gobe ne amma?" AJ yace "I am leaving for the airport now" Jay yace "Ohk, zaka jira inyi dropping Housemate dina sai in dawo in kai ka airport din?" AJ yace "No, don't bother" Daga haka ya fita daga parlon tare da daya daga workers din gidan wanda da alama shi zai yi dropping dinsa airport din, Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, ya lura tunda gari ya waye jikinta yake a sanyaye, yana kallonta yace "Are you Okay Halysaah?"
an murmushi tayi tace "Sure" yace "Kin gaya ma kawarki yau zaki tafi?" Khaleesat ta gyada masa kai tace "Na gaya mata" Yace "Ok, ita yaushe zata tafi?" Khaleesat tace "Yayanta yace ta bari ranan lahadi" Jay yace "Kin tabbatar baki mance komai ba kuwa a sama?" Ta gyada masa kai, yace "Je dai ki sake dubawa Housemate" Bata masa musu ba ta juya zata koma sama yace "Toh ki ajiye jakar taki mana" Ta dawo ta ajiye jakarta a kan kujera sannan ta wuce sama, Mikewa Jay yayi ya tafi gun jakar ya dauka ya bude sannan ya ciro Dala dubu daya a aljihunsa ya sa mata a jakar ya kulle ya mayar ya ajiye mata ya koma ya zauna, ba a dau lokaci ba Khaleesat ta dawo downstairs tace "Ban manta komai ba" Yace "Good" Mikewa yayi bayan yaji fitar motar AJ don dama jira yake yaji sun fita daga gidan, yana kallonta yace "Mu je, ur Flight is in an hour time in sha Allah" Khaleesat ta gyada masa kai ta dau handbag dinta, tana biye da shi suka fita daga parlon gidan, har gari ya fara duhu, suna shiga motarsa ta mika masa wayarsa dake hannunta kar ta manta, a hankali tace "Thank you so much" Ya amshi wayar sannan ya dauko pin a motar ya cire sim card din cikin wayar snn ya mayar mata yace "Your ticket is on the phone, in kin koma Nigeria sai kiyi SIM card replacement, in kuma baki son wayar sai in sa a kai maki sabo a Nigeria" Tayi murmushin karfin hali tace "Saboda me zance bana so, nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "To ai nasan ku mata da son sabon abu" Ta girgiza masa kai kawai tana murmushi bata ce komai ba, a haka suka bar gidan suka dau hanyar airport da tunani iri iri a ran Khaleesat, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya ga wani daren, ko me zata je ta tarar a Nigeria sai Allah, it's now that reality is dawning on her, bayan sun isa airport Jay ya juya ya kalleta yace "You can sort ur self out ba sai na shiga ciki ba ai ko?" Ta gyada masa kai, da kyar tayi karfin halin cewa "Thank you so much Housemate, Allah ya saka da alkhairi da abubuwan da ka min" Kasa ci gaba tayi saboda hawayen da ya fara sauka a idonta she just can't thank him enough, gani take words aren't enough to thank him, shi dai Jay kallonta kawai yake with surprise, can yace "C'mon Halysaah, to menene abun kuka?" Ta kasa basa amsa ta rufe fuskarta da gyalenta tana kuka a hankali, Jay ya kwantar da murya yace "Pls ki dena wannan kukan, in nasan abinda zaki yi kenan i will have just order either Lfyt or an Uber that will be taking you to the airport" Dena kukan tayi tana goge hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsa, ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido taga Luggages dinta dake booth zai dauko, a hankali ta bude side dinta ta sauka daga motar tana bin sa da kallo, daya daga porters dake wajen ya ba luggages din nata ya shigar mata da shi ciki ya hada masa da tip dinsa, ita dai Khaleesat kallonsa take, ya juya ya dawo kusa da ita yace "Alright safe trip Halysaah, idan kinyi replacing Sim card dinki sai ki min magana ta WhatsApp, my regards to everyone back home" Ta sauke idonta a hankali tace "I will miss you" sai bayan da ta fada haka ita kanta tayi realizing abinda ta fada, sai kuma ta kasa dago kanta, ya
an yi murmushi yace "I will miss you too Housemate, in sha Allah next week i will be in Nigeria too" Bata iya ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai ta juya a hankali ta bi bayan porter din da ya shigar mata da luggages dinta zuwa check in counter for her Boarding pass, kasancewar Business class ticket gareta all the processes were smooth and straight for her, daga karshe ta nufi waiting lounge don in 15 mins time za su fara boarding jirgi, tunda ta shiga lounge din take kallon wanda ta gani zaune da mamaki, ta kalli boarding pass dinta sannan ta kalli na hannunsa taga iri daya, wayarsa kawai yake dannawa, ganin bai ganta ba ta juya a hankali ta koma wani wajen daban ta zauna ta inda ma bazai ganta ba, bata sake waigen inda yake ba, iya drink kawai ta amsa a lounge din unlike wasu da ke ta cin abinci duk a cikin kudinsu, gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa saboda damuwa, da ta tuna inda zata sae taji har wani juya mata kanta yake kamar bata da lafiya, ta sa
a wancen a ranta ta kwance har daga karshe aka fara boarding din jirgi, sai da Khaleesat ta jira AJ ya fara tafiya sannan ta mike ta bi bayansa walking slowly, Har seat dinta wata Flight Attendance da ke welcoming dinta da fara'a ta kai ta, hada ido Khaleesat tayi da AJ that was sitting few seats away from hers, ta sunkuyar da kanta ta zauna Seat dinta tana mayar da Amenity kit din da aka ajiye mata a gefe, AJ ya kasa daina kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, he can't even explain what he is feeling at that moment don bai ta
a ganin wanda ya gama rena masa wayo a duniyar nan kamar Jay ba, jiya wajen karfe sha biyun dare ya farka ya gansa yana duba masa waya ashe ticket din da ya siya yake dubawa, he felt like just leaving the plane at that moment, after a while kawai ya dauke kai yana kara gyara barrier din da zai sa ko hangota bazai dinga yi ba, Ita ma Khaleesat ko by mistake bata sake kallon direction din sa ba, a haka jirgin ya tashi, Khaleesat bata ta
a jin motion sickness ba tun da ta fara tafiya a jirgi amma yau ko don saboda pressure din da ta saka ma ranta ne kawai sai ji tayi as if she wants to throw up tun da jirgin ya daga, ta cire seat belt dinta da sauri ta mike ta nufi Lavatory din jirgin almost running, shi dai ya bi ta da kallo, Flight Attendance din da ta kawo mata Hot towel kafin tashin jirgin ne ta bi bayanta tana tambayar if she's okay, Khaleesat ta gyada mata kai kawai bayan ta fito daga Lavatory din, AJ ya bi ta da kallo har ta koma seat dinta ta zauna sannan ya tabe baki, Flight Attendance din ta duka kusa da ita tana tambayarta ko tana bukatar wani abu ne, Khaleesat ta girgiza kai tana murmushin karfin hali tace "Thank you, i am okay" Matar ta sake tafiya sai ga ta ta dawo da ruwa da orange drink, sai kuma wani drink daban duk a glass daban daban akan tray daya, ta duka tana mika ma Khaleesat ta dauki wanda take so, glass din ruwa kawai Khaleesat ta dauka ta mata godiya sannan ta sanar mata bazata ci abinci ba all throughout the flight don ma kar matar ta sake dawo mata, gani take tana cin abu zata yi aman da bata yi ba daxu, gyara kujeranta tayi ta kwanta ta lulluba da blanket din da jirgin yayi providing for business class passengers, nan da nan bacci ya dauketa, da za su sauka Turkey wajen karfe hudun asuba sai da wata Flight Attendance daban ta zo ta tasheta ta sanar mata jirgi zai sauka, Khaleesat ta mike zaune da kyar don ciwo kanta ke mata, tayi fastening seat belt dinta, bayan sun sauka Istanbul ta bi AJ da kallo har sai da ta daina hangosa sannan ta mike ta dau handbag dinta da waya ta bi bayansa tana tafiya da kyar leaving her Amenity kit behind, jiran awa biyu za su yi a Business Class waiting lounge na airport din kafin a canza masu jirgin da zai kai su Nigeria, ta riga AJ shigowa lounge din kilan masallaci ya tafi, ita ma tana ganin lokacin sallahn asuba yayi ta tafi tayi sannan ta dawo ta zauna a business lounge din, after like 15 mins sai gashi ya shigo, not far away from her ya zauna da ruwan gora a hannunsa, Ita dai ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune ta daura handbag dinta a kafarta, she is having a terrible headache a lokacin, after almost 30 mins of sitting wani
an Nigeria ya dawo kusa da ita ya zauna, wanda shi ma daga nan Turkey zai je Nigeria a Business class, kuma jirginsu daya kamar yanda ta ga ticket irin wanda ta amsa bayan sun sauka Istanbul din a hannunsa shima, yana kallonta yayi mata sallama cikin nutsuwa, ta
an kallesa sannan ta amsa, yace "Guess you are coming from America right?" Tace "Uhm" Yana kallon Flight ticket dinta yace "Oops you are having the same name as my Mum, can i call you Jiddah instead of the real name?" Khaleesat dake sauraronsa without looking at him tace "Ohk" Yana murmushi yace "Alright, are you traveling alone Jiddah?" Ta girgiza kai tace "No" Ya buda ido yace "Ohk with who?" Ta kalli direction din AJ, shi ma mutumin ya kallesa suka hada ido don kallonsu kawai Ajayn yake yana jin conversation dinsu, mutumin na murmushi ya tashi yaje ya gaisa da AJ sannan ya koma ya zauna, shikenan Khaleesat ta samu lafiya, don bai sake ce mata komai ba kawai danna wayarsa yake tayi tunda shi dai bai san ko waye Ajayn a gunta ba, daga karshe ma ya tashi ya bar wajen, at last aka fara boarding din jirgin da zai kai su Lagos Nigeria daga Istanbul, Usman ya juya ya kalli Khaleesat da ta mike tana rike da handbag dinta, har AJ ya wucesu sai kuma ya tsaya amma bai juyo ba, ita dai tana tafiya a hankali har ta isa inda yake tsaye sannan ya ci gaba da tafiya tana biye da shi, har jirgi ya tashi Usman dake zaune not far from Khaleesat but close to AJ bai ce mata komai ba, this time around ma dai bacci kawai tayi har zuwa Nigeria.
Chapter 55 · 0% Book details