Sashe 115
Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To zan yi maganinsu gaba daya, in dai karatu ne kamar Khaleesah taje Amurka ta karasa in har ina numfashi, Allah ya kai mu anjima da yamma, Alin ai zai dawo daga zaman kashe wandon da yake yi a kasuwa, zan je har gidan in samesa inji ko na tauye masa karatunsa duk da talauci na, in de ni na amince taje to ko wani
an iska ma kar ya amince" Nenne na kai wa nan ta mike ta jawo kofar dakinta ta kulle da kwado, sannan ta dau mayafinta sabo dake rataye saman igiya ta yafa, ta dau handbag dinta ta saka makullin kofar a ciki, ta zura takalmanta ta nufi kofar fita daga gidan tana taku dai dai don sabuwar atamfa ce a jikinta, Aunty Farida ta bi ta da kallon mamaki tace "Wai fita zaki yi ne Nenne?" Ba tare da Nenne ta juyo ba tace "To me zan maki, anguwa har uku zan je yau da kika gan ni, bazan zauna a banza ki bata min lokaci ba, in ba gulma ba ganinki nake yi a gidana, ni dai in kin gama zaman kin fito ki ja min kyauren gidana kar almajirai su shiga su min sata" Daga haka Nenne ta fice daga gidan, murmushi Aunty Farida tayi ta mike ta nannade mata tabarmanta ta ajiye sannan ta daura nikab dinta, bin bayanta tayi da sauri don jadadda mata kar tace ita ta zo ta gaya mata maganar don tasan tsaf sai yayarta ta kullace ta.
_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Read my book "HALYSAAH" on ArewaBooks, Platform available: "app only" :: https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
HALYSAAH 54
Wajen karfe shidda na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Ummanta tana yanka mata alaiyahu a cikin roba, stepsisters dinta Labeebah da Lamisah na can zaune su ma daga bakin kofar dakin Mama Shatu da kawayensu sai hira suke suna shewa duk sun cika tsakar gidan kai kace gidan biki ne, Mama Shatu da Mama Zubaida su ma suna tsakar gidan don da su ake hiran da kawayen 'ya yan nasu, magana daya biyu sai su kwashe da dariya, yawanci kuma duk habaici suke jefa ma Umma da Khaleesat, ita dai Umma tana zaune gaban Coal pot tana kwashe tuwon masara da ta gama tukawa, Aunty Farida kuma ta tafi Hotoro tun bayan la'asar da su Noor, Nenne ce ta shigo gidan rataye da jakarta a kafada, lkci daya gidan yayi tsit, a takaice Nenne ta amsa gaisuwan da su Mama Zubaida da Lamisah da kawayensu ke yi mata ta nufi gun Umma tace "Zahra'u Alin ya dawo ko be dawo ba?" Umma ta gaida Nenne sannan tace "A'a bai dawo ba tukun Nenne, sannu da zuwa" Nenne tace "Kin gan ni nan daga Sheka nake daga can na tafi
an Agundi, ni ce har Na'ibawa yau, tun safe na bar gida sai yanxu nake dawowa 'yan adaidaita sahun kano dai sauransu yawo da bindiga kawai...." Murmushi kawai Umma tayi tana ci gaba da kwashe tuwon da take yi, Nenne ta jawo kujera ta zauna tace "Gidan Katime me Aya na tafi a Sheka, in gaya maki me Aya dai kafafuwanta sun mutu murus Zahra'u, ko tashi bata iya yi, babu yanda ban yi da matar nan ta rage cin nama ba amma taga kamar bakin ciki nake mata don mijina baya kawo min, to yau ni da ban ci nama ba gani da kafafuwana biyu rass, ita kuwa duk sun mutu, wai tana ganina ina taku dai dai na shigo gidan sai ta fashe da kuka, ni dai bata ban tausayi ba wallahi, sai kinga yanda take mana fafa da nama lokacin, kullum kya ji kamshin tafashen nama a gidanta, mu sai dai mu watsa er daddawa a miya" Umma na girgiza kai tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Nenne tace "Ba batun Allah ya bata lafiya ba, ai duk kafafuwan sun rube, da kyar in baza ace za a yanke mata su ba tunda ko motsa su bata iya yi " Su Mama Zubaida gaba daya kunnuwansa na kan labarin da Nenne ke ba Umma, Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne ta juya tana kallonsa, can ta mike ta nufesa tace "Yanxu Ali baza ka hakura da fita kasuwar nan ba tun da ba wani abu kake yi a can ba sai zama cikin rana da iska?
Ka dubi yanda duk kayi bakikirin kamar baka ta
a haske ba a rayuwarka Ali, tunda ba aikin fari gareka ba balle ba
i a kasuwar ka hakura da zuwa mana" Gaisheta kawai yayi ya dau buta zai debi ruwa ya fita waje ya zauna ya jira Magariba, Nenne ta tabe baki tace "To wajen kai da matar ka Zahra'u na xo" Umma ta juya tana kallon Nenne jin abinda tace, Shi ma ya tsaya yace "To lafiya dai ko?" Nenne tace "A ina lafiyar take, ba sai kun nemi zaman lafiyar za a zauna lafiya ba, labari na samu wai masu kare hakkin 'yan Adam sun zo gidan nan sun ce za su ci gaba da daukar nauyin karatun Khaleesat a Amurka saboda tausayin abinda tsinannen mutumin nan Awdul yayi mata, to amma wai saboda kai da Zahra'u yan bakin ciki ne sai ku ka gwalesu ku ka koresu, da wanne ku ke son yarinyar ta ji fisabilillahi?
Da mayar da ita bazawara da aka yi tana da karancin shekaru ko kuma da asaran karatun ta da kuke kokarin yi mata?
In ita Zahra'u jahila ce bata yi karatun boko ba kai ma Jahili ne Ali?
Ina ne ban shiga nayi aikatau ba don kayi karatu?
To wallahi ko karshen bangon duniya ne sai Khaleesat ta koma ta karasa karatun ta tunda har aka ce za a dau nauyinta babu ko sisin ku, to ina ma ku ka ga ko sisin" Malam Ali dake ta kallon uwar tasa yace "A ina kika ji wannan zancen Nenne?" Nenne tace "Labarin duniya na buya ne dama?
Ina zaune yan Mariri suka zo suka tsegunta min har unguwan da naje yau...." Mama Shatu ta kalli Mama Zubaida da ta saki baki tana sauraron Nenne, Mama Zubaida ta kasa daurewa ta gyara zama cikin kwantar da murya tace "Amma Nenne na farkon ma ba a wanye lafiya ba shi ne za a sake na biyu?
Dama gashi duk garin nan kallon makwaita masu son abun duniya kawai ake mana, ko ina sai zaginmu ake tun da aka samu labarin sakin walakancin da aka yi ma Khaleesat, ana ta cewa ubanta ne ya ja mata, A rayuwar nan yanxu fa in ba iyayenka ne za su yi maka dawainiya ba duk wanda yace zai dau dawainiyar ka sama ta ka to da wani abu da yake hangen zai samu a gare ka ne, Khaleesat fa 'ya mace take ba namiji ba Nenne, kuma ba komai ke rudar maza akanta ba sai kyanta da kalan fatar ta sun ga buzuwa, shi kenan saboda son abun duniya sai a zuba ido har sai yarinyar nan ta lalace tukunna, Abdul ya gama nasa ya samu abinda yake so ya sako mana ita sai kuma yanxu ace ga wani ma ya zo wai zai ci gaba da daukar nauyinta?
Haba sam batun nan babu tsari a cikinta, shikenan ita kuma haka ta zama kamar Tasi...." Nenne ta kundumo wani zagi tace "Toh duk wanda ya fasa fadin abinda ke ransa akan Khaleesah Allah ya tsine masa albarka, kuma in de karatu ne kamar tayi ta gama sai dai bakin ciki ya kashe duk wani shege wallahi, ko ma ina za a kai ta a kai ta ni na amince ta je, ai ita tasan tarbiyyar da muka yi mata in ma ta gantalar da tarbiyar ita da Allah, kuma gobe gobe zan sa a kira min ba
ar kawar tata ta zo in gaya mata uban Khaleesah ya amince koma waye zai dau nauyinta ya dauka, taje can ta ci gaba da karatun ta, ai gwara tayi nesa da mu ko bakin cikin dake damunta a rai zai ragu, mu kanmu in tana ganinmu takaici da bakin ciki take don ba mu da wani babanci da Awdul a wajenta tunda mu muka ja mata komai, gwara ta koma ta gama karatunta ta dawo da kwalinta don bazata tashi a tutar babu ba, shi kansa Awdul din yana samun labari an samu wanda ya maidata Amurka ta ci gaba da karatu sai bakin ciki ya kusa kashe shegen, a nan kuma zai san ba a banza Khaleesah take ba farin jininta ya shahara" Nenne na huci ta juya ta kalli Umma tace "Ke kuma Zahra'u halan tallan alalen ki ke da niyyar dora mata da kike mata bakin cikin komawa ta karasa karatun?
To kamar yanda kike takama kina da iko da ita nima haka tunda ni na haifi ubanta, ban ga shegen da ya isa yace bazata koma ta karasa karatun ta ba" Ita dai Umma bata ce ma Nenne komai ba, Malam Ali dai na tsaye rike da buta a hannunsa yana kallon uwarsa, can dai yace "Amma dai Nenne sam babu tsari ace mun sake barin yarinyar nan ta bar kasar nan da sunan wani zai dau nauyinta bayan duk abinda ya faru, me kike son jama'an gari su ce a kaina?