← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 191

Sashe 36

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kinsan yanzun ma ba karamin aikinsa bane sai ya iya kamo hanya ya zo" Khaleesat ta dafe kanta tsabar she is confuse, Safiyyah tayi shiru, can kuma ta kyabe baki tace "Kuma haka ne ba kai ne da shi ba sai ya iya kamo hanya tunda ba su dau kudi bakin komai ba, kawai anjima ki kirasa sai ki kisa abinda zaki ce masa da zai gamsar da shi, kuma kina iya cewa baki da lafiya gantalallen ya kamo hanya, ni dama ya tafka wani tsiya America su kwace visan sa kowa ya huta" Duk da damuwar da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya, Safiyyah tace "Allah kuwa, ban ki ba ya zo ya maki hauka da kaina zan kira masa 911 wallahi" Khaleesat dai tayi murmushin karfin hali kawai, wayar Safiyyah ne ya fara ring ta duba taga Mustapha ke kiranta, turo baki tayi tace wannan mutumi yana takura rayuwata a kasar nan, wai daga cewa zan kawo maki abinci ya zata yawo zani shine fa ya biyoni, kema baki ji ba wai ki dawo gidansa da zama, salon wataran matar ta saka mana guba a abinci mu ci mu mutu gaba daya, yanzu haka fa ko ga maciji bama yi da ita,
an fitar nan da yayi da ni muna nan dake sai ya zamar masa matsala, tana can ta cika tayi fam tana jiransa, ko a jikina kuwa, sai na ma lallabasa ya kai ni ya siya min ice-cream ta yanda zata ga na dawo rike da leda" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Safiyyah ta mike tace "Bari in je, sai mun hadu Monday in sha Allah" Khaleesat ta rakata bakin kofa a hankali tace "Thank you Safiyyah" Safiyyah tace "No thanks kawata, ki ce ma Housemate dinki na tafi" Khaleesat ta gyada mata kai, a haka Safiyyah ta fita daga gidan, Khaleesat ta kullo kofar a hankali, abincin da Safiyyah ta kawo mata ta dauka ta kai fridge da wanda Housemate dinta ya sa ayi mata takeaway.

Khaleesat ta fito wanka kenan taji Housemate dinta na knocking kofarta, ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, yana rike da laptop dinsa yace "Good night Halysaah, i am sleepy" Khaleesat tace "To sai da safe, thank you for the dinner" Yace "No thanks.... kin kira BF din naki?" Khaleesat taki basa amsa, yace "Amma bari in tambayeki, a ina kika hadu da gayen nan ne?

Don't know ko na ta
a tambayarki kwanaki...." Khaleesat ta jingina da kofa without looking at him tace "Back home" Yana gyada kai yace "I see, ni at first na zata you are not Nigerian, was thinking you are from Niger or Chad, probably Shuwa Arab" Khaleesat ta dinga kallonsa, bata san sanda tace "Why?" Yace "Na ganki kamar Buzuwa" Khaleesat ta sauke idonta bata basa amsa ba, yace "Ok, i will be on my way, good night" Daga haka ya juya ya bar wajen, a hankali ta sauke idonta sannan ta kulle dakinta ta jingina jikin kofar, she stood there for almost 5 mins kafin ta karasa cikin dakin ta cire hijab din jikinta ta ciro sleeping dress dinta ta saka, sanitary pad dinta dake gaban dressing mirror ta dinga kallo, sai kuma ta dauke daga wajen, sai da ta kwanta sannan tayi dialing number Abdul gabanta na faduwa, har ya katse bai daga ba dama tasan ba lallai ya daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, ta bude WhatsApp tayi masa magana ta nan, reply yayi mata yace "I don't have ur time so do not border me" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta kashe wutan dakin sannan tayi kwanciyar ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa.

Washegari bayan Khaleesat ta gama azkar din da take yi, ta jawo wayarta a hankali, tunda ta tashi jikinta yake a sanyaye don mafarki tayi Abdul ya zo kamar yanda ya zo wancan lkcn still kuma ya sake haduwa da Housemate dinta a gidan, ba karamin daga mata hankali mafarkin nan yayi ba, WhatsApp dinta ta bude bayan tayi deciding zata masa message din ban hakuri duk da bata saka ran reply dinsa ba, cause it won't be funny if her dream comes true, tana shiga WhatsApp din ta ga ya turo mata hotuna kusan biyar tun 3 hours ago, bude message din tayi zuciyarta na bugawa don bata san hotunan menene ba, nan taga har da message yayi mata kafin yayi sending hotunan, ta fara downloading hotunan at the same tana duba message din da ya rubuto mata kamar haka "So now, kina kokarin nuna min cewa i made the mistake of letting you go to America to study right?

Kin mance wacece ke ko? kin mance daga inda kika fito, then that is so foolish and stupid of you Khaleesat, amma ina me tabbatar maki idan har kika ci gaba da daukata for granted kamar yanda kike yi kwanan nan sai na sa kinyi da kin sani wallahi" Lkci daya Hawaye ya cika idon Khaleesat, ta sauke idanuwanta kan hotunan da ya turo mata, daya hoto ne da shi yayi mata a bakin kofar dakin Ummanta, yana zaune kan tabarma ta duka gabansa zata ajiye masa ruwa a Cup shine ya dauketa hoton, shekaru hudu da suka wuce kenan, she look so so young and meek a hoton, hoto na biyu kuma tana wajen debo ruwa a nan unguwansu ya zo ranan ya ganta a wajen, ita bata ma san yayi mata hoton ba ga zaninta duk a jike, hoto na uku kuma tana ba
in murhu a tsakar gidansu tana juye alalan siyarwan Ummanta a Cooler shi kuma ya zo gidan ranan, duk bata san ya mata hotunan nan ba sai yau da ya turo mata ta gani, hoto na hudu kuma ranan da ya kai ta zata zana Jamb ne, jamb din da bata ma yi amfani da shi ba daga karshe, sai kuma hoton karshe na ranan da zai kawota USA for the first time, looking at all the pictures da kuma looking at her now zaka ga banbanci me tazara sosai, infact the difference is very obvious don a yanzu she looks more beautiful, matured, nourished and well taken care of, yanzu skin dinta har wani glowing yake, in ma ba ka santa ba bazaka taba cewa ita ce a hotunan ba, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta hade kanta da pillow tana kuka sosai, but like seriously Abdul bai yi deserving haka daga gareta ba, but did she also deserve irin abubuwan da yake mata?

Kuma tun asali haka yake mata, Kuka sosai tayi babu me rarrashinta, bata ma san me take ji a zuciyarta ba a lkcn, she cried profusely for almost 30 mins, daga karshe tayi karfin halin mikewa zaune ta dau wayarta, she don't even know where to start from, Voice note ta fara masa muryarta na rawa trying to tell him she is sorry, amma bata kai ko ina a basa hakurin ba ta fashe da kuka sosai, cikin kuka ta ci gaba da basa hakurin, sai da tayi masa Voice note uku sannan ta ajiye wayar still crying....
07087865788
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
18.....

Wajen karfe goma na safe Khaleesat na kwance dakinta idonta rufe duk da ba bacci take ba, ji tayi ana kwankwasa kofa, kamar bazata iya tashi ba daga karshe dai ta mike ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka, tana tafiya a hankali ta fito parlor, ta tagar parlon ta duba ta ga Housemate dinta ne, ta karasa ta bude kofar, Yace "Sorry na tashe ki kina bacci, i forgot the key at home" Ita dai bata yarda sun hada ido ba a hankali tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how are you feeling now?" Ta juya going back to the parlor tace "Alhamdulillah" Ya bi ta da kallo sannan ya shiga parlorn, dakinta ya ga zata koma yace "Halysaah" Ta tsaya, after few seconds ta juyo but couldn't let her eyes contact his, shi dai kallonta kawai yake, ya karasa inda take tsaye yace "What happened?" Girgiza masa kai kawai tayi, lkci daya hawaye ya fara sauka idonta, ya dauke kai na 'yan dakiku kafin ya sake juyowa ya nuna mata kujera yace "Sit" Komawa tayi ta zauna, ya zauna shima yana kallonta yace "Tell me what's wrong" Ta sunkuyar da kanta, yace "Are you sick?" Ta girgiza masa kai, yace "Wannan saurayin naki ko?" Ta kasa basa amsa wasu hawayen na sauka idonta, sai kuma ta fashe masa da kuka, mikewa yayi yace "Waye ya hadaki da wannan mutumi ne?

Why did u allow him know ur weak point?

Why are you always crying because of him?
Chapter 36 · 0% Book details