← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 191

Sashe 88

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Cikin wannan yanayin Khaleesat tayi kwana uku a gidan tare da Abdul, a wannan kwanaki ukun kuwa duk da halin da take ciki a haka yake sakawa taje tayi masu girki a kitchen wai shi baya son abincin restaurant, Khaleesat bata ta
a fatan kar period dinta ya dauke ba kamar irin wannan lokacin, she wish she will keep on flowing continuously like the woman with the issue of blood amma tasan dole ya dauke nan da kwana biyu don bata wuce 5 days in tana period, sosai hankalinta ke kara tashi idan ta tuna hakan, yau tunda gari ya waye tayi wanka ta saka pad take kwance kan gado saboda azababben ciwon kan da take, all these pass days bata wani samun baccin kirki da daddare tsabar damuwar da ta saka ma kanta da tunane tunane, daga karshe dai haka ta daure ta fita zuwa kitchen da kyar don dora breakfast kafin ya fito daga dakinsa kamar yanda yayi mata umarni 2 days back, tana fita parlor ta leka compound din gidan taga babu motarsa alamar ya fita, ta murda kofar parlon taji a kulle kamar yanda tayi tunani, Zaunawa tayi kan kujera ta dafe kanta hawaye masu zafi na zuba idonta, after a while ta mike tana shesshekan kuka ta wuce kitchen din, tana cikin hada breakfast taji alamar shigowar motarsa gidan, after a while aka bude kofar parlon,
asa kunne tayi jin kamar muryar mace take ji a parlor, can kuma taji tsit, ita dai ta ci gaba da abinda take yi jiki babu kuzari har ta gama ta tsaftace kitchen din sannan ta juya zata fito ta kusa cin karo da wata mace in her late 30's zata shigo kitchen din, daga sama har kasa matar dake tsaye kofar kitchen din take mata wani irin kallo da za a iya kira da kallon kaskanci, ita dai Khaleesat tunda ta kalleta sau daya ta sunkuyar da k
anta ita kanta bata san sanda ta gaisheta ba don duk ta rude gashi kuma taga suna kama da Abdul duk da bai ta
a nuna mata wani nasa ko da a hoto ba, a walakance matar tace "Da ban kwana ba zaki gan ni munafukar Allah, Er gidan matsiyata ma ci amana....

A gidan ubanki kika san ni da zaki gaisheni?" Sai a sannan Khaleesat ta sake daga kai tana kallonta da mamaki cause kalmomin matar kawai a bazata suka zo mata, bata san sanda tace "Ki zageni amma banda iyayena...." Bude baki Meema tayi da mamaki tana kallonta ganin guts dinta, kafin tace komai Khaleesat ta bi gefenta zata fice daga kitchen din wanda saura kiris ta bangajeta wajen fitan, cikin zafin nama da bacin rai Meema ta fincikota ta dawo da ita gabanta sannan ta sauke mata wani wawan mari ta shakota tana kokarin kai ta kasa ta nakadi banza, Khaleesat ta kwala wani kara, dai dai isowan Abdul wajen, lkci daya yanayinsa ya canza don a kan idonsa yayar tasa ta sauke ma Khaleesat mari sannan ta shakota tana kokarin dukanta, cikin daga murya yace "Zo ki fita ki bar min gidana Amina, how dare you?

Me tayi maki zaki mareta haka?

Baki da hankali ne?

Get out of my house pls, fita ki bani waje" Sake baki Meema tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin zafin nama ya tafi ya bude kofar parlon kirjinsa na sama da kasa yace "Ki fita nace Amina kar in rama mata" Cikin karfin hali Meema ta dafe kirjinta da hannu daya tace "Abdallah ni kake cewa in fita a gidanka?" Ya jefar da wayar hannunsa yana huci ya nufeta kamar zai kai mata duka cikin daga murya yace "Na ce ki fita din ko gidanki ne?

Get out of this house before i loose my control Amina, gerrout" Ita dai Khaleesat makalewa tayi jikin kofa jikinta na rawa, sum sum sum Meemah ta karasa ta dau handbag da karamin travelling bag dinta don dama daga airport yaje ya daukota saukanta garin kenan, ta nufi kofar fita parlon sannan ta juya tana kallonsa da mamaki tace "Abdallah ni kake daga ma murya kake cewa in fita in bar gidanka akan wancan matsiyaciyar?

Har kake ikirarin zaka kai min hannu?
Chapter 88 · 0% Book details