Sashe 119
Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Allah ya sauwake, ita kuma uwar Abdul wallahi matsiyaciya ce er wahala, har ta iya kamo hanyar Mariri akan kudin da ba ita ta bada ba, in kin bibiya ma
an nata bai sani ba ta kamo hanya, ki min sending shegen account din nata da ta bar maki" Daga haka Safiyyah ta kashe wayarta, Khaleesat ta jawo handbag dinta tana goge hawayen da ya taru idonta, ta bude jakar ta ciro takardan account details din da Mom din Abdul ta bar mata, tura ma Safiyyah account din tayi ta message sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta koma ta kwanta, ita dai Aunty Farida bata ce komai ba don duk ta fahimci conversation din nasu.
Washegari Khaleesat na idar da sallan asuba kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tayi picking call din ta kai kunne, a hankali tace "Good morning Safiyyah" Safiyyah tace "How was ur night?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah tace "Na tashi yanzu naga Housemate dinki ya tura min receipt din 10M da ya tura a account din da kika turo min jiya, he sent the receipt via my WhatsApp, ba ki yi activating WhatsApp dinki ba da sai in tura maki ki tura masu, sai su san su ne matsiyata" Kasa cewa komai Khaleesat tayi hawaye ya fara sauka idonta, Safiyyah tace "Ko kuma bari in tura ma Aunty Farida receipt din kawai since she is on WhatsApp" Khaleesat ta gyada mata kai da kyar tace "Nagode" Safiyyah tace "Kuka kike yi ko?
Kina da aiki, ni dai sai anjima, make sure ki fito gida da wuri kin san Flight dinmu zuwa Abuja karfe daya ne" Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Umma na kallon Khaleesat tace "Wai me ya faru?" Khaleesat na share hawayen da yaki tsaya mata tace "Ta ce ya tura masu kudin ne, zata tura ma Aunty Farida receipt" Shiru Umma tayi ta rasa abun cewa, kana ganinta kasan jikinta yayi sanyi sosai, Aunty Farida dake zaune kan darduma tace "Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi ya kare sa sharrin masu sharri, Allah ya mayar masa da dubban abinda ya kashe maki, yanda ya rufa maki asiri Allah ya rufa masa shi ma" a hankali Umma tace "Ameen ya Allah" Mikewa Khaleesat tayi don dama ta gama azkar din da take yi, ta kwanta kan gadon Umma har sannan hawaye yaki dena sauka idonta.
Da safe wajen karfe tara Aunty Farida na bude WhatsApp dinta taga Receipt din da Safiyyah ta tura mata, tana kallon Khaleesat tace "Yanxu ta ya za a tura masu receipt din su gani Khaleesat?" Umma tace "Ba kina da number Abdul din ba?
Ki tura masa ta WhatsApp din kawai" Khaleesat dake cin wainar da Umma ta sa aka siyo mata ta daga kai ta kalli Umma, sai kuma ta girgiza kai a hankali tace "A'a Umma kar a tura masa, ba sun ce za su zo da safe ba, in sun zo sai a nuna masu receipt din" Umma tace "Saboda me?
Ba kudinsa bane kuma shi ya aiko su karbar masa?" Aunty Farida ta kalli Umma tace "Suka aiko kansu dai Umma, don Abdul dai a yanda yake ji da kansa bazai ce a zo a amsar masa miliyan goma ba, dama sun san da kudin kuma kilan sun san bazai ce zai amsa ba shi yasa suka taho su amsa" Khaleesat tace "Shi yasa nace kar a tura masa receipt din, don nasan ba shi yace su zo ba" Umma tace "To ko ma dai yaya ne ai kudinsa ne, ni bana son su sake dawo mana nan su mana tijara makota na ji shi yasa nace a tura masa kawai, idan yaso sai yayi ma uwar tasa magana tunda zai ga a account dinta aka tura kudin ai, tonan asirin bai ishe mu bane da har za mu sake yarda su dawo gidan nan" a hankali Khaleesat tace "Umma ni bana son abinda zai sake hadamu magana da shi balle har yace zai dawo da wata magana kuma" Aunty Farida tace "Ya dawo da wani magana?
Saboda ba shi da hankali zai dawo da wata maganar?
Ai yanxu ba mu da abinda zai sake hadamu da shi da ya wuce kudin nan nasa, saki uku ya aiko maki balle ace zai dawo da wata magana" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya tace "Aunty ba fa shi ya aiko da takardan sakin nan ba, ba rubutunsa bane, iya saki daya yayi min" Daga Aunty Farida har Umma kallonta suka dinga yi, a hankali tace "Shi yasa bana son a tura masa receipt din balle har hankalinsa ya dawo kan mu..." Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya tace "To Allah ya kyauta, yanxu su suka rubuto takardan suka aiko kenan?
To su dai suka sani Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu da ke baki daya, idan sun kwaso kafa sun sake dawowa sai a nuna masu receipt din" Umma dai bata ce komai ba don bata ma san me zata ce ba.
Meemah na bacci Momy ta shigo dakinta wajen karfe goma na safe ta tasheta tana mika mata wayar hannunta, Meemah ta amshi wayar tana kallon screen din, sai kuma ta kalli Momy tace "Kudin suka sako?" Momy ta tabe baki tace "Gashi kuwa kina gani, nima yanxu naga alert din ashe tun daren jiya aka sako" Meemah tace "To a gidan uban wa ta samu ta turo bayan tace bata yin transfer kuma bata da Atm card" Momy tace "Ke baki ga sunan wanda ya turo kudin ba?
Ai ba ita bace ta turo" Meemah ta kara kallon wayar da kyau taga sunan namiji, ta
e baki tayi tace "To wai ke Momy da nake ce maki iskancinta ta dinga yi da maza a Amurka kin zata wasa nake?
Ai ba abun mamaki bane don kin ga ta samu wanda ya turo miliyan goman, harkar iskancinta kawai ta dinga yi a Amurka da 'ya yan masu kudi, kuma karya take babu miliyan goman nan a account dinta wallahi, to dai gashi nan daya daga farkanta ya turo kudin nan take" Momy tace "Oho dai koma wa ya turo kudin ta matse masu can, ni dai ba na amshi kudin
a na ba, da ban yi haka ba har a tashi duniya in dai Abdul ne wallahi bazai yi maganar kudin nan ba, kin ga da shikenan sun ci bulus, to ni da na haifesa ba asararriya bace da zan yarda ya bar masu makudan kudaden nan" Meemah tace "Wallahi Momy ni so nayi mu ce sai sun biya kudin sponsoring dinta da Abdul yayi, ke kinsan nawa Abdul ya kashe akan yarinyar nan kuwa?
Wallahi idan na fara maki lissafi sai kin rike baki don mamaki, kudade ne ba na wasa ba da, duk kanta dukiyarsa ya dinga tafiya kamar kin masa baki, yaushe rabon kiji Abdul ya siya wani asset nasa ya ajiye?
Tun da ya hadu da tsinanniyar yarinyar nan ya dena yi ma kansa komai sai dai yayi mata, ranan a gabana ya siya mata Abaya har biyu ko wanne dubu dari da hamsin, nayi masa magana ya nemi ya min rashin kunya cikin jama'a, handbag din nan shegiya sai Abdul ya siya mata na dubu kusan dari har fin haka, komai designer yake siya mata, suturu kam yayi mata ba iyaka, to wai ko monthly allowance da yake tura mata a kasar Amurka in kika ji sai hankalin ki ya tashi, uwa uba a zo kan kudin makarantar ta da House rent" Momy tayi mitsi mitsi da ido cikin bacin rai tace "Don Allah ki bar wannan maganar don raina baci yake Meemah, su je kawai Allah ya isa, ni da nake uwarsa ma sai ya ga dama yake siya min abu, to yanxu ko ce masu muka yi su biya a ina suka ga kudin biya Meemah?
Ko gidan da suke ciki suka ce za su siyar wallahi karkari yayi dubu dari biyar, kai ni dubu dari biyar din ma bazan siya wannan kangon ba wallahi, kin ga kuwa gwara a bar zancen kawai, baki ji yanda raina ya baci ba wallahi, kawai Allah ya isa zan ta ja masu a kan uban kudin da Abdul ya kashe ma yarinyar kuma ba wai don bani da kudin maka su kotu ba...." Meemah tace "Ko kuma mu je duk mu kwaso kayan da ya dinga siya mata da jakunkuna masu tsada" Momy tace "Ki ci uwar me da su?
Kema dai wallahi, shekara 38 ban san yaushe zaki yi hankali ba Meemah, Allah ya isan dai shi ne dai dai su, don babu abinda za mu ci da kayanta, tunda muka samu miliyan goman ma ai mun gode Allah" Meemah ta tabe baki ta koma ta kwanta tace "Kuma kin san wani abu Momy, da Abdul yana kasar nan har yanxu zai fa iya waiwayanta idan asirin ya sakesa, don wallahi masifaffen so yake ma shegiyar ke har yanxu baki gane ba, ji fa kafin su bar kasar yanda ko magana baya yi ma mutane a gidan nan, kullum zaka gansa babu walwala" Momy ta hade rai tace "Ni kuma ga er iska sai in sakankance har asiri ya sakesa ko?