← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 191

Sashe 189

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wajen karfe tara Jay ya bude kofar dakin Ajay, yana tsaye bakin kofar yake kallonsa ganin yana kulle tsadadden traveling box dinsa, Jay yace "What is the meaning of that?" Without looking at him Ajay yace "I am leaving for Abuja" Da mamaki Jay yace "Abuja?

But you are not well Ajay" Ajay yace "I am" Jay yayi shiru still looking at him, after some seconds yace "Amma baka gaya ma Mai martaba ba tukun" Ajay yace "Na gaya masa" Jay yace "To ka bari zuwa gobe sai mu tafi tare mana" Ajay yace "Yau zan tafi" Jay yace "Amma bai fi kayi kwana biyu ba ai" Ajay yace "I can't say" duk da kwana biyun ma Mai martaba yace yayi ya dawo tunda baya jin dadi, Juyawa Jay yayi ya bar bakin kofar ya tafi can
angaren Maminsa, Mami ta ajiye wayar da take bayan ya shigo tace "Kayi breakfast Jawwad?" Ya zauna saman kujera yace "Nayi" Mami ta
an yi shiru, sai kuma tace "Ya jikin
an uwan naka, ka shiga wajen nasa kuwa?" Jay yace "Daga can nake" Mami ta dinga kallonsa ta ji ko zai ce komai cause he look moody, har ta fara zargin ko Ajay ya gaya masa maganganun da taje ta masa daxu ne, Jay yayi breaking silence din yace "Abuja ma zai wuce yau" Mami tace "Wajen Amina?" Jay yace "Eh" Mami ta ta
e baki tace "Gwara ai yaje ya huta a can din" Jay ya kalleta yace "Duka kwanansa nawa a nan da zai je Abuja ya huta?

Nan da Abuja ina ne asalin inda ya kamata ace ya samu hutu?

The occupants of this palace ain't being fair to him, they are just making the palace miserable for him to leave in, gida da mutum yake saka ran dawowa ya samu rest of mind and peace but in Ajay's case it is totally different, he is always sad and restless in his father's palace, walwalarsa iya America ne ko kuma wani state a nan Nigeria aside Bauchi, sau da yawa in ya dawo Nigeria sai Mai martaba ya dinga takurasa ya zo garin nan, till when za a bar shi ya zauna peacefully a gidan nan ya samu kwanciyar hankali?

Shi ba shiga harkar kowa yake ba he is always on his own baya shiga sabgar da bata shafesa ba, sai ya ga dama zai tanka abu, step Siblings dinsa gaba daya an dora su kan hanyar maida sa bare a masarautan nan, what is his offense pls?

Menene yayi triggering attitude din da ake ganin yake showcasing a gidan nan?" Mami dake ta kallonsa ta kwantar da murya tace "Ya ce maka an masa wani abu ne yanxu?" Jay ya mike yace "Sai yace Mami?

Nafi kowa saninsa idan da abinda yake damunsa ko kuma yana cikin bakin ciki, Kullum ya dawo gidan nan ba shi da walwala, ba shi da farin ciki, nan din kamar ba comfort zone dinsa ba, banda Mai martaba dake son ganinsa a kusa ni na tabbatar Ajay bazai dinga shigowa garin nan ba balle ya zauna gidan nan" Mami ta ta
e baki tace "In zaka bar wahal da kanka ka bari Jawwad, yanda kaga halin sa din nan haka mahaifiyarsa take ba wai, ci kanka sai ta ga dama zata ce ma mutum a sanda take raye, bata fiye son shiga harkar abinda bai shafeta ba ita ma, she is always on her own, miskila ce ta ajin karshe, in ba saninta mutum yayi ba sai yayi zaton tana da damuwa ne amma tsabar miskilanci da nukurci ne, don haka ka bar Ajay gado yayi ba taka haye ba, Mai martaba kansa ai yana da miskilancin da izza, shi abun ne yayi masa yawa wai shege da hauka, in zaka yi harkar rayuwarka ka bar damun kanka akan Junaid da zai fi maka alkhairi, sannan ni da kake kawo ma korafi zama nake a gidan nan?

Ba sai inyi wata ba a gan ni ba, na hanaka shiga sabgar da bata shafe ka ba amma baka ji Jawwad" Jay dai kallon Mami kawai yake, Mami tace "Allah dai ya kyauta kawai, shi ma in zai zauna ya saki ransa ya zauna lafiya da kowa ya bi su a yanda suke so da zai fi masa" Jay yace "Zan shirya za mu tafi Abujan tare yau...." Mami ta hade rai tace "Kanwar uwarka ko ta ubanka ce a Abujan Jawwad, ka kawo min magana mai muhimmanci ina jiran ka ka shigo mu iddasa magana kuma kace min zaka bi sa ku je Abuja?" Jay yayi shiru jin abinda Mami tace, after some seconds ya zauna a hankali yace "Yeah haka ne Mami, amma ai za mu iya gama maganar yau sai mu tafi, bai wuce yayi kwana biyu ba kawai" Mami tace "Kai ka sani, tun da ga Boss dinka zai tafi Abuja ai dole hankalinka ya tashi kace zaka masa rakiya" Shi dai Jay bai sake cewa komai ba, bayan wani
an lokaci Mami ta kwantar da murya tace "Amma Jawwad baka ganin maganar can da ka kawo min daxu da safe zai kawo tangarda a zumunci tunda kasan wacece Hadiyah a gidan nan?" Jay yace "Ai Mami ni ban yi deciding kwata kwata bazan aureta ba, na dai ce idan hakan zai zo da matsala ni na amince zan iya hadasu su biyu" Mami tace "Haka ne, a nan ma kayi tunani me kyau, kuma ana ta jiran ku dawo ne a tsaida rana fa, don a yanda aka tsara wannan lahadin ake son tsaida ranan in sha Allah, sai gashi ka dawo da wata magana kuma" Jay yayi shiru jin abinda Mami tace, a hankali yace "Mami in dai kun amince min don Allah a ha
a duk biyun a saka gaba daya" Mami ta
an yi murmushi, sai kuma tace "Ai kuma dole a
aga saka ranan Jawwad, don kaga wannan maganar da ka kawo dole sai an yi calling family meeting kowa yasan abinda ake ciki, yanxu ya sunan ita yarinyar?" Jay ya kalli Mami, sai kuma yace "Sunanta Jiddah" Mami tace "Ikon Allah, ba ka yi ma
an uwanka
ara ba kenan dai, haka kake kiran nata?" Jay ya
an yi murmushi yace "A'a, Halysaah ake kiranta" Mami tace "Maa sha Allah, Allah Ubangiji yayi zabi mafi alkhairi" Yace "Ameen" Mami tace "To ba damuwa, zan fara samun Mai martaba da maganar sai mu ga yaya za ayi kafin ma a kira meeting din" Jay yace "To Mami" Mikewa yayi don hankalinsa na can wajen Ajay duk da bai san Flight din karfe nawa zai bi ba, in ma na yanxu ne yasan dai bazai tafi bai kirasa ba, Mami tace "Fita zaka yi ne" Jay yace "A'a ba da nisa zan je ba" Mami tace "Toh kira min Maman Hadiyah ta wayar ka naji an min warning ina waya kafin ka shigo" Jay na kallonta yace "Maganar zaki mata Mami?" Mami tace "Haba, sai kace wata yarinya, maganar mu daban, in ma maganar ne ai yayanta ne zai mata" Jay ya ciro wayarsa ya mika ma Mami, ta amsa tace "In ji dai babu password, naga ka miko min haka" Yace "Babu" Tace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga parlon, Mami ta shiga call logs dinsa, Miss call ta gani da number da yayi saving with Halysaah with love emoji a gefe, ko picking call din ma bai yi ba kuma tun karfe takwas ta kirasa, wayarta ta jawo ta kwashe number gaba daya ta adanasa a wayarta, sannan ta fita daga call log din, gallery dinsa ta shiga nan ta ci karo da recent pictures da suka yi da Halysaah a amurka wanda Safiyyah tayi masu, kallon hoton ta dinga yi babu ko kiftawa with shock, tayi zooming din Halysaah sosai tana kare mata kallo, ajiye wayar tayi tsabar yanda ta girgiza taji zuciyarta na bugawa, ita Jawwad zai jajibo ma wannan yarinya me kama da buzuwa ko halfcast, mutanen da aka san su da mugun mallake miji, sannan ko me miji ya mallaka to a kansu yake karewa su kadai ke mora don raba mijin suke da danginsa kaf, sosai hankalin Mami ya tashi ba kadan ba, ta dinga kallon duk hotunan, da irin kallon tsantsan kauna da Jay yake ma Halysaah a duk hotunan kamar zai cinyeta, Mami ta ajiye wayar ta dafe kanta da yayi mata nauyi ta dinga nanata Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, rabon da ta shiga irin wannan tashin hankalin da kidimewa har ta manta, wayarta ta jawo ta shiga WhatsApp dinsa tayi ma kanta sending hotunan guda biyu sannan tayi deleting yanda shi bazai gani ba ko yasan abinda tayi, daga nan ta fita daga WhatsApp din ta goge duk wata alamar da zai nuna wajajen da ta shiga a wayar nasa gaba daya, ta fi minti biyar a kidime sannan tayi dialing number Maman Hadiyah ta wayar sa don kar yaga bata kira ba, minti uku kawai suka yi suna magana da Maman Hadiyah sannan ta ajiye wayar tasa ta dau nata ta fita ta nufi bangaren Aunty cikin tashin hankali.
Chapter 189 · 0% Book details