← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 191

Sashe 151

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk sai kice he is just being kind ko?" Khaleesat ta wani kalleta, Safiyyah na dariya tace "Ae ba abun mamaki bane kice baki gane yana sonki ba har yanxu, amma wallahi Housemate dinki na bala'i son ki kawata, don wannan care din is extra ordinary, ko kanwarsa da suka fito ciki daya bazai dinga yi mata irin wannan hidimar da yake maki ba, kai budurwar da saurayinta zai mata haka ma ba karamin musulmin sonta yake ba, yan mata nawa ne yanxu ko Naira biyar baya hadasu da samarinsu kuma a haka wai aurensu za ayi, ke dai wallahi you are very lucky om earth, Allah ya kashe ya baki kawai, ni kuma zan baki shawara kar kiyi misusing privilege din nan, cause it's a privilege to you wallahi, bai duba wai kin ta
a aure ba kawai shi tsakani da Allah yake son ki a zuciyarsa, come to think of who he is, daga gidan sarauta fa ya fito, in zaki ajiye kunya ki nuna masa kema kina sonsa to zai dai fi maki, you are not a kid Khaleesat, kinsan sonki Jawwad yake, so me tsanani kuwa" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Kinsan me Sophie?" Safiyyah na kallonta tana washe baki tace "Ina jin ki" After some seconds Khaleesat tace "Abdul came to my apartment yesterday night" Mikewa Safiyyah tayi ba tare da tasan ta yi hakan ba a tsorace, tana kallon Khaleesat with shock all over her face tace "Waye kuma Abdul?

Did you have another frnd that is Abdul by name da ban sani ba?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta, cikin sanyin murya tace "Abdul dai guda da kika sani" Safiyyah tace "Na shiga uku na lalace, Abdul tsohon mijin ki wai kike nufi?" Khaleesat ta kasa ce mata komai, Safiyyah ta koma ta zauna tana kallonta da wani expression tace "Ta yaya yasan apartment din ki Khaleesat?

Kuma me yaje yi maki a apartment?

Don Allah ki min bayani yanda zan gane, i am lost...." Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Wallahi ban san ta yaya yasan apartment dina ba Sophie, ni kaina i am still shock up till now, ko breakfast na kasa yi saboda tsoro, yanda kika san an jefo sa" Safiyyah ta maida jakarta gefe tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ji min shege
an iska, to wai uban me yaje maki a apartment din, tell me what happen da yaje, ke kuma da yaje kofa kika bude masa ya shigo?" Khaleesat tace "Bayan Housemate dina yayi dropping dina a gida ya tafi ana ruwa, after like 10 mins sai aka danna bell, to na mance jakana a motar Housemate i was thinking shi ne ya dawo ya kawo min jakar, da na sauka downstairs sai na bude kofa kawai, ashe Abdul ne" Safiyyah da tayi mitsi mitsi da ido tana sauraron Khaleesat tace "Go on, ina jin ki, sai aka yi yaya?" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "I was very shock and afraid bayan na bude kofan ya shigo, shi ne na shiga kitchen da gudu dama wayata na hannuna nayi dialing number Ya Junaid, sai gashi ya biyoni kitchen din ya karbe wayar" Buda baki Safiyyah tayi tana kallonta da firgici a fuskarta, cikin sanyin murya Khaleesat ta gaya mata duk abubuwan da Abdul yace mata a kitchen din bayan da ya sameta a ciki, da kuma yanda Ajay ya zo gidan duk bata boye mata komai ba....

Safiyyah na girgiza kai tace "Amma kin bani mamaki Khaleesat, yanxu shi Abdul har wani abun tausayi ne shi da zaki boyesa a apartment dinki?

Abdul fa???" A hankali Khaleesat tace "Ce min fa yayi in tuna alkhairansa gare ni Sophie, kuma he look afraid also baya son Ajay ya gansa, shi ne yace in rufa masa asiri" A fusace Safiyyah tace "Wani shegen alkhairin yayi maki da zaki tuna?

Harrassing dinki da ya dinga yi ko kuma gorin da yake lafta maki da walakanta ki da yake yi?

Nan nan ranan kika bani labarin zaman ukuban da kika yi a gidansa kafin ya sake ki, da yanda ya bar ki da kwalin indomie ko albasa babu balle tarugu, marukan da ya dinga maki da zagin cin mutunci ne alkhairin da zaki tuna game da shi?

Mutumin da ya ci mutuncinki ya sake ki bayan ya samu abinda yake so a wajenki har shi ne abun tausayi Khaleesat?

Yanxu kina nufin kika boye Abdul har washegari a apartment din ki kika bar Ajay da gadin ku?

Ikon Allah, Gaskiya baki ta
a bani tsoro irin yau ba Khaleesat, i fear who no fear you, me yake damun ki ne haka?" Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi tana kallon Safiyyah tace "Safiyyah kar ki manta this is America, we are not in Nigeria, Ya Junaid na lura temper dinsa a kusa yake, yana da zuciya sosai, what if yaje ya masa wani illa wajen dukansa don nasan definitely bazai kyalesa ba idan ya gansa a gidan, kina tunanin idan yayi masa wani abu za a kyalesa ne a kasar nan? dole doka zai yi aiki a kansa, kuma duk saboda ni sai haka ya faru Sophie??" Safiyyah ta wani kalleta tace "Sannu me hangen nesa, da duk baki san da hakan ba kika doka masa kira?

Why did you call him at the first place idan ba don ya zo ya fitar maki da Abdul ba?" Hawaye ya cika idon Khaleesat tace "Ai a sannan ban san da wani Intention ya zo min gida ba, kinga if he just came to harm me wannan daban ne, amma he meant no harm he was even afraid, banda haka ai bazai rokeni kar in gaya masu ya zo gidan ba" Safiyyah tayi wani murmushi tace "Maa sha Allah, kinga shawara daya kawai Abdul ya koma Nigeria ya bada sabon sadaki a kara daura maku aure kije can ku karata, tunda yanxu kam ya tuba kuma har kin yarda da tubansa kina mugun tausayinsa a rai, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a masu yawa" Khaleesat ta hade rai tace "Come off it Safiyyah, ni nace maki i am ready to accept his repentance?

Ko sake daura min aure aka yi da shi ba sai dai a kai gawata gidan ba, how will I forget what i went through so soon Safiyyah, wallahi kawai kalman alkhairi da ya furta ne da kuma irin sigar da naga ya zo min yasa na rufa masa asiri, ni ba butulu bace bazan ce Abdul bai min abubuwan Alkhairi ba a rayuwata, in ba don shi ba yaushe har ma zan zo kasar nan in hadu da su Housemate dina?

I lacked nothing tun da Abdul ya kawo ni kasar nan karatu, don har nafi wasu da iyayen nasu ke daukar nauyinsu, kinga bazan ce Abdul bai min wani abun alkhairi ba, kuma bazan ta
a iya biyansa abinda yayi min ba, ki fahimce ni plss Sophie, ba wai nace ya kamata in sake kulasa bane, don wallahi ko ganinsa bana son yi don hakan na fama min ciwon dake zuciyata..." Safiyyah ta tabe baki tace "Tun da kin rufa masa asiri kin ga yau ma nasan yana can bakin apartment din naki yana jiran ki, hauka ake zan rufa ma Abdul asiri idan ni ne a shoe din ki?

Abdul fa?

Ai ko duk alkhairan duniya yayi min wallahi bazan rufa masa asiri ba sai dai Allah ya yafe min kawai, Monster in form of human ne fa Abdul, gaskiya kin ci amanar Junaid, kin cuce sa, kuma da ya kuskura yasan abinda kike boyewa a gidan nasan ko ciki daya ku ka fito da shi bazai sake barin wata ala
a ta hada ku ba har abada, kuma bazai ta
a yafe maki ba, in kina tsoron kar Ajay ya masa illa me ya hanaki kiran 911?" Khaleesat dai tayi shiru tana bin inda suke zaune da ido, Kawai ganinsa suka yi a gabansu, ta rike numfashi tsabar yanda tayi shock tana kallonsa babu ko kiftawa, Safiyyah da ita ma ta gwalo ido tana kallonsa da mugun mamaki ta mike tana huci tace "Kai bawan Allah lafiya muna zaune zaka tsaya mana a kai, ko dai batan hanya kayi ne?" Sau daya ya kalli Safiyyah sannan ya mika ma Khaleesat wayoyin dake hannunsa guda biyu yana kallonta, daya na Jay daya na Ajay, Khaleesat ta wani hade rai tace "Abdul kaga bana son muyi creating scene a nan, kindly stay away from me, are you even okay?

Meye zaka dinga bibiyata?" Safiyyah ta figi jakarta tana kokarin ciro wayarta tace "Idan ban kira maka 911 ba Allah ya tsine min albarka...." Tana ciro wayar ya fixge daga hannunta yana kallonta da kyau yace "Wajen ki na zo da zaki kira min 911 Malama?" Safiyyah ta kundumo wani zagi tana kallon Khaleesat tace "Kin dai ga crook din da kika ji tausayi har kika boye a apartment din ki kar Ajay ya gansa ya jibgesa ko, kin ta
a ganin inda shedan ya tuba dama?

Shey u can see the useless monster you are pitying har da boyesa kar a dokesa?" Abdul na mata wani kallo yace "Hey watch your tongue, idan ba haka ba i will teach you a bitter lesson Billah, Ajay kika kirasa ko?
Chapter 151 · 0% Book details