← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 191

Sashe 64

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na'am bane kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka?

In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya?

Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane" Wata matashiya ce er shekara 39 dake zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace "Momy ban gane abinda kike nufi ba?

Wai nufinki ya saketa kenan?" A fusace Momyn tace "Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema?

Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?" Warce ta kira da Meema ta girgiza kai tace "A'a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy?

Ae wallahi bata isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci da tijara haka?" Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace "In har aka ga na saketa to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan ne zata gwammaci bata ta
a sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her" Momy ta tabe baki tace "Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar yarinyar nan" Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace "Ai ki ma dena maganar asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji" Momy dai ta tabe baki tana kallon me aikinta tace "Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min naman yatsu" Hakuri mai aikin ta hau bata.

Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta
an kishingida a 3 seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya ta
a biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta kalli Khaleesat tace "Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?" Khaleesat ta girgiza mata kai, dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace "Tare da brother dina muke" Aunty Farida tace "To ku shigo mana" a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara'a, sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace "Are you feeling better now Housemate?" Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace "Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha Allah, i promise you" Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl din hannunta Softly yace "Take ur soup" Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali, Aunty Farida ta kalli Ajay tace "Baka zauna ba Junaid" Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna, Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace "Mu ma duk ba da son ran mu bane abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za su dau er su su ba Abdul aure"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Alhamdulillah!

Shin kunada labarin MG
s Beauty Lounge zai bu
e a ranar Litinin, 2nd June 2025
daidai lokacin Sallah!

Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
s Beauty Lounge ya bu
e da kwalliya, tsafta da
amshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai
aukar ido
Wanke
afafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-turai, humra, incense da
amshi masu da
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba
kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.

Zo ki ji da
in wanke
afa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da
amshi
komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki
ki ji da
in sauyin MG
s Beauty Lounge.

Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
HALYSAAH 32
Sai da Jay yaga Khaleesat ta ci pepper soup din me
an yawa sannan ya mike ya koma kusa da Ajay ya zauna, After a while Ajay yayi breaking din silence din da ya ziyarci parlon yace "Iya daukar nauyin karatun ta kawai yayi Aunty?" Aunty Farida zata yi magana wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin Umma ce ke kiranta ta wayar makociyarsu Sha'awa, ta mike ta tafi dakinta don daga wayar, Ajay dai kallon Khaleesat yake kamar yanda Jay ke kallonta don har ta shanye pepper soup din, ta ajiye bowl din kasa tana kokarin disconnecting drip din hannunta ta yanda zata bar cannula din kawai, Jay ya mike yana kallonta yace "What happened?

Do u want to ease ur self" Da kyar tana girgiza masa kai tace "I think i want throw up" Ya karasa cikin hanzari yayi disconnecting din mata, ta tashi ta wuce bandakin Aunty Farida da sauri tana toshe bakinta, sai ga Aunty Farida ta fito daga daki, ta kalli inda Khaleesat ke zaune ganin bata nan ta kalli kofar bandaki, zaunawa kan kujera tayi a sanyaye tana kallonsu tayi kasa da murya tace "Yanzu yayata ta kirani wai an zo an tafi da mahaifin Khaleesat" Da mamaki Jay da Ajay ke kallonta, Ajay yace "Kamar yaya kenan?" A sanyaye Aunty Farida tace "Baban Abdul din ne yasa aka je aka tafi da shi" Daga Ajay har Jay kallonta suke with confusion da kuma mamaki, fitowar Khaleesat daga bandaki ya sa Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, bayan Khaleesat ta kwanta kan 3 sitter din Aunty Farida ta juya tana kallonta tace "Ko zaki shiga daki a maida maki drip din?" Khaleesat ta gyada mata kai don ita ma ta gaji da kwanciyar kujeran, Aunty Farida ta mike tace "Bari in ma makociyata magana sai ta sa maki a daki" Daga haka ta fita daga parlon, after some minutes sai ga ta ta dawo da Neighbor dinta Bayerabiya, Khaleesat ta tashi ta koma dakin Aunty Farida, Bayerabiyar ta bi ta ciki ta sa mata drip din, ita dai Aunty Farida na zaune parlor tayi nisa tunanin da take har makociyarta ta fito ta tafi, Aunty Farida ta kalli su Ajay a hankali tace "To abinda yayata ta kirani ta gaya min kenan" Ajay yace "So suke a biya su kudin makarantar da ya dinga biya mata?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai ba iya kudin makaranta bane Junaid" Ajay yayi shiru yana kallonta, Jay yace "Bayan makaranta akwai wani abu na kudi da ya hadasu ne?" Aunty Farida tace "Kwarai kuwa....
Chapter 64 · 0% Book details