← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 191

Sashe 3

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari har karfe sha daya Khaleesat na dakinta bata fito ba duk da yunwan da take ji, tayi tagumi don gaba daya ta ma rasa what is her problem particularly, ta dau wayarta jin shigowar WhatsApp message, tun daxu suke chatting ta VN da Ummanta ta wayar makociyarsu Sha'awa, da taji shiru ta ma zata an maida ma Aunty Sha'awa wayar nata ne, ta bude VN din tana sauraren voice din mahaifiyarta, Addu'a Ummanta ke mata tana mata fatan nasara a karatun ta, sannan kamar ko da yaushe ta sake jaddada mata ta kula da mutuncinta ta kula da kanta, daga karshe ta
are da cewa za a kai ma sha'awa wayarta don zata fita kasuwa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar a hankali sannan ta mike ta dau hijab din sallanta ta saka ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita daga dakin don ta gaji da horan kanta da yunwa ita da ke breakfast da wuri, kitchen ta tafi almost bumping into her new House mate shi kuma yana kokarin fitowa daga cikin kitchen din, komawa baya yayi at the same time yace "Good morning" Bata yarda su hada ido ba ta matsa gefe allowing him to pass, ya fito daga kitchen din yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan ta shiga ciki, tsaye tayi tana kallon littered cups da plates din da yayi amfani da su ya bari a sink din wanke wanke without washing them, ga bowl din fruit salad da shi ma ya ajiye bai sha ba, bin kofar kitchen din tayi da kallon mamaki, to wa ya bari yayi masa wanke wanke?

Ta fi minti daya tsaye a inda take da tunani iri iri a ranta, wata zuciyar ta ce mata kawai tayi abinda ya kawota ta fita daga kitchen din ta bar unclean utensils din a yanda ya bar su, amma dai kawai ta jawo liquid wash da sponge fuskarta a daure ta fara wanke kayan wanke wanken kawai, bayan ta gama ta goggoge kitchen din ta hada shayi ta debi cookies a plate sannan ta fita daga kitchen din ta wuce dakinta.

Wajen karfe uku Khaleesat ta fito daga dakinta, tun da ta gama breakfast take karatu sai sallah kawai ta tashi tayi da azahar, jin ko ina shiru and to be sure baya gidan ta nufi kofar parlon zata bude taji an kulle da makulli, dakinta ta koma ta dauko makullinta ta bude kofar tana duba garage taga babu motarsa a ciki, komawa cikin gidan tayi ta kulle kofar sannan ta tafi kitchen, tun shekaranjiya take son cin shinkafa da miya amma kasancewar she is not comfortable tun da ya dawo gidan yasa ta hakura da girkawa, yanzu da taga baya nan kawai tayi deciding tayi shinkafa da miyar, bayan ta daura shinkafar, ta fara hada miyar dama tana da sauran chicken thighs a fridge, fitowa parlor tayi da sweeper zata yi shara, ta ajiye sweeper din hannunta to tidy the couch first, dukawa tayi tana kallon takardun Housemate din nata da ta gani, sai kuma ta kyabe baki ta bar su nan yanda ya bari a kan kujeran, share rug din parlon ta fara yi bayan ta dauke makullin da ta gani a kasa, ta dinga juya makullin ganin kamar na Bedroom ne, kafin minti arba'in ta gama girkin da take ta tsaftace ko ina na gidan, ta debi abincinta ta tafi daki da shi, sai da ta fara yin sallahn Asr sannan ta dau wayarta tana dubawa, sosai gabanta ya fadi ganin miss call din Abdul, nan da nan taji abincin ya fita ranta gaba daya, ta zauna gefen gado a hankali tana kallon wayar, ta fi minti goma zaune a haka, she was soo worried, to yanzu me zata ce masa ma in ta kirasa, daga karshe ta daure tayi dialing number nasa, har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, duk da yunwan da take ji haka nan taji abincin ya fita ranta, ta tsani duk wani abu da zai sa Abdul ya daga mata hankali, haka tayi forcing din kanta ta ci abincin sannan ta kwanta side din gado, bata san sanda bacci ya dauketa ba a haka.... knocking kofar dakinta da ake yi ne ya farkar da ita daga baccin da take, ta mike zaune da kyar tana murza idonta tana kallon kofar at the same time tana mamakin me zai sa ya dinga bubbuga mata kofa haka, to ko dai bashi da kai ne?? ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe shidda da mintuna, bata yi tunanin ta dade tana bacci haka ba, sake knocking da aka yi yasa ta mike tsaye ta saka hijab fuska daure tace "What is that??" Ta ji yace "Ohk i think i misplaced my keys, just want to know if you saw it while tidying up the parlor?" Sai a sannan ta tuna makullin da ta gani a parlor daxu da take shara, tana tafiya a hankali ta karasa kofar dakinta ta murda key din jiki sannan ta bude door din, tuni har ya bar corridor din ya koma parlor ya tsaya yana jiranta, da alama dawowarsa gidan kenan a lkcn, ta karaso cikin parlon ba tare da ta kallesa ba, shi dai duba message din da ya shigo wayarsa yake with all his attention, ta tafi inda ta ajiye makullin sannan ta dawo ta ajiye masa kan takardunsa dake kan kujera tace "Here" Yace "Ohk" dakinta ta koma ta shiga tana mamakin wai Ohk, ba ma thank you ba kamar irin ya ajiyeta din nan, kwafa tayi ta saka ma kofarta key, bayan Khaleesat ta idar da isha ta sake kiran Abdul bai daga ba, sau hudu kenan tana kiransa tun karfe bakwai bai yi responding ba, yanzu dai tafi tunanin yana bacci don dare ne sosai a can kasar, even at that tasan she is in soup, mikewa tayi ta dau plate din da ta ci abinci daxu ta nufi kofa ta fita daga dakin, a parlor ta ga sabon Housemate dinta yana tattara takardunsa at the same time yana answering phone call taji yana cewa "I am on my way now" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa ya dau takardunsa da makullin mota ya mike tsaye, ido hudu suka yi for the first time tunda ya dawo gidan, ita dai ta dauke kai kamar bata ma gansa ba ta karaso cikin parlon zata tafi kitchen taji yace "I ate a little out of the food you cook, and...." Yayi pointing takeaway din da ke kan kujera yace "I am taking some to my frnd too" duk wannan abun bai kalli inda take tsaye ba yake magana, sai ita ce ma da ta dinga kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, ya dau takeaway din ya nufi kofa cikin hanzari, yace "Good night" Ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle gidan da makulli ta waje, mamaki yasa ta kasa karasawa kitchen din, after some seconds ta tafi kitchen din, da plate din da ya ci abincin, da cup din da ya sha coffee, da bowl din da ya sha fruits salad duk suna ajiye a sink babu wanki, ta jingina da kofar kitchen din ta rungume hannu tana kallon sink din kamar zata fashe don bakin ciki, can ta karasa ciki tana duba shinkafar da ya bar mata, taga da kyar in zai yi spoon uku, gashi duk yayi littering din wajen da shinkafar wajen diba kuma ya bar shi haka, haka nan ta juye er shinkafar da ya rage a karamin bowl, ta wanke duk utensils din, ta gyara ko ina ta goge sannan ta hada shayi ta koma daki da bowl din sauran abincin, zaunawa tayi gefen gado ta dau wayarta tayi dialing number Safiyyah, sai da ya kusa katsewa Safiyyah tayi picking daga daya bangaren tace "Allah da gaske baki da kirki Khaleesah, to ko baki kira ba dai na isa Virginia cikin koshin lafiya" Khaleesat ta
an yi murmushi tace "Dama nasan kin isa lafiya ai, hope you are doing good?" Safiyyah ta tabe baki tace "Oho dai, wannan ba matsalar ki bane" Khaleesat tace "Amma don Allah ina kika ce ma Ya Musty za ki?" Safiyyah tace "Ahaf tsaya wasa, sai kace baki san ni ba, munafukar matarsa da yake ba son zamana a gidan take ba ita ce ma ta kara convincing dinsa, duk zatonsu ina gidanki muna group reading with some of our Coursemate" Khaleesat tayi murmushi tace "To ai shikenan, yanxu yaushe zaki dawo?" Safiyyah tace "Gobe ne birthday din ai, in sha Allah i will be back on Monday" Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu, kinsan mene?" Safiyyah tace "Aa" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi in gaya maki Abdallah ne ya kirani nayi missing call dinsa as i am speaking to you now tun daxu nake kiransa yaki picking, nasan fushi yayi sosai, ni kuma...." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ke kuma me?

Shikenan rayuwa babu uxuri dama?" Khaleesat tayi kasa da murya tace "He warned me times without number kar in sake missing call dinsa Safiyyah, kuma wallahi ina kitchen sanda ya kira wayar kuma na daki ba da gangan nayi missing kiransa ba" Sounding so pissed off Safiyyah tace "Wai don Allah me yasa kika dauki tsoron duniya kika dora ma mutumin nan ne Khaleesat?

For how long will things continue this way?

Yaushe za ki fara nuna masa ke fa mace ce? yanzu haka za ku yi auren ya maida ki slave a gidansa tunda kin nuna masa kina mugun tsoronsa tun a waje? wannan wani irin gantalallen relationship ne?

Gaskiya ina jinjina maki Khaleesat, don wallahi in nice bazan iya ba Allah ma ya gani sai dai duk abinda zai faru ya faru" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I have no choice nor option Safiyyah...." Tana fadin haka hawaye ya fara gangarowa idonta, a
an fusace Safiyyah tace "To wai ke kadai ce mace a gidanku ne da ya gani?
Chapter 3 · 0% Book details