← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 191

Sashe 6

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washegari da safe Khaleesat na kitchen tana ma kanta snacks da zata kai school don har yamma suke da Lecture gashi suna da er jarabawan da za su yi ranan da safen, Housemate dinta ne ya shigo parlon, tun jiya da daddare da ya fita sai a sannan ya dawo gidan, har zai tafi dakinsa sai kuma ya tsaya yana kallon Handbag dinta da makulli dake ajiye gefen jakar, karasawa yayi ya dau makullin sannan ya juya ya fice daga parlon gaba daya closing the door gently ya kulle da key, Khaleesat tafi minti sha biyar tana duba makullinta bayan ta fito daga kitchen, tun daga dakinta har parlor zuwa kitchen babu inda bata duba ba amma bata ga alamar makullin ba, she can't even tell ko ta fito da shi parlor, she was so confuse gashi tayi latti, daki ta koma sai da ta birkice ko ina amma babu alamar makullin, how comes will her keys disappear just like that, tunda ta fara karatu a kasar bata ta
a misplacing makulli ba banda wani lkci da Safiyyah ta yar mata guda daya, ko gyara dakin da ta birkita bata yi ba ta dawo parlor looking so frustrated, tsaye tayi trying to calm her brain ko Allah zai sa ta tuna inda ta ajiye keys din, ta
aga kai da sauri tana kallon kofar parlon jin ana budewa, House mate dinta ne ya shigo living room din da wasu takardu a hannunsa, sai da ya kulle kofar ya zare makullinsa sannan ya karasa cikin living room din ya ajiye takardunsa kan kujera without looking at her yace "Good morning Housemate...." Bai tsaya yaji amsarta ba yayi wucewarsa daki yana cire jacket din jikinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shige daki ya kulle, zaunawa tayi gefen kujera ta dafe kanta da taji har ya fara ciwo, yanzu ina ta jefar da mukullin nan for God sake gashi lokaci na ta wucewa, after few minutes sai gashi ya sake dawowa parlon, har sannan bai yarda ya kalli direction dinta ba, taga yayi wucewarsa kitchen ya fito rike da ruwan gora ya sake komawa dakinsa ya kulle, wayarta dake jaka ne ya fara ring ta bude jakar ta ciro wayar taga Safiyyah ce, dagawa tayi ta kai kunne Safiyyah tace "Ya baki shigo schl ba har yanzu, duk latti na yau na riga ki shigowa makaranta, ko kin manta muna da test ne" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina sane Safiyyah" Safiyyah tace "Na fa ce akwai tutorial da zaki min kafin mu shiga test din" a hankali Khaleesat tace "Zan taho yanzu" Safiyyah tace "Don Allah ki taho, wallahi ba abinda na sani a course din kema kin sani" Khaleesat ta ajiye wayar bayan Safiyyah ta katse, agogon wayarta ta kafa ma ido, bayan wasu yan mintuna ta mike after gathering courage to do what her mind is telling her, walking slowly ta nufi dakinsa, tsaye tayi tana facing kofar, a hankali ta kai hannu kofar tayi knocking tana turo baki, Yana jin knocking din ya kalli kofarsa, gyada kai yayi letting out a grin, sai da ta sake knocking din sannan yace "Waye wannan?" Exactly yanda take yawan fada, Shiru tayi bata ce komai ba ta kara turo baki, ya mike ya tafi gun kofar ya bude yana kallonta daga sama har kasa da alamar mamaki, tuni ta kauda kai, still keeping a surprise face yace "Madam hope nothing??" Trying to sound a little polite tace "I need you to open the door for me" ya gyara tsayuwa yace "I don't understand, dama a hade makullinmu suke?

Where is ur key?" A takaice tace "It's fine, no long talk" Juyawa tayi zata bar wajen, yace "Ko baki ga naki bane?" Ta wani kallesa tace "Banda haka ai da ban zo nan nace ka bude min kofa ba" Yace "Ohh i see, does this mean u are careless too?" Barin wajen tayi ta koma parlor ta zauna, ya gyada kai with smile of satisfaction sannan ya koma daki ya dauko makullinsa ya fito, sai da ya shigo parlon yace "Ta yaya ma zaki yi misplacing a whole bunch of key sai kace allura, this is kind of weird" Daukar handbag dinta tayi ta nufi kofar yana budewa ta fice daga parlon tayi wucewarta without turning her back, ya gyada kai yace "Zaki dawo ai, zan ga ta inda zaki shigo gidan" Kulle kofar parlon yayi still smiling, ko ba komai ya rama abinda ta masa jiya.

Safiyyah na kallon Khaleesat tace "To ko ya shige cikin Couch ne makullin?" Khaleesat tace "Ta yaya zai shiga kujera?" Safiyyah tace "Kuma har kitchen din kin duba?" Khaleesat tace "Babu inda ban duba ba fa" Safiyyah tace "Toh kawai kiyi ma agent din gidan magana su baki wani makullin mana" Khaleesat tace "Gani nake kamar dogon process ne hakan, kuma ai biyu ne makullin kika yar min da daya shine na dauko spare key din nake using, to shima gashi ban gansa ba yanzu" Safiyyah tace "Kar ki wani damu kanki, makullin na nan zaki gansa, kawai kin mance inda kika jefar ne, amma definitely it's either in ur room ko kuma parlor, yanzu jira zaki yi sai sanda housemate dinki ya dawo ki koma gidan kenan?" Khaleesat tace "Wani housemate?

Shi da ba kwana ma yake a gidan ba, kuma ba shi da exact time da yake zuwa" Safiyyah tace "Kai haba, to a ina yake kwana?" Khaleesat ta zaro ido tace "Kin ji ki da wani tambaya, ta yaya ni kuma zan sani? what is my business with him da zan san inda yake kwana" Safiyyah tace "To kawai mu je gidanmu ki kwana" Khaleesat tace "Kina ganin babu matsala hakan?" Safiyyah tace "Wani irin matsala?

To gidanta ne ko na ubanta da za a samu matsala? ta shi mu tafi jare" Safiyyah na gaba Khaleesat na biye da ita a baya suka shigo parlor da sallama, Surayya matar cousin brother din Safiyyah dake zaune parlorn ta daga kai tana kallonsu, Safiyyah tace "Sannu da gida Mom Aslam" Surayya ta ci gaba da danna wayar hannunta tace "Yauwa" Khaleesat ta zauna kan kujera ta gaisheta, Surayya ta amsa without looking at her tana danna wayarta, Safiyyah tace "Ai kin ganeta Mom Aslam, kawata ce kuma Coursemate dita Khaleesat" Surayya tace "Ohk" Safiyyah tace "She will be passing the night here, makullinta ne ya
ata" Surayya ta daga wayarta da ya fara ring ta kai kunne hade da amsa sallama ta mike ta bar masu parlon, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Tashi mu je ciki" Mikewa Khaleesat tayi ta bi bayan Safiyyah zuwa dakinta, Safiyyah na idar da sallah ta canza kayan jikinta tana kallon Khaleesat dake zaune saman darduma tace "Bari in samar mana abinda za mu ci a kitchen" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Safiyyah ta fita daga dakin...
Chapter 6 · 0% Book details