← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 191

Sashe 178

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe shidda da yan mintuna na asuba suka sauka airport din Abuja, a cikin Airport din suka jira next flight dinsu to Kano which is 7 am flight, tun basu karaso Nigeria ba suna
asar da suka yi Transit ya sa a siya masu ticket din kan su karaso, Khaleesat dake ta kallonta ta jira har ya gama wayar da yake wanda da alama da Maminsa yake magana, yana daga kai ya kalleta a hankali tace "Gidan da Ya Junaid ya ta
a sa aka kaini a nan Abuja is she his late mother's sister?" Jay yace "Ammi?" Khaleesat ta gyada masa kai, Jay yace "No, she is his mother's Childhood frnd, since after his mother's demise she was always there for him, har hutu Mai martaba yana bari yaje yayi wajenta when he was little, a Bauchi take da mai gidanta before suka yi relocating to Abuja years back, so she is just like a mother figure to him, yana kuma bata value sosai" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi, ta tuna irin yanda Ammi ta ja ta a jiki kamar ta ta
a saninta lokacin da ta sauka gidan, ta kalli Jay a hankali tace "She is very kind" Jay yayi murmushi yace "Sure she is, Ajay doesn't joke with her matter, ko abu zai yi idan ta hanasa ya hanu, in kuma tace ga yanda zai yi to hakan zai yi, although yana son Grandma dinmu ma amma kuma ita baya jin maganar ta" Khaleesat tace "To kana da number din Inteesar din Ammin?" Jay yace "A'a bani da numberta, sai dai Ajay" Khaleesat tace "Pls ka amso min wajensa, da ace Flight dinmu zuwa Kano ba na yanzu bane da naje gidan in gaisheta" Jay yayi murmushi yace "Da nasan za ki je ai da nace ayi mana booking ticket din yamma, da sai in kai ki gidan ku gaisa" Khaleesat ta langwabar da kai tana kallonsa, yace "Ko ayi cancelling ticket din kawai?" Ta zaro ido, sai kuma tayi murmushi ta girgiza masa kai tace "A'a, ba haka nake nufi ba" Yace "To ya kike son ayi ur Royal Majesty?" Er dariya tayi tace "In ka amsar min number wajensa sai in kira Inteesar daga nan sai ta ba Ammi wayar mu gaisa" Jay yace "Ohk zan ce ya turo min number idan muka isa Kano in sha Allah" Khaleesat tace "Yana Kanon ne ko yana Bauchi?" Jay yace "Yana Bauchi, bai tsaya Kano ba" Khaleesat ta langwabe kai tace "Da ma ya auri Inteesar kawai because of her Mother, since she sees him as a son, and he takes her as a Mom, kuma Inteesar din ba ruwanta i like her so much, she will be of a good wife to him, she is so gentle, and she is beautiful" Jay yayi dariya yace "Ko?" Khaleesat tace "Allah..." Jay yace "Toh ko za ki basa shawara?" Khaleesat ta wara ido tace "Kai dai da yake brother dinka ka basa shawaran, zai samu peace of mind sosai idan ya auri Inteesar" Jay na murmushi yayi kasa da murya yace "Kamar yanda zan samu peace of mind idan na auri Halysaah?" Rufe fuskarta tayi da sauri tana murmushi, shikenan kuma yayi cutting conversation din don bata sake yarda ta ci gaba da hirar ba, he wish she will continue don yana jin dadin conversing da ita barin idan ta saki jiki, har wani natsuwa yake ji a ransa, don dai ta ci gaba da magana yace "Yanxu dai baza ki bi kawar ki ku zo masarautar mu ba?" Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace "Are you taking Sophie serious?" Jay yace "To ai ita da gaske take, she was so serious saying it" Khaleesat tace "Uhm, nasan ma baza a bari taje bikin da take cewa a Gombe ba balle har taje Bauchi, her father is very strict" Jay yace "Amma gaya min gaskiya, kuna da yan uwa a Bauchi kamar yanda tace?" Khaleesat ta
aga manyan idanuwanta ta kallesa, murmushi tayi ta girgiza masa kai alamar a'a, yace "Ban yarda ba, tunda har Safiyyah ta fada haka ne, so why are you hiding it?" Khaleesat tayi shiru, after some seconds tace "Stepsister din Dad dina ce a can amma a kauye suke, Nenne ce ta rike ta don tun tana karama Baabarta ta rasu" Jay yace "Ina kenan a Bauchi?" Khaleesat tace "Nima ban sani ba wallahi" Yace "Baki ta
a zuwa ba kenan?" Khaleesat tace "Ban ta
a zuwa ba, amma Aunty Farida da su Ummanmu suna zuwa idan ya kama, step mothers dina ma duk suna zuwa" Jay yace "Amma ita ta Bauchin bata zuwa Kano?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Tana da yarinya with Cerebral palsy, and she is almost 14 years, saboda yarinyar yasa bata zuwa ko ina tunda bazata iya tafiya da ita ba saboda condition dinta, kuma ba me kular mata da ita kamar yanda ita zata yi" Jay yace "Allah Sarki, Allah ya basu ikon cin jarabawa" Khaleesat tace "Ameen" Bayan few more minutes suka yi boarding jirgin da zai yi take off zuwa garin Kano wanda shi ne jirgin farko da zai tashi zuwa Kano a ranan, duk da farin cikin da Khaleesat take zata je gida taga Ummanta da Aunty Farida da Siblings dinta har ma da Babanta, amma deep down her she is so afraid don bata kuma san me zata tarar wannan karan ba ko kuma me zai faru zuwanta kano, da ta tuna tashin hankalin da ta tarar zuwanta na karshe tare da Ajay sai taji faduwan gabanta na tsananta, bayan jirgin ya tashi Jay dake lura da ita don kusa suka zauna yace "Halysaah" Juyawa tayi ta kallesa, yayi kasa da murya yace "What happen?" Tayi murmushin karfin hali ta girgiza masa kai, yace "No Halysaah, tell me why you became tensed all of a sudden..." Sauke idonta tayi jikinta yayi sanyi, ganin yana jiran amsarta ta kallesa a hankali tace "Kawai naji gabana yana faduwa ne, I don't know what I will meet home this time around" Calmly Jay yace "Babu abinda zaki tarar sai alkhairi in Sha Allah, stay positive dear" Sosai taji hankalinta ya kwanta with just his words, tayi murmushi tace "Toh Nagode" hannunsa ya saka a nata shi ma yana murmushin yana kallonta, ta zame hannunta da sauri, ta wani kallesa, kashe mata ido yayi yace "Ashe idan kina bacci sleeping beauty kike komawa..." Zaro ido tayi jin abinda yace, yana murmushi ya ciro wayarsa ya shiga videos din da yayi mata
ashi
ashi tana bacci, buda baki tayi with shock tana kallon video din da yake playing, kamar zata yi kuka tace "Innalillahi, ni dai wallahi ka goge" Murya can kasa yace "Anki"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH PAGE 84.

Sun sauka garin Kano karfe takwas bai karasa ba na safiyar, motar da zai dauke su har ya iso airport din yana jira, bayan drivern ya saka luggages din a booth Jay ya bude ma Khaleesat back seat ta shiga tana dan murmushi cikin sanyin murya tace
Thank you
murmushin yayi mata shi ma ya bude front seat ya shiga, Khaleesat tried her best to stay positive kamar yanda Jay yace mata all through the ride home, but she is excited and still tensed at the same time, suna isa layinsu driver yayi parking dai dai inda Jay yayi instructing dinsa, Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, Jay ya juya ya kalleta tayi murmushi a hankali tace
Thank you soo much Housemate
Har ta mance rabon ta kirasa da hakan a gabansa, shi dai kallonta kawai yake can yace
I don
t understand why you are thanking me for
Langwabe kai tayi tana murmushi tana kallonsa yace
Za ki sani
Tuni Drivern ya sauka daga motar ya zaga zuwa booth, Jay ya sauka shi ma ya nuna masa luggages din ta, Khaleesat na sauka daga motar yaran makotansu na kyallara ido suka ga ita ce suka taho da gudu suka baibaiyeta suna Oyoyo, Jay dai ya juya yana kallon ikon Allah, yaran ta hada da boxes dinta su shiga mata da shi gida, duk suka fara rige rigen dauka, ta juya ta kalli Jay tana murmushi tace
Zaka shiga ciki ne?

Ya rungume hannunsa yace
a, amma da yamma zan zo in sha Allah
A hankali tace
Allah ya kai mu
Yana murmushi yace
Ameen Halysaah
Ita ma murmushin tayi tace
Amma zaka dan kwana biyu a Kano before going to Bauchi?

Yace
a, gobe zan tafi in sha Allah, Mai martaba is worried about how of recent we are traveling separately with Ajay which is unlike us, kinsan for many month now bama tafiya tare kuma ba haka muka saba ba, duk tafiya tare muke yi da shi, so his highness is worried may be we had issues that we are hiding away from him, muna Turkey ya kirani nace masa gobe zan shiga Bauchin in sha Allah
Khaleesat dai tayi shiru tana kallonsa, can ta sauke idonta tace
Toh Allah ya kai mu goben
Yace
Ameen
Dubu hamsin rudin Nigeria ya dauko a gaban motar da alama Drivern ya sa ya taho masa da shi, ya mika mata yace
In case you will need anything Halysaah
Khaleesat ta zaro ido tace
a ni babu abinda zan bukata wallahi
Juyawa tayi zata bar wajen yace
Halysaah
Ta juyo amma bata ce komai ba, yace
Bana son kina min haka, ba ni na baki ba?
Chapter 178 · 0% Book details