← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 191

Sashe 46

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen karfe sha daya da rabi Khaleesat na kwance hannunta rike da wayar Housemate dinta, tun 20 min ago ta tashi daga baccin da ya dauketa daxu, she felt a bit relieved now da alluran da Salem yayi mata, sai dai har sannan kanta bai daina mata ciwo ba kamar ta cire ta huta, tayi kokarin ta tashi ma ta tafi bandaki amma ta kasa, she is so weak kamar warce ta dade tana ciwo, hakan yasa kawai ta jawo wayar Jay, da har zata shiga gallery dinsa to while away time amma sai taga it's not proper ta shiga hotunansa, hakan yasa ta shiga wani game da ta gani kawai tana yi daga kwancen da take, bude kofar dakin aka yi ta daga idonta, Jay ne ya shigo dakin AJ dake bayansa yaki karasowa ciki ya tsaya daga bakin kofar, Jay ya nufota yace "Ashe kin tashi, how are you feeling now Halysaah?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Good morning" Yace "Morning Housemate, are you feeling much better now?" Kai kawai ta gyada masa, yace "Ohk bari a kawo maki breakfast, idan kinyi sai ki daure ki sha magani kin ji" Ita dai bata ce masa komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita ya mika ma AJ wayarsa sannan ya sauka downstairs zai kawo mata breakfast, shi dai AJ daga sama har kasa yake kallonta, ta
an saci kallonsa to see if he is still standing by the door ko ya tafi, hada ido suka yi ta dauke idonta tana ci gaba da game dinta da take, after a while ta kara satan kallon bakin kofar taga ya bar wajen, sai ga Jay ya shigo ya ajiye mata tray din breakfast ta dinga kallon plate din baked beans irin na turawa a gefe da soyayyen kwai a gefe, with veggies, sai sausages, ga cup din hot chocolate with few slices of bread a gefe su ma, ita dai tasan ba iya cin wannan abincin zata yi ba, yana kallonta yace "Can you give me ur frnd Safiyyah's Home address?" Ta sauke idonta ta gaya masa address din, yace "Ohk, na ma san area din, i have a frnd there" Ita dai tayi shiru, ya dauko mata maganin da taki sha daxu ya ajiye kusa da ita yace "Pls ki daure kiyi breakfast din, sai ki sha drug din kafin in dawo" A hankali tace "Toh nagode" ya mata murmushi ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo.

Jay ya tarar da AJ zaune a waje gurin shan iska dake compound din yanna danna wayarsa, hakan yasa ya nufesa ya zauna kujeran dake facing dinsa yace "AJ, i think i am confuse at this point, what do u suggest about this young girl's issue?" AJ ya daga ido ya kalli Jay yace "My suggestion is that... ka barta ta tafi duk inda ma zata ka cire hannunka da bakinka cikin wannan case din babu abinda ya shafe ka, a cikin kunnenka kaji tace shi gayen ne ke sponsoring dinta, babu kuma ta yanda zai yi sponsoring dinta without the consent of her parent, kaga they are comfortable with that, so who are you to intrude Jawwad?

Baka san komai akan ta ko kan saurayin ba don me zaka zakalkale haka?

Tare fa ka gansu, da can baya zuwa America din ya sameta ne a gidan? sai yanzu tasan yana molesting dinta?

Girl's can be very cunning fiye da tunaninka, don't start what u can't finish Jawwad" Jay dake ta kallonsa yace "So now what are you insinuating?" AJ yace "Since you are daft kar Allah ya sa ka gane abinda nake insinuating" Jay dai kallonsa kawai yake, after a while a hankali yace "But duba da abinda ya faru tsakaninka da guy din kasan zai iya hurting dinta idan nace ta koma gidan nan AJ, she is no longer safe in that apartment, ka dai ga ba ma cikakken hankali ke gare gayen ba, ka duba fa wuka yaje ya dauko a kitchen" AJ ya gyara zama yace "Sai kayi mata hanyar komawa gun iyayenta as the good Samaritan that you are from Samaria, kaga in ta koma sai ta gaya ma iyayen nata abinda ke faruwa da abinda selfishness dinsu ya ja mata a kasar mutane, sai su yi sorting kansu a can kawai" Jay yace "Kar kace haka, we know nothing about why they allowed him to sponsor their daughter, we shouldn't judge them har sai mun san dalilinsu AJ" AJ yace "Dalilin banza, babu responsible parent din da za su damka ma kato irin wannan mutumin er su ya kai ta wata kasa da sunan karatu, it doesn't even make sense, sai kace ba musulmai ba, ko da cousin brother dinta ne ma abun bai yi tsari ba balle babu ko wani relationship na jini tsakaninsu, who does that" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk da haka dai ni bazan yi judging dinsu ba tare da nasan komai ba, let give them benefit of doubt" AJ yace "Sai kayi ta basu ai, ni kam bazan bayar ba" Jay yace "But komawarta Nigeria yanzu bazai yiwu ba AJ, ba shine solution ba, Monday za su fara exams, John Hopkins university take ita ma fa" AJ yayi dariya har da kyakyatawa yace "Tabb, lallai gayen ya kashe kudi ba na wasa ba" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ yace "Toh za a fara exams me kake nufi kenan?

Naji ka ce apartment din nata is not safe for her anymore..." Jay yace "She will remain here har su gama exam kafin ta koma Nigeria wajen iyayenta" AJ ya wani kallesa da sauri yace "What do you mean?

Kana nufin mu zauna gida daya da balagaggiyar yarinya da ba muharramar mu ba kamar wasu jahilai marasu tsoron Allah?

Kai da wa za ku yi wannan nonsense din??" Jay yace "Duk yan iskan turawan da kake kawowa gidan nan ka basu daki su zauna dama muharramanka ne ban sani ba?" AJ yace "Turawa kace ai, kuma babu komai tsakanina da su kai ma ka sani, i am only helping most of them tunda ba a garin nan suke ba" Jay ya mike yace "Ita ma haka za mu yi helping dinta tunda ba a garin take ba, take it or leave it" yana kai wa nan yayi wucewarsa inda yayi parking motarsa, Ajay ya bi sa da wani kallo, can yace "Sai dai ku je can ku biya wani apartment din ku zauna tare, babu wanda zai takurani a gidan nan wallahi, dama ai kun saba zama gida daya tare, it's not a new thing, dole ne sae ta zauna gidan nan cikinmu mu ba maguzawa ba" Shi dai Jay ya shiga motarsa ya fita daga compound din ya kama hanyar gidansu Safiyyah....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Jay na isa unguwan da gidansu Safiyyah yake sai ya mance apartment din da Khaleesat ta gaya masa, hakan yasa ya kira wayarsa dake wajenta, Khaleesat na zaune saman gado har sannan tana playing game da wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din wayar ganin image din hotonsa da number da yayi appearing, sai taga kamar shi din ne a gabanta take gani, sai da kiran ya katse ta zaro ido bayan tayi realizing bata yi picking ba har ya katse, bayan few seconds ya sake kira, dagawa tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Na'am" Yace "I think i forgot the apartment u told me" Gaya masa ta sake yi yace "Thank you" Daga haka ya katse wayar ya ci gaba da driving dinsa, dai dai gaban apartment din yayi parking don motar Mustapha baya nan, yana tsaye bakin kofa yayi knocking gently, after a minute aka bude kofar parlon, komawa baya Safiyyah tayi tana kallonsa da mamaki daga sama har kasa, ya
an mata murmushi yace "Hi Safiyyah" Ta bude ido sosai tana leka motarsa da taga yayi parking thinking may be he is together with Khaleesat, ganin motar ba kowa ciki tace "Hi, good afternoon" Yace "How are you doing Safiyyah?" Lokaci daya tace "Ko dai Khaleesat bata da lafiya ne?" Da damuwa sosai tayi tambayar, Yace "Yeah bata da lafiya" Tace "Wallahi yanzu na gama shiryawa nake son in ci abinci inje gidan naga miss call dinta jiya ina ta kira har yau wayar baya shiga, and i am disturb" Yace "Shi yasa na zo in dauke ki idan ba damuwa so you can be together with her she is sick, probably idan kin mata magana zata ci abinci ta sha magani" Da sauri Safiyyah tace "Sure, bari in dauko gyalena" Juyawa tayi da sauri ta koma cikin gidan, shi kuma ya koma parking space, Surayya dake zaune a parlon ta kasa kunne duk tana jin conversation dinsu kafin Safiyyah ta shigo, Safiyyah ko kallon direction dinta bata yi ba ta tafi dakinta da sauri ta dauko jakarta da gyale sai wayarta sannan ta fice daga gidan, ganin Jay cikin motarsa yana jiranta ta bude gaban motar ta shiga tana cewa "Tun jiya ne bata da lafiyan?

Kuma me yasa ta kashe wayarta?" Jay yace "Tace wayar ya fada ruwa ne" Safiyyah tace "Ohk" Sai da suka dau hanya sannan Jay yace "Amma tana can gidanmu fa, can za mu je yanzu" Safiyyah ta juya da sauri tana kallonsa da mamaki tace "Gidanku?

Why?

What happened?" Calmly yace "Before then za mu fara zuwa apartment dinmu sai ki dau mata kayanta da zata yi amfani da shi, we left yesterday with nothing" Safiyyah bata sake cewa komai ba tunani iri iri na yawo a ranta, to me ya faru? ta yaya Khaleesat da ta sani me shegen taurin kai ta yarda har ta bi sa can gidan nasu?

Ko dai rashin lafiyar nata is critical ne haka?
Chapter 46 · 0% Book details