← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 191

Sashe 79

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga Deejah me sana'ar lamurje da ganja, tare da Aunty Amzaj Maman mara Jidda da Damsalele, Uwata Zeenariya kema an gaisheki da babban murya tare da Hajiya Safiyyah Usman me kantin kayan yara
Aneesah Zero zero da Ummi matar mijin uwar gida ku ma na gaisheku da siririn murya, Barrister Inna da 'ya ta Uwar Annur da Hajiya Sadiya Uwar Hanan kuma duk na gaisheku da fatan alkhairi, Hajiya Sadiya Chamo au banda ke
, Mom Asas, Maman Faruk me data, da Sis Aisha Dalhat ga kuma Maman Aisha da Hajiya Bilkisu duk Khaleesat na maku fatan alheri
HALYSAAH 38
Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan Baaba Gaje da yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta ta
a saninta ba don casually ma take amsa mata kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abinda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace "Munnira me ke faruwa?" Munnira tace "Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayaniyar tayi yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika, ance a katuwar mota suka zo...." Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da su Islam ta shiga gidan har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani tsaye da 'ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai cike yake da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace "Wai me ke faruwa ne a gidan?" Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace "Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna zazzaune sai ga wasu kattin gardawa sun kusa goma babu annuri a tare da su sun shigo mana gida da makamai suna tambayar dakin Malam, basu tsaya iya dakin Malam ba hatta sauran dakunan gidan nan sai da suka shiga..." Sai a sannan Umma ta lura da bakin kofar shiga dakin Malam Ali, gaba daya yayi kaca kaca da takardun da ta mayar daxu bayan su Jay sun dau wanda za su dauka, har kayan cikin dakin sai da aka watso su waje har da er katifarsa da akwatin kayan sakawan sa da butar alwalansa, Umma ta juya tana bin tsakar gidan da kallo taga har dakinta an fito da kaya an yi watsi da su waje, da kyar Umma ta karasa kofar dakin Malam Ali ta leka ciki taga basu bar komai ba, dama ba wasu abun kirki ke cikin dakin ba, can ta juya tana kallon Kishiyoyinta amma ta ma rasa me zata ce, Mama Shatu ta kyabe baki tace "Ni takaicina dakunan mu da suka shiga wai ina takardun da Malam ya ba mu ajiya, ni ko nace mu muka san wasu takardu mu da bamu yi karatu ba ta yaya Malam zai bamu takardu mu ajiye ai sai dai ko ya ba er sa da aka kai turai karatu daga karshe tayi ma wanda ya kai ta karatun butulci wai bata son sa kuma, amma ina mu ina ajiyar takardu mu da muke jahilai" Umma bata tanka ta ba ta duka tana tattara takardun dake watse bakin kofar su Islam suka je suna tayata, a haka duk ta maida kayan Malam Ali cikin dakinsa, su Mama Zubaida sai hararanta suke, can Mama Shatu ta kyabe baki tace "Mu dai mun san ko ma wani takarda suke nema bazai wuce yana da alaka da er ki ba kilan kotu za a shiga, tun da kika haifi yarinyar nan muke shiga jarabawa munana a gidan nan, ko kuma muce tunda aka auro ki, mu da bamu san wani talauci ba balle wahalar rayuwa, daga auro ki karayar arzikin da ba a ta
a yin irinsa a tarihi ba ya samu Malam, sannan gashi sanadin er da kika haifo ga abinda ya samu Malam a karo na biyu, daga ke har 'ya yanki babu wani abun alkhairi a tare da ku sai masifa, ina ma Malam zai yada kwallon mangwaro ya huta mu ma mu huta ki tattara ki koma can kasar ku ki auri buzu
an uwanki" Sha'awa dake tsakar gidan wanda tana daga cikin mutanen farko da suka shigo bayan Mama Zubaida da Mama Shatu sun kurma ihu, amma fa sai da gardawan suka fita sannan suka samu bakin ihun neman agaji su da yaransu, Sha'awa tace "Haba Mama Shatu, wannan wani irin magana ce kike yi haka don kin ga Ummansu Khaleesah bata tanka ku a gidan nan, wannan ai cin fuska ne, kar fa wataran ku kureta ayi dauki ba dadi a gidan nan, don mai hakuri bai iya fushi ba wallahi" Wani zagi Mama Shatu ta kundumo mata a fusace, Sha'awa ta rama tace "Wallahi ba dai ubana ba, sai ko in naki uban me gyaran keke dake kabari" Ganin fada na kokarin kaurewa a tsakar gidan Umma da wasu mata suka fitar da sha'awa dake kunduma ma Mama Shatu zagi ta uwa ta uba, ga su Labeebah na kokarin dambe da Sha'awa dake zagar masu uwa su ma duk aka rirrike su, a haka dai aka fitar da Sha'awa dake gyara daurin zaninta da ya kusa faduwa gashi babu komai kasan zanin, tana huci take cewa "Shegu en kutumar uba masu bin bokaye, ko jiya sai da aka bani labarin kun je wajen wani boka na kuma san warce ta raka ku, kun ga kuwa Umman Khaleesah ta fi ku ko a wajen Allah tunda bata san hanyar zuwa gun Malamai ba" A haka dai aka fitar da Sha'awa daga gidan, Umma dai jiki a sanyaye ta tafi kofar dakinta ta tarar su Islam suna ta maida kayan cikin dakin da aka watso waje bayan sun kunna er fitilar dake ba dakin hasken, Noor na kallon Umma tace "Umma kinga babu kayan abincin a inda suke" Umma ta kalli inda Maman Salame ta ajiye mata kayayyakin abincin da su Jay suka kawo taga wayam, tsayawa tayi tana kallon wajen babu ko kiftawa tsabar mamaki yasa ta kasa cewa komai, muryar Nenne taji a tsakar gidan cikin fushi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meye haka aka cika gidan nan kamar ana taron farin ciki?

Ku yan unguwan nan tsabar munafurci da gulma bakwa tashi shigowa sai iftila'i ya faru sannan ku bi ku cika ma mutane gida ko wacce da warin jikinta, farin cikin iftila'in ku ke ko menene haka?

Doo Allah duk ku fita ku ba mutane waje mu ji da daya, ai ba kanmu farau ba, en iska kawai magulmata" Rai bace ta nufi dakin Umma hannunta rike da jarkar manja daya hannun kuma rike da tocilan ta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Zahra'u me suka dauka a dakin Alin da suka zo?" Umma da ta zauna gefen katifar ta tace "Shigowa ta kenan nima Nenne, na je gidan Baaba Gaje an sakota daxu da yamma" Nenne ta kalli kayan da su Islam ke shigarwa daki tace "Har dakin naki suka shiga ne?

To ni Usama ce min yayi iya dakin Ali suka shiga suka watso kayan ciki, ke kuma wa ya watso naki tsummokaran waje?" Mama Shatu tace "To shi da ya sulale ya gudu ya bar gidan ta yaya zai ce iya dakin Malam suka shiga?

Ai babu dakin da basu shiga ba a gidan nan yau, mu ma duk mayar da namu kayan mu ka yi, hatta babban jarkan mangyada da na siya jiya sun dauke, iya shi suka dauka a dakina, Ita kuwa Zubaida kwashin adashin da aka kawo mata suka dauke" Nenne ta fara matsar kwalla cikin rawan murya tace "Lallai na ga abinda ya isheni bai ishi Ubangijina ba, to yan fashi Awdul din ya aiko mana wannan karan?

Don dai duk mun san yafi karfin wani kudin adashin da bai taka kara ya karya ba balle wata jarkan mangyada, Allah mun gode maka da wannan rantsattsiyar jarabawan da mu ke ciki mun gode maka Allah, Alhamdulillahi ya Allah, Ina ga in ba tattarawa muka yi muka hakura da zaman birni mu koma kauye gaba daya ba muna cikin mummunan hatsari a Mariri gashi ba mu da gata, kar wataran cikin dare mun saki baki muna bacci su babbake mu, su babbake banza tunda babu me
tsaya mana" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Nenne na kallonta tace "Su kuma samarin da suka sha uban fararen kaya suka zo mana nan suna kwambo dama yaudarar mu suka zo yi bamu sani ba, sun zo nan sun gama cika mana baki sai gashi tunda suka karkade wandonsu suka fita bamu sake ganin keyar su ba, to ina amfanin karya? har da ce min za a saki Ali kwanan nan ashe duk yan iskan gari ne makaryata bamu sani ba" Umma dai kallon Nenne kawai take, Nenne ta mika ma Islam jarkan manjan hannunta tace "Ba ruwana, wahalan da nake ta sha kan Ali ko shi ya halittoni duniya ai sai haka, kai kenan kullum ayi ta garkame ka kamar kasungumin barawo, sai kace wanda yayi ma Allah wani sa
on da bamu sani ba, saura kadan kwale kwalen da na hau jiya zan je nema masa taimako ya kife da mu banda Allah ya tsare, to ina dalili bayan ba shi kadai na haifa ba, in ya kasheni sauran su yi yaya? ke ungo amsa ki mika ma uwarki ta tsiyaya min manja, nawa ya kare" Islam tace "To ai an kwashe kayan abincin gaba daya Nenne" Nenne ta gwalo ido tana kallon direction din da aka ajiye kayan abincin taga wayam, bude baki tayi tana kallon Umma tace "Zahra'u ina kayan abincin?

Ko kasuwa ki ka kai kika siyar?
Chapter 79 · 0% Book details