Sashe 185
Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Farida ta jingina jikin cabinet ita ma dai duk jikinta a sanyaye, she wish everything will be easy as it seems now, amma gidan sarauta abun su sai su, babu abinda ya kara kashe mata jiki sai zancen Hadiyah da kuma alakarsa da Hadiyar da Khaleesat ta gaya mata, amma don ta kwantar mata da hankali ta sauke ajiyar zuciya tace "Ki ci gaba da addu'a Khaleesat, Nima zan taya ki, Umma ma zan yi mata magana duk za mu taya ki da addu'a, Allah Ubangiji ya kawo komai da sauki, kuma Allah ya tabbatar da alkhairi" Har sannan Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta nufi kofa ta fita daga kitchen din, sai a sannan Khaleesat taji hawaye masu zafi sun zubo idonta, ta juya tana kallon windown kitchen din babu ko kiftawa, da Aunty Farida bata ankarar da ita ba da bazata ta
a hango kalubalen dake tattare da aurenta da Jay yace zai yi ba, she never saw all this coming, kasa controlling kanta tayi ta duka a hankali kitchen din hawaye na zubo mata, sai yanxu ta kara tabbatar da masifaffen son da take ma Jay a ranta, she can't imagine loosing him, hade kanta tayi da gwiwa hawaye masu zafi na zubo mata tana shesshekan kuka....
Aunty Farida na shiga dakin Umma ta sameta tana waya da Malam Ali, hakan yasa ta juya ta bar dakin, sosai wannan maganar da Khaleesat tayi mata ya tsaya mata a rai, she don't want her to go through another heartbreak, kuma ta lura tayi zurfi a son nasa ita ma with the way she reacted, tana shigowa parlor Nenne tace "Zuwa nan da anjima kadan fa za mu fara ganin yan uwa sun zo mana Allah ya sanya alkhairi Parida, er shinkafar nan zata isa a girka a
an tarfa ma kowa a kwano kuwa?" Aunty Farida tace "Idan mun karya za mu fita kasuwa da Khaleesat, da kudi a hannuna sai a siyo duk abubuwan da ya kamata...." Nenne tace "Allah Ubangiji dai ya baki miji nagari kema kiyi auren ki Parida, bauta kam kin bauta ma yayarki, abun ki bai rufe maki ido ba sam, kin rike zumunci gaskiya" Ita dai Aunty Farida kawai tayi murmushi bata ce komai ba, Nenne tace "Dama mun taho da tabarmin mu, su za a shimfida a tsakar gida babu shegen da zai shigo mana nan a lalata mana sabon waje, kowa yayi Allah ya sanya alkhairinsa daga tsakar gida ya kama gabansa" Wajen karfe goma da rabi Aunty Farida da Khaleesat suka bar gidan za su je kasuwa siyayya, Khaleesat har ta mance rabon ta shiga damuwa irin wannan da take ciki yanxu, sau biyu ta kira Jay daxu taga bai dauka ba shine damuwar nata ya linku akan wanda take ciki tun bayan maganganun Aunty Farida daxu a kitchen, Aunty Farida na kula da yanda tayi sanyi gaba daya bata da kuzari tun daxu, bayan sun shiga adaidaita Sahu da zai kai su kasuwan Aunty Farida tayi kasa da murya tace "Damuwa kike son sa ma kanki Khaleesat?" Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "A'a Aunty" Da sauri ta kauda zancen tace "Safiyyah ce ma daxu ta min voice tana kuka wai kilan shirgata yayanta yayi, gashi ta saka ran dawowa, ni dama a raina nasan ba lallai ya barta ta dawo ba" Tana dariyar karfin hali ta kare maganar, Aunty Farida tace "Ai ko bai kyauta mata ba, Allah sarki baiwar Allah" Har suka isa kasuwan Khaleesat was trying to act alright, amma Aunty Farida tasan deceiving kanta kawai take, Aunty Farida bata zo kasuwa da Khaleesat with the expectation of her buying anything ba don bata san tana da kudi ba ma, ita dama Aunty Farida da dubu
ari biyu ta shigo kasuwan domin ta
an tsintsintar masu abubuwan da za su bukata na gida, har da su Bucket da sabulu da omo da su tsintsiya da mop, duk dai wani abun amfanin gidan, sauran kudin kuma tayi maneji ta
an hada masu kayan abinci da cefane ko babu yawa, amma nan take Khaleesat tayi withdrawing 1M a kasuwan, don kudi ne sosai a account dinta wanda Jay ke tura mata a kai a kai na Uber da kuma wasu abubuwa idan tana bukata barin sanda ya dade a Nigeria bai dawo ba, sanda yake Nigeria kuma Ajay ma ya amshi account dinta during that period ya tura mata kudi multiple times for her transportation to school and in case she needs to get anything for herself, duk da abubuwa da yawa shi yake siya mata a lokacin, kuma in ya tashi tura mata kudin shi ma ba kudi kadan yake saka mata ba, sannan ga 5000 dollars da Mai martaba ya bata, dama Safiyyah taki amsan wanda ta bata a ciki, Jay kuma ya amshi kudin yayi mata transfer dinsa gaba daya a account dinta, ganin uban kudin da Khaleesat ta cire Aunty Farida ta fara fada tace "Baki da hankali ne?
Ke da ba gama karatun kika yi ba zaki ciro wannan kudi haka" Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "Aunty in babu ai bazan cire ba, akwai kudi a account din ne" Sai wajen karfe daya suka koma gida da siyayya ma
il, a compound suka tarar da yan zuwa sanya alkhairi Nenne ta shimfida masu tabarma ta hada kowa da pure water, tana zaune kan kujerar plastic ta
ora kafa daya kan daya, ita ma Umma na zaune tsakar gidan don ta rasa yanda zata yi da Nenne, ko kadan bata ji dadin barin jama'a da tayi a tsakar gida ba taki bari su shiga cikin gidan.
Nenne tayi kicin kicin da fuska don bata so su Aunty Farida sun shigo da kayan da suka siyo kan idon mutanen dake tsakar gidan ba, a haka dai su Islam da Noor suka dinga diban kayan da za su iya dauka suna kai wa cikin gidan, Khaleesat ta dau iya wanda zata iya dauka sannan ta wuce ciki ta tafi daki tayi wanka ta dauro alwala tayi sallah sannan ta kwanta, sosai hankalinta ke a tashe ganin Jay bai biyo kiranta ba har lkcn, Umma ta shigo daki tana kallonta tace "Khaleesah ke da ke karatu har yanzu menene na kashe kudi har haka?" Khaleesat ta kalli Umma tace "Na fa ce ma Aunty Farida akwai kudi a account din ne Umma" Umma tace "Toh Allah yayi albarka, ki tashi ki zubo abinci ki ci" Khaleesat tace "Anjima zan ci Umma" Umma tace "Allah ya kai mu" Daga haka ta fita daga dakin, Khaleesat ta koma a sanyaye ta kwanta, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a ranta, hawaye taji ya cika idonta ta rufe fuskarta da Pillow ta fara shesshekan kuka a hankali....
Nenne ta fita ta zagaye unguwan tana neman almajirai da za su kama buhunhunan shinkafar da su Aunty Farida suka siyo a shiga da shi kitchen, da kyar ta samo almajiran biyu ta dawo tana mitan su Mariri yaushe za a nemi almajirai a rasa, daya daga mutanen dake zaune tsakar gida tace "Ai da kin mana magana mu kama mu shiga da shi ciki Nenne" Nenne tayi banza da ita tana tafe almajiran na biye da ita a baya har aka shiga da buhunhunan kitchen, naira hamsin ta basu suka tsaya suna kallon ta, tace "Lafiya ku ke kallona haka?" Wata er cousin din Malam Ali tayi dariya tace "Ya masu kadan Nenne, ke baki ga unguwan ta masu kudi bace, ai hansin ta masu kadan" Nenne ta juya ta kalli almajiran baki bude, kafin tace komai Umma ta mika masu dari biyu su hada da Naira hamsin din, suka amsa suka fita daga gidan, Nenne ta kalli Umma tace "Kin ji almajirai kamar barayi, mu Mariri yaushe almajirai za su yi haka?
Kudin ne ya maki yawa kika basu dari biyu, ai niyyar ce masu su shiga su fito da buhunhunan shinkafar nake da shi" Nenne bata rufe baki ba aka rafka sallama bakin gate, duk aka juya ana kallon gate din gidan sai ga Sha'awa da yan Mariri su hudu sun shigo cikin compound din kafafuwansu butu butu da
ura, Nenne da ta girgiza sosai ganinsu tace "Su waye nake gani haka, daga ina?" Sha'awa na washe baki tace "Su mu ne Nenne, Sha'awa ce da su Maman Sagir da Maman Balki da Maman Shehu, sai sabuwa" Nenne da zufa ya keto mata ta ja kujera ta zauna da kyar tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, wa ya nuna maku gidan?" Ita kanta Umma was so shock amma hakan bai hanata dinga ce masu sannu da zuwa ba da murmushinta duk da gaba daya hankalinsu na kan Nenne da ta tsare su da tambayoyi cikin kidimewa, Sha'awa tace "Almajirin ki ne wai an ta
a zuwa da shi yayi share share da goge goge sanda aka siya gidan, ai ko ranan yayi ma Salisun Tabawa kwatancen gidan ashe Salisu sun ta
a zuwa aikin pilamba a wani gida a Tudun Yola, shi ne muka sa yayi mana kwatance, tun karfe sha dayan safe muke neman gidan sai da muka zaga kaf Tudun Yola muna cewa sabon gidan da aka tare jiya da daddare muke nema, da kyar wallahi aka gano gidan da taimakon wasu yara, ga uban kudin mota duk bamu san haka unguwan ke da nisa ba, ko sallan azahar bamu yi ba ga la'asar ta gabato" Nenne ta rike kai tace "Hu....huhu, ashe dama
anLami munafiki ne
an iska ban sani ba nake alaka da shi jama'a?
Wa iyazubillahi" Ita dai Umma ta shimfida masu wani tabarma tana welcoming dinsu da fara'a kafin Nenne tayi recovering daga shock din da ta shiga ta fatattake su daga gidan don tsaf next action dinta kenan.