← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 191

Sashe 183

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe goma sha daya Nenne ta shigo gidan ta nemi kujera er tsugunno ta zauna tana kwalo ma Umma kira, Khaleesat dake wanke wanke a tsakar gidan ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Ahamad din ya tafi Bauchin kuwa, yace min da sassafe zai bi hanya yau" Khaleesat tace "Har ya isa tun karfe goma" Nenne tace "Maa sha Allahu haka ake so, in kun yi waya ki ce ina gaishesa don Allah, ni ba waya gareni ba balle in kirasa, amma kar ki ce masa haka, kawai kice ina gaishesa ina masa bangajiya" Khaleesat na dauraye kwanon hannunta tace "Toh" Sai da Umma ta fito sannan Nenne ta amsa gaisuwan su Mama Zubaida a dakile ba tare da ta kalli inda suke ba, Umma ta zauna kan tabarman dake shimfide ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Ina parida" Bata rufe baki ba sai ga Aunty Farida ta fito dakin Umma, ita ma ta gaida Nenne ta amsa sannan tayi kasa da murya tana kallon Umma tace "Zaura'u, ina ga fa lallai lallai yau za mu bi dare mu bar unguwan nan, don daxu almajirina ke ce min yaga Awdul ya shigo unguwan nan da safe" Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon Nenne gabanta na faduwa, Nenne tace "Don haka baza mu biye All ba, In yaga duk mun tattara mun tafi ya biyo mu da dan akwatinsa, don ba irin maganar da ban masa jiya da daddare ba kan ya hakura ya amshi gidan nan da bawan Allahn nan ya siya masa hannu bibbiyu don da zuciya daya ya siya masa, amma tsoro ya hana Ali sakat, yace shi tsoro yake gaskiya...." Umma dai tayi shiru don bata san me zata ce ba, ita kanta hankalinta ba a kwance yake ba tunda Khaleesat ta dawo jiya don bata san wani mugun abun ke ran Abdul ba, tana ta tsoron kar ya samu labarin ta dawo ma, Nenne tace "Sabili da haka cikin dubara a kira makota duk a basu sadakar abubuwan da baza mu koma sabon gidan da shi ba, irinsu rubabbun tukwanen ku da katifa da tarkacen kwanukan ku, don babu abinda yaron bai zuba mana a gidan ba har kujeru da kayan gado, sannan na aika aje kasuwa a kira min Ali yayi maza ya dawo babu lafiya, so nake ya dawo mu ji yanda zai yi da matansa don baza su bi mu gidan nan ba gaskiya, in ma kauye zai maida su ya dinga zuwa can duk sati yana duba su to" Daga Mama Zubaida har Mama Shatu suka juya suna kallon Nenne, Nenne tace "Don ban ga inda za a kunna icce ko kuma a dafa abincin talla a wannan tanfatsetsen gidan da yaron nan ya siya mana ba, ko ina tas ne malale a kasa, komai sabo dal" Umma dake ta kallon Nenne tace "Ki dai yi hakuri Nenne don da mu da su Shatu duk daya muke a wajen Malam, dakuna shidda ne a gidan banda gini daban me daki daya da parlor da bandaki da kitchen, duk zai ishe mu Nenne" Nenne tace "Ke in baki da hankali ni ina da shi Zahra'u, banda karamin tunani irin naki kinga gidan yayi kalan Shatu da Zubaida?

Kinga alamar kazanta zata samu muhalli a wannan tanfatsetsen gidan kamar a kasar waje?Na kirga dakuna biyar a gidan da katon parlor sal wawakeken kitchen, sannan har da bangaren me gida duk a cikin gidan, shima naga parlor ne sai daki da bandaki, to wannan na Ali ne, ke kuma ki dau daki daya, Farida daki daya, Khaleesah daki daya, yan biyunki ma a basu daki daya, daki daya da ya rage ya zama na saukan baki, ginin dake waje dama nace nawa ne ni zan zauna ciki kada wanda ya saka ma ginin ido, to a ina kika ga dakunan da za a zuba su Zubaida da 'ya yansu rakacaa idan ba dai baki de nankali ba?

Ai babu guri a gidan, kai ko da wurin ma ni sam bazan amince in zauna da su Shatu ba sai dai ni in hakura da tarewa a gidan inyi zamana a Mariri har wa'adin da Allah ya dibar min a duniya ya cika in koma garesa, in kuma ance lallal lallai sai sun bi mu ta sai dai Malam Ali ya siyar da wnn gidan da nawa ya tafi unguwan yaku bayi ya siya masu gida me dakuna uku ya ajiye su da 'ya yan su, amma wannan gida kam ta silan Khaleesah aka siyesa ba wani shege ba, yau in tace n
ma bazan shiga ba ya zauna balle wasu yan iska Zubaida da Shatu, da ma suna ganin mutuncin mijinsu ne balle ni, balle ke karan kada miya da suka rena, yau watanni kusan hudu kenan babu abinda Ali ya rage su da shi a gidan nan, tun da Allah ya saka ma hatsin da ya fara siyarwa a kasuwa albarka bai ragi iyalinsa da komai ba komai korrai yi masu yake, amma sun ki dena abincin siyarwa don su yi ta ja masa zagi a gari, kudin makarantan yara idan ya basu sai su bi su kwace su bar yaran suyi ta yawo kamar almajirai a unguwa suna talla, to ina amfanin matan nan?

Shi dai wannan yaro da ya basa jari Allah yayi masa albarka..." Nenne te kalli Khaleesat tace "Ya sunan abokin Ahamad din nan mara fara'a?" Khaleesat ta daga ido ta kalli Nenne, Umma dai tayi shiru don bata san me zata ce ba kuma, Aunty Farida ma dai is speechless, Nenne ta mike tsaye tace "Duk ki fito da tarkacen ki Zahra'u a bada su sadaka, in sha Allahu baza mu kwana a gidan nan ba, gwara mu koma gida me get yanda sai an kwankwasa ma za mu bude, shi kuma Ali ya dawo yasan yanda zai yi da matan nan nasa, bari inje in fara harhada nawa kayan, ina nan dawowa nan ba da dagowa ba, ni dama ba shirgi ne da ni ba, ai 'ya mace abar alfahari ce in dai ka tsaya kayi mata tarbiyya yanda ya dace, da Khaleesat bata da tarblyya uban wa zai kalleta balle har ayi mana wannan abun arzikin ta dalilinta, wannan kadai ya ishi yan baya izini, in za su tsaya su tarbiyyantar da 'ya yansu su zama na kwarai to su za su ci riba ba wani ba" Nenne na kai wa nan ta kalli Aunty Farida tace "Dauko gyalenki mu tafi ki tayani parida, in akwal abinda zan bayar kawai aiken k
i zanyi kiyi sallama gida ki kira matar gidan ku taho tare, cikin sirri nake son ayi komai" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida ta mike ta dauko Hijab dinta ta bi bayanta ta fita, Bayan yan mintuna Mama Zubaida ta mike ta tafi ta bude kofar gidan tana leka waje taga Nenne da Aunty Farida har sun sha kwanan gidanta, dawowa tayi tsakar idanta, gidan tana ma Umma matsiyacin kallo tace ""Aikin banza, aikin hofi, kur
zauna kun tsara kayan ku shine kike son ki mayar da mu yan iska ke ga er slyasa, bayan duk kin san da tsarin, kin ga wannan sabon gidan In anyi duniya don manzon Allah sai ya zame maku bala'l da fitinar da yafi karfin ku, sai kun gwammace ba a baku ba, kuma waye bai san me Khaleesah tayi aka bata gidan ba?

Mu duk bamu yi mamaki ba don mun san ba yanxu ta fara karuwanci ba, kuma muna nan dake sai ta jajibo maku abun kunyan da har ku mutu bazai goge ba daga ke har Nennen, bakin cikin abun kunyan ne kuma zai kar ki har lahira" Umma ta mike tana murmushi tace "Ni dai kullum ina maku tuni da ku koma islamiyya ko za ku samu saukin jahilcin nan, in sha Allahu kuma ni da zuri'ata babu abinda za mu gani sai alkhairi, Allah ya baku lafiyan cutar hassadan dake neman nakasa maku zuciya..." Mikewa Shatu tayi, Umma bata sake bi ta kansu ba ta shige dakinta, Khaleesat dai murmushi kawai take ta mike ta wuce daki ita ma, hayaniya Mama Zubaida da Mama Shatu suka dinga yi a gidan suna batanci da fadin mugaven kalamai har sal da makota suka shigo bada hakuri, ita dai Umma tuni ta sake labulen dakinta tayi kamar bata san da ita suke ba.

Bayan la'asar Nenne ta dawo gidan da Aunty Farida, sai ga sha'awa da wasu makotansu Umma su uku sun shigo gidan su ma, duk Nenne ce tasa Aunty Farida ta shiga gidajen su ta kirasu, Nenne na tsaye har Umma ta gama fiddo duk kayan da zata bada, Nenne ta dau zannuwan gado biyu ta wurga ma Sha'awa da wata tukunyar Umma, haka ta dinga rarraba kayan tsakanin makotan da tasa aka kira mata suna girmamata awa enda ke ganin mtuncinta suna girmamata a unguwan, bayan sun kare ta mike tace "Toh gasu nan saboda Allah, shirgi ne suka mata yawa take bayarwa..." Su Mama Zubaida dai na tsaye bakin kofar dakin su fuskokinsu a murtuke suna kallon ikon Allah, Nenne ta sallami makotan duk suka fita gidan suna godiya kaca kaca, sal kuma ta kalli Umma tace "Kin gama hade kayayyakin naku na sa wa dake da yaran ki?

Har fa mun je mun samo motar da zata kwashe mu anjima, karfe sha daya da rabi na dare muka yi da me motar" Umma tace "To Allah ya kai mu" Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne tace "Yauwa Ali, mu dai anjima za mu bar gidan nan kamar yanda na gaya maka jiya, yanxu ya za kayi da shirga shirgan matan nan naka?

Kauye zaka tura su zuwa sanda zaka samar masu gidan haya ne ko ya zaka yi da su?
Chapter 183 · 0% Book details