← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 191

Sashe 168

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wato ke kawai kulasa kike yi kaca kaca a gidan ma kenan" Khaleesat tace "Ni dai wallahi ban ce maki haka ba kece dai baki fahimce ni ba, mutumin da ba magana ma sosai yake min a gidan ba" Safiyyah tace "Oho dai ni har kin bata min rai wallahi, sai kace wata kuturwa meye na dinga cin abincinsa da ya dafa da baza ki dafa naki ba" Khaleesat dai kallonta take, Safiyyah na gyara
ankwalin kanta tace "Housemate ai bazai ji dadi ba fisabilillahi, ni ma kaina ban ji dadi ba balle shi da baza a rasa sa da kishi ba tunda duk mun san yana sonki" Ita dai Khaleesat bata ma san me zata ce ba, amma da gaske Ajay ko lkcn kulata ma baya da shi a gidan, iyaka yayi masifa in ta debar masa abinci kuma wani lkcn late take komawa gida shi yasa ma bata girkin in taga yayi sai ta debi nasa, kuma ka
an yake dafawa kamar abincin rowa, can ta ta
e baki tace "Wai ke ance maki yana da time dina ne a gidan, shi fa kawai ya kalli football ko wrestling or boxing sai kuma ya buga PS5 dinsa" Safiyyah ta kalleta da sauri tace "Ke haba, da gaske? yaushe ya kawo PS5 din?" Khaleesat tace "Oho kawai gani nayi nima" Safiyyah tace "Ki ce wataran idan naje gidan baya nan za mu buga" Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace "Za ki buga dai, ni ba ruwana" Safiyyah tace "Kin tuna na saurayin former Housemate dinki Nancy, a sannan fa kema kika iya, Mutumin kirki haka ya bar mana ps4 dinsa a gidan da yaga muna so, kullum sai naje apartment dinki saboda shi lokacin muna level 2, mu yi ta buga game" Khaleesat tace "Hmm na tuna, ai yanxu ma idan naga yana yi sai in makale in ta kallo, kamar inje inyi" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Wani rana da wani rana ne baya zaman gidan?" Khaleesat tace "Every Saturday saboda ina tsayawa school mu yi karatu baya zama gidan sai sanda zan dawo da yamma yake dawowa shi ma" Safiyya tace "Tunda dai ba mu muka kawo karatun nan duniya ba, gobe kawai in kin taho school sai mu koma apartment dinki tare da sauri mu buga PS5 din, abinda ma mun gama karatun course din da za muyi ran Monday in de ba haram za mu kara karantawa ba, kawai mu je mu shoshale a apartment din ki da Ps5" Khaleesat ta zaro ido jin wayarta na vibrate tace "Lahh, na manta ban kai masa key din ba" Safiyyah tace "Je ki kai masa ki dawo mu ci gaba da maganar mu, ai ni ban san yana da ps5 ba" Khaleesat ta mike ta bar wajen, duk da hadarin dake gari Safiyyah ke ce mata taje ta dawo su ci gaba da magana ko a jikinta idan ruwa ya musu duka.

Khaleesat bata karasa inda Ajay yayi parking ba aka fara yayyafi, tana isa wajen ta bude front seat ta mika masa makullin apartment din, zata kulle motar yace "Kwana za ki yi a makarantar?" Tayi shiru bata ce komai ba, can tace "To zan je in ma kawata sallama" Yace "Ohk" Juyawa tayi ta koma inda ta baro Safiyyah, Safiyyah na ganinta tace "Kin ga an fara yayyafi, mu koma department mu ci gaba da maganar mu..." Khaleesat tace "Gida ma zan wuce" Safiyyah ta tabe baki tace "Motarsa za ki shiga kenan?

Dama abinda yasa ya kira ki kenan ya ga hadari" Khaleesat tace "To ba waje daya za mu ba in ma saboda hakan ya kirani?

Dama dawowa nayi in maki sallama sae gobe" Safiyyah tace "Ai shikenan" Khaleesat tace "Ko kuma tunda hanya daya ne mu je yayi dropping din ki kawai mana" Safiyyah tace "Wa??

Gwara inyi trekking inje gida, salon ya koreni, kema da kike iyayin cewa in shiga motar ba kyaleki zai yi ba....

Hadawa zai yi ya fatattake mu" Khaleesat bata sake ce mata komai ba suka nufi inda Ajay yayi parking, suna karasawa wajen Khaleesat tayi shiru ta tsaya ganin babu motarsa, can ta
an kalli Safiyyah ta gefen ido, Safiyyah dake ta waige waige tana neman motar Ajay tace "Ina motar tasa?" Khaleesat tace "Kawai mu tafi mu hau Uber" Da Safiyyah ta fara ba
aka dariya har da durkusawa kasa, tun Khaleesat na daurewa har ta kasa ita ma ta fara dariyan, da kyar Safiyyah ta dago tsabar dariya har da hawaye tace "Har kina min iyayin in shiga ayi dropping dina ke me sabon Housemate, yanxun nan kika gama kakkaresa sai gashi ya shuka maki rashin mutunci, an gaya maki Ajay zai canza halinsa ne" Khaleesat ta ta
e baki ta bude handbag dinta ta ciro waya zata yi ordering ride, har suka rabu da Safiyyah dariya take mata kamar zata shide, ita dai ko tanka ta bata sake yi ba....

Jay na zaune motarsa yana waya da Mami yaga Khaleesat ta sauka daga Uber din da ya ajiyeta, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment dinta bata lura da shi ba, Muryar Mami yaji tana ta masa magana, ya
an sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali yace "Idan na dawo za mu yi magana Mami it's nothing to be worried about, in less than 3 weeks zan dawo Nigeria in sha Allah" Daga daya bangaren Mami tace "Jawwad kana tunanin da akwai wani abinda zaka tambayeni da zan ki maka ne?

Plss tell me what you want, hankalina bazai kwanta har nan da sati uku ba, ko kuma in taho Maryland din ne?" Jay yace "A'a Mami ba sai kin zo, ba wani abu bane da zaki damu kanki, idan na dawo za mu yi magana" Mami dai tayi shiru, alamar bata gamsu ba.
Chapter 168 · 0% Book details