← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 191

Sashe 24

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni nace ina kunyan in ci abincin?" Ya
an bude ido yace "Naga u ate just the Tacos bayan ga abinci da yawa a gabanki" Ta sauke idonta tace "Nafi son sa ne" Yana goge lips dinsa da tissue alamar ya koshi yace "Ohk, so now can i talk to you?" Shiru tayi na few seconds, sai kuma ta kallesa a hankali tace "Ohk" Ya karasa shanye drink dinsa yace "A nan America kika hadu da saurayin naki ko a Nigeria?" Khaleesat was silent, sai kuma ta sauke idonta tace "Nigeria" Yace "Ohk, but me kike tunanin yake janyo maku matsala tsakaninku?" Ta girgiza kai tace "Nima ban sani ba" Yace "Saboda ke ya taho nan daga Nigeria or he have a business here?" Ta gyada masa kai tace "Saboda ni ya zo" ya gyara zama yace "Kinga yana sonki kenan, sosai ma kuwa yake sonki, he left everything he was doing and came over just to see you, in na fahimta bai son kiyi sharing apartment da namiji a kasar nan ko?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana wasa da gefen mayafinta, yace "Sure... yana da gaskiyarsa, don ko ni bazan bar budurwata tayi communal living ba" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, Yace "Yanzu dai kiyi kokari ki basa hakuri ku dai daita kanku, ni kuma i will think of another alternative for peace to reign between u and ur boyfriend, sannan shawaran da zan baki shine try all possible best ki dinga nuna masa abinda baza ki yi tolerating ba tun kafin kuyi aure, ya kamata ace akwai mutual understanding tsakanin ku, he look cool though kawai yana da hot temper ne and i notice insecurity na daya daga cikin matsalarku da shi, but you can definitely change him gradually Halysaah, so last maganar da zan maki ina ga ba abinda ya shafeni bane, kawai dai zan tunatar da ke Do's and don't din addininki ta bangaren relationship tsakanin mace da namiji" Khaleesat dai sauraronsa kawai take without looking at him, kuma taki ce masa komai tana kokarin fahimtar abinda zancensa na karshe ke nufi, shirun da taji yayi yasa ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, at the same time ta kalli wa enda yake kallo a cikin restaurant din, 3 Guys ne suka shigo restaurant din gaba dayansu yan Africa, amma daya ne
an Nigeria a cikin su, guys din da ba yan Nigeria ba suka daga ma Housemate din nata hannu alamar girmamawa, and he waved back at them with smile on his face, Khaleesat ta dinga kallon daya mutumin da ya nufo su don ta ma ganesa, su sauran biyun kuma suka tafi yin abinda ya kawo su restaurant din, Mutumin na isowa kusa da table dinsu yana kallon Housemate dinta yace "Done with the power point?" Tuni kamshin turarensa ya cika wajen, Housemate dinta ya daga kai ya kallesa yace "Yau kuma har da kai za a ci abinci a nan kenan...." Yace "Not at all, i am getting some Steak for legend, meanwhile ashe kana nan" Housemate dinta yace "Yea, i came with my friend for Dinner" Khaleesat dai danna wayarta kawai take don mutumin yi yayi kamar bai san da Allah yayi ruwanta a wajen ba, ita ma ko kallon direction dinsa bata yi ba, Housemate dinta ya nuna masa bill dinsu yace "Get the bill cleared" juyawa mutumin yayi ya bar wajen yana tafiya irin ta
asaita, Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido, he was wearing a Jogger and a white Polo, ta dai ci gaba da danna wayarta, muryar Housemate dinta taji yace "That's my gee Halysaah, we share the same name with him...." Khaleesat ta daga kai without interest tace "Ohk" Yace "Sorry about his attitude, he isn't friendly, but i promise you he is good" Khaleesat tace "Likewise myself" Murmushi housemate dinta yayi sannan yayi excusing kansa ya mike ya nufi gun wanda ya kira da gee dinsa, daga inda take zaune taji mutumin na cewa "Kai kuma ina ka samo waccan yarinyar dake zaune kamar gunki bata iya gaisuwa ba, duk wani harkar raini ka iya ja ma mutane, that was how the other day da ka kawota karfe ukun dare a mota ta dinga kallon mutane kamar statue da aka dasa a gaban motar" Definitely yayi maganar ne ta yanda zata ji, Housemate dinta dake kallonsa yace "Ban gane bata iya gaisuwa ba, ba kai ka sameta a wajen ba, kayi mata magana ne kaga bata amsa maka ba?" Maimakon ya ba Housemate dinta amsar abinda yace sai taji yace "Na kai Legend gun Veterinary daxu" Taji Housemate dinta yace "Hope he is better now?" Mutumin yace "Let me get the bill cleared mu tafi gidan Mike yanxu...." Housemate dinta yace "No kayi tafiyarka zan yi dropping frnd dina first" Taji mutumin yace "Like seriously kai ko wani irresponsible being sae kace friend dinka, why are you stooping your self soo low Jay" Taji Housemate dinta yace "C'mon Ajay, come off it, this is so harsh..." Mutumin da ya kira da Ajay ya tafi ya bar sa gun a tsaye, Dawowa Housemate din nata yayi inda take, tuni ta mike tana gyara gyalenta without looking at him tace "Thanks for the dinner, kawata na kirana zan tafi gida" Housemate dinta yace "Ke kika kawo kanki da za ki koma ke kadai?" Taki kallonsa tace "Ae naga ur responsible frnds are here, so let me get going" Yace "Halysaah" ta daga kai ta kallesa, yace "Jira ni inyi clearing bill dinmu in yi dropping dinki gida" Yana fadin haka daya daga masu aiki a restaurant din ya nufosa da ladabi ya sanar masa anyi clearing bill din su, ya bi A-jay da ya fita daga Restaurant din da kallo, wa enda suka shigo tare na biye da shi a baya.

Khaleesat bata yarda ta hada ido da Housemate dinta ba har suka fito daga Restaurant din zuwa inda yayi parking motarsa, sai da ya shiga motar sannan ita ma ta shiga ta zauna tana danna wayarta, bai tada motar ba ya kalleta, speaking calmly yace "Hope you are not offended Halysaah?" Without looking at him tace "Offended at what?" Yace "I don't really know" Ta kada baki tace "Ai ni ban yi kama da someone that isn't responsible ba balle in zama Offended at what a random stranger spew out, out of his ignorance, shi dai da bashi da manner shi ne babban irresponsible being, ai da ya fada a gabana yaji abinda zan gaya masa" Housemate dinta ya bude baki yana kallonta da mamaki looking completely speechless, bai yi tunanin taji abinda Ajay din ya fada ba, bai kuma yi tunanin tana ma da baki haka ba, after few seconds yayi kasa da murya yace "Pls kiyi hakuri Halysaah, bana son wannan yasa ranki ya bace, i purposely brought you out to cheer you up and make you lively don naga kamar kina cikin damuwa, amma ba don a kara bata maki rai ba, plss ignore Ajay's attitude, wani lkcn yana da problem i think today is one of those days" Khaleesat bata sake cewa komai ba but she is trying hard not to cry, ya ci sa'a ba yana tsaye gabanta ya fadi haka ba da tsaff zata mayar masa da ba
ar magana dai dai da abinda ya gaya mata a wajen, Housemate dinta ya tada mota suka bar Restaurant din, hakuri ya dinga bata kamar shi ne yayi mata laifi har suka isa gida, direct dakinta kawai ta wuce, after like 40 mins ta fito wanka tana duba sleeping dress din da zata sa taji yayi knocking kofar dakinta, hijab din da tayi sallah ta dauka da sauri ta saka, bai bude kofar dakin ba har sai da taje ta bude tana kallonsa, yace "Sae da safe Halysaah, pls ki kwantar da hankalinki and get some rest, gobe kuma ki je school" ta sauke idonta bata ce komai ba, taji yace "Take care" Sai da ya juya ya bar wajen sannan ta daga kai ta bi sa da kallo cikin sanyin murya tace "Thank you so much, for..." Sai kuma tayi shiru, ya juya yace "For?" Ta langwabar da kai tace "The Dinner" Ya
an buda ido yace "My pleasure Halysaah" A hankali tace "But.... i don't... know, ur name" Yace "Oh really, amma ranan da na fara zuwa gidan nan ai nayi introducing kaina sai dai in kin manta, I am Ahmad Jawwad Yusuf, my frnds call me Jayy" Kallonsa Khaleesat ta dinga yi without blinking, yace "Are you okay with that?" Ta sauke idonta tace "Alright, i really appreciate you" Ya sakar mata murmushi yace "See yah tomorrow" daga haka ya bar wajen ta bi sa da ido har ya fita daga gidan gaba daya sannan ta juya a hankali ta koma dakinta ta kulle kofar.
*Make ur payment before the end of free pages, kar a ji shiru*
07087865788
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
12.....

Washegari da safe Khaleesat ta gama duk abinda zata yi a gida ta shirya ta tafi makaranta, tana zaune favourite spot dinsu ita da Safiyyah bayan sun fito daga aji, Safiyyah na facing dinta tace "Tsakaninki da Allah ina kika je jiya da yamma da naje gidan baki nan?

Ni dai nasan babu inda kike zuwa a garin nan, ba kuma frnds gare ki ba, So where did u go?" Khaleesat da idonta ke kan jotting da tayi a aji tace "To ke meye na zuwa da yamma likis, i was expecting you around 5pm not 7pm" Safiyyah ta amshi takardan hannunta tace "Ina maki tambaya kina min tambaya, ko akwai abinda kika fara boye min ne Khaleesat?" Tagumi tayi tana kallon Khaleesat din da tuhuma, sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta, dariya ta bata amma bata yi ba, kamar dai bazata ce mata komai ba sai kuma ta bude baki tace "Mun fita zuwa restaurant ne da Housemate dina" Safiyyah ta buda baki tana kallonta with surprise, can tace "Waw, really?

Housemate dinki fa kika ce?" Sai kuma tayi dariya tana gyara zama idanuwanta kamar za su fito tace "Anya Khalee babu magana a kasa kuwa?

Restaurant fa kika ce?
Chapter 24 · 0% Book details