← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 191

Sashe 162

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Lokaci daya taji gabanta yayi mugun faduwa bayan Abdul ya fado mata a rai, kaddai Housemate dinta mance kofar yayi a bude yayi bacci, tana cikin wannan tunanin zuciyarta na bugawa aka bude kofar dakin dake kallon nata, wani kara ta kurma a mugun tsorace tun ma bata ga wa zai fito daga dakin ba, Jay ya mike da sauri yana kallonta, sai kuma ya nufeta da mamaki yace "What happened Housemate?" Tana hada ido da Ajay da ya fito daga dakin shi ma yana mata kallon mamaki ta durkusa wajen ta fara kuka tana jin har lkcn zuciyarta bai dawo dai dai ba, tuni Jay ya karasa inda ta durkusa yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana kuka a hankali ta daga idanuwanta ta kallesa tace "Tsoro ya bani ai, ni na zata fa ya tafi daxu..." Ajay yaji kamar yayi ball da ita ta gangara downstairs tsabar yanda ta bashi haushi, don shi kansa sai da ihunta ya juya masa kai, Jay dai kallonta kawai yake ya kasa cewa komai ma, Ajay ya fara saukowa downstairs fuska daure yace "Tashi ki ban waje kar inyi ball dake a nan, silly gal" Turo baki tayi tana goge idonta ta basa hanya yayi tafiyarsa downstairs ya bar su a wajen, ta
an daga kai a hankali ta kalli Jay dake ta kallonta ya ma rasa me zai ce, boye fuskarta tayi da hijab din jikinta tana lekosa ta
an space din da ta bari a hankali tace "Kayi hakuri, ni wallahi ban san a gidan nan zai kwana ba shi ma, na zata ya tafi tun daxu" Murmushi yayi mata, calmly yace "It's fine Halysaah, you need something?" Ta gyada masa kai, a hankali tace "I want to take tea" Yace "Ohk, let me get you some, ki koma dakin ki" Tana murmushi cikin sanyin murya tace "Thank you" Daga haka ta juya ta koma sama zuwa dakinta, shi kuma ya sauka downstairs Ajay ya bi sa sa kallo har ya shiga kitchen, kwafa yayi ya dau remote ya kunna TV, after some minutes Jay ya gama hada mata tea ya debar mata cookies a plate sannan ya tafi sama, Ajay ya ta
e baki ganin yanda ya maida kansa Boy Boy dinta kawai, alhalin ko 5% din treatment din nan baya yi ma Hadiyah, Jay na kai mata shayin sama yayi knocking ta fito ta amsa amma ta kasa kallonsa, cikin sanyin murya tace "Nagode sosai" Kai kawai yayi mata nodding, slowly yace "Good night Halysaah" Ta juya ta koma cikin dakin ta kulle kofar.

Washegari wajen karfe tara na safe Khaleesat ta sauko downstairs bayan tayi wanka ta shirya duk da bazata je school ba ranan, kallonsa ta dinga yi yana kwance saman kujera ya rufe fuskarsa da karamin towel ya kife wayarsa a kirji, karasawa tayi har inda yake kamar tana son gano wani abu, lokaci daya ya cire towel din fuskarsa suka yi ido hudu, komawa baya tayi with shock tana
an zare ido tace "Ohh, I tot it's my Housemate" Ya mike zaune yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Kin ta
a ganinsa da wannan kayan?

Ko kuma ina wasa dake ne?" Ta
an langwabar da kai tace "To ai dai bazan san ba shi bane, since you are having the same height and complexion with him" Yace "I could slap you idan baki fita a gabana ba Malama" Ta wani ta
e baki ta nufi kitchen, irish ta diba ta fere wanda zata yi using, tana yanke yanken veggies da zata soya kwai da shi a ranta tana mamakin Why Ajay is in the house instead of her Housemate, kawai daga jiya zuwa yau ya mata masifa sau biyu, turo baki tayi ta ajiye wukan sai a sannan ta zaro ido ta dau irish dinta ta zuba a man gyada da ta dora don har ta manta da man gyadan, rufe baki tayi da hannunta jin fire alarm din kitchen din ya dau ruri, gaba daya ta mance da shi, don in dai zata yi soye soye wani lokacin lullubesa take da Shower cap dinta ta yanda bazai yi detecting komai ba balle ya fara tona mata asiri yana ruri, ta juya ta fito daga kitchen din tana kallon Ajay kamar munafuka tace "Don Allah ka zo ka min stopping din alarm din ya dena" Ajay yace "A'a ki dai kona masu gida ni ina ruwana, kin zata a Nigeria kike ba" Ta marairaice tace "Don Allah mana, kaga it's very loud fa" Ko kallon inda take bai sake yi ba, ta juya ta koma kitchen din tana kallon inda smoke alarm din yake, ita bata ma san ya ake kashewa yayi shiru ba, ta rage abun girkin zata sake komawa parlor ta masa magana ta kusa cin karo da shi zai shigo kitchen din, komawa gefe tayi tana kallonsa har yayi silencing smoke alarm din sannan ya fita daga kitchen din, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da girkin da take yi, bayan ta gama ta fito daga kitchen din dama iya wanda zata ci da Housemate dinta kawai tayi, tana kallon Ajay tace "Housemate dina fa?" Bayansa ya nuna mata alamar gashi ya goya shi, juyawa tayi ta wuce sama ya bi ta da wani kallo, tana shiga dakinta ta dau wayarta ta zauna gefen gado tayi dialing number Housemate dinta, yana fara ringing ya daga, in his calm voice yace "Good morning Halysaah" Ta
an yi murmushi kamar yana ganinta ta fara wasa da gefen duvet dinta a hankali tace "Good morning" Yace "How was your night?" Tace "Alhamdulillah, naga baka nan" Yace "Yea i went to get something, i will come over later" Tace "I made some breakfast for you" Yace "Really" Tayi shiru bata ce komai ba don har ranta ta so ya ci breakfast din, yace "Ohk give me 30 mins zan dawo sai in ci" Tayi murmushi har sai da dimples dinta ya lotsa tace "Toh Allah ya kawo ka lafiya" Katse wayar tayi sannan ta mike ta fita daga dakin ta koma downstairs, bata ko kalli Ajay ba tayi wucewarta kitchen ta ajiye ma Housemate dinta nasa breakfast din ta dau nata ta fito, hada ido suka yi ta sauke idonta har zata wuce sai kuma ta
an kallesa tace "There is everything available in the kitchen, idan kana son kayi making breakfast for ur self" Ya juya ya kalleta yace "Kee, ki shiga hankalin ki, ni ba Jay bane" ita dai tayi tafiyarta sama bata ce masa komai ba.
Chapter 162 · 0% Book details