Sashe 59
Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
HALYSAAH 29
Sai da Khaleesat taga sun bar unguwansu gaba daya sannan reality yayi hitting dinta ta kara fahimtar me Abdul ke da niyyar yi, she felt so helpless at this point, ta jinginar da kanta jikin kujeran motar hawaye masu zafi na sauka idonta ta kasa cewa komai, shi dai driving dinsa kawai yake bai ko kalleta ba, ganin tafiya kawai yake ta juya tana son ko hakuri ne ta bude baki ta basa amma tsoron kar ya sake marinta yasa ta kasa don babu alamar rahama a fuskarsa, ta rufe fuskarta da hijab din jikinta hawaye wasu na bin wani a idonta, tsabar tashin hankali da firgicin da ta shiga a wannan moment din kilan da za a duba jininta za a ga ya hau, bayan tafiyar kusan minti talatin taji ya tsaya cak, da sauri ta sauke Hijab dinta zuciyarta na bugawa tana kalle kallen inda suke, taga dai dai wani eatry ya tsaya, ita dai kallonsa take har sannan hawaye bai daina sauka idonta ba, ya sauka daga motar without looking at her ya kulle, ta bi sa da kallo har taga ya shiga gidan cin abincin, ta fashe da matsanancin kuka tana waige waigen wajen cikin tashin hankali, babban wajen cin abinci ne sosai, ga mutane suna ta kai kawo a gurin, glass din motar ta fara bubbugawa da hannunta amma taga nobody is noticing her, ta fara kalle kallen cikin motar taga bunch of keys da ya ajiye ta dauka da sauri ta fara bubbuga glass din motar da shi da karfi, hakan ya ja attention din wani mutumi da ya fito daga cikin eatry din zai shiga motarsa dake kusa da inda Abdul yayi parking, ita dai bata fasa bubbuga glass din ba tana kuka sosai tana cewa don girman Allah ya taimaketa, da alama baya ganin cikin motar saboda tinted glass din, ya zaga ta gaban motar yana duba ciki, ta dinga kuka tana cewa don Allah ya taimaketa, ba ta damu ko yana jin abinda take cewa ba ko baya ji ita dai kawai ya taimaketa, mutumin ya tafi ya taho da wani security dake wajen, dai dai nan wani soja da ya fito eatry din zai shiga motarsa shi ma ya karasa gun motar kan kace me attention din jama'an dake gurin gaba daya ya dawo kan motar Abdul, Khaleesat bata fasa kukan da take ba duk da ta samu relieve ganin mutanen da suka zagaye motar wasu na kokarin mata magana suna haska cikin motar da fitila, mutane duk suka tsaya aka yi cirko cirko a kusa da motar, ita dai kuka me sauti kawai take kamar ranta zai fita, babu wanda bazai ce sato ta aka yi a lkcn ba, bayan wasu mintuna Abdul ya fito daga Eatry din rike da abinda ya siyo, yana zuwa inda yayi parking yaga jama'a jikin motar ya tsaya yana kallon ikon Allah, Security din dake tsaye wajen don yaga sanda Abdul yayi parking ya shiga eatry din, ya kalli sojan dake tsaye yace "Ga me motar nan ya fito" Da wani expression Abdul yace "What happened?" Sojan yace "Bude motar ta sauko Malam" Abdul yace "Ban gane in bude mota ta sauko ba, matata ce a ciki" Sojan yace "Ai bamu mu sa ka ba, mota kawai zaka bude ta sauko, ba wani abun tashin hankali bane ai" Nan jama'an wajen suka dinga cewa ya bude motar suna hayaniya, Abdul ya bude motarsa da Key din hannunsa daga inda yake tsaye, Khaleesat na jin alamar yayi unlocking din motar ta bude ta sauko da sauri tana kuka, Sojan ne ya fara mata magana yana nuna mata Abdul yace "Waye wannan?" Ta fashe da matsanancin kuka muryarta na rawa tace "Ni ban san shi ba" Kallonta Abdul ya dinga yi da mamaki babu ko kiftawa, hayaniya sosai mutanen wajen suka hau yi sojan na kokarin calming dinsu, Sai kuma ya sake kallon Khaleesat yace "Baki san shi ba?
To garin yaya kika shiga motarsa?" Tana shessheka tace "Kawai dauko ni yayi a unguwanmu wallahi, ni ban san shi ba" Tuni matasa yan zaman kashe wandon dake wajen suka fusata suka zagaye Abdul suna dure duren ashar suna kokarin fara mazgarsa, gaban Eatry din ya cika da jama'a an zo kallo wasu har sun fara video, with the intervention of the soldier and the security men da wasu responsible mutanen dake wajen aka saka Abdul cikin motar Sojan don tsaf sun kula matasan za su yi aika aika ne a wajen, wannan opportunity din Khaleesat tayi using cikin dubara ta sulale cikin jama'ar wajen without letting anyone to notice her don gaba daya hankalin mutane ya koma kan Abdul a wajen, a haka ta samu ta tsallaka titi ko waigawa bata yi ta afka wani layi, nan ma tayi ta tafiya da sauri da sauri gabanta na faduwa, duk inda taga alamar hanya ce haka ta dinga bi ba tare da tasan inda zata ba, tafiyar kusan minti arba'in tayi a kafa hawaye na zuba idonta, ko sanin unguwan da take bata yi ba, daga karshe tsabar yanda ciwon kai ya matsa mata ga jiri dake ta kwasarta ya sa ta samu gaban wani gida ta zauna ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, tana ta zaune for almost 10 mins wani mutumi dake
an nesa da ita yana zaune kofar gidansu ya mike ya nufota, don tun da ta shigo layin ta zauna ya ganta, sallama yayi mata ta dago kanta a tsorace, yace "Baiwar Allah lafiya dai ko?" Ta girgiza masa kai da kyar tana goge idonta tace "Bana jin dadi ne, kuma gida zan je" Yace "Ikon Allah, to ina ne gidan naku?" Without second thought tace "Hotoro" Yace "Hotoro?
To bari in samo maki adaidaita sahu sai ya kai ki" Ta gyada masa kai cikin rawan murya tace "Nagode" Ya juya ya bar wajen, bayan wani minti goman sai gashi ya dawo cikin adaidaita sahu bayan yaje har bakin titi ya samo mata adaidaita sahun, ya sauko daga ciki yana kallonta yace "Toh ga adaidaita sahun na samo maki Hajiya" Tace "Nagode" Ta mike da kyar ta dafa adaidata sahun sannan ta shiga ciki, mutumin ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Ki saka min lambarki sai inji ko kin isa gida lafiya" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Matar aure ce" Mutumin yace "Ohh, na gane to, Allah ya tsare Hajiya, Allah ya baki lafiya, na biya sa kudinsa ba sai kin basa ba" Ta gyada masa kai tace "Nagode, Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen ya Allah" a haka mai adaidaita sahun ya bar layin.
Har suka isa hotoro Khaleesat bata san sun iso ba, sai da me adaidaita sahu ya ankarar da ita, dai dai kofar gidan Gaje ta sa ya tsaya, ta sauka tayi masa godiya ta shige cikin gidan, nan gaban Gaje dake zaune tsakar gida ta zuba tana kuka kamar zata shide, Gaje tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Khaleesah?
Me ya faru? daga ina kike haka?" Da kyar Gaje ta lallashi Khaleesat tayi shiru bayan lokaci me tsayi, sannan ta fara gaya mata abinda ya faru, Gaje ta saki salati a rikice tace "Mun shiga uku mun lalace, yanzu gidan yan sanda suka tafi da Awdul din kenan?" Cikin kuka Khaleesat tace "Ban sani ba nima" Gaje tace "To kuwa zaman gidan nan bai kama ki ba Khaleesah, yasan bayan gidanku baki da inda zaki taho a kano da ya wuce gidana ko gidan Nenne, wannan fa ba karamin kess bane, Awdul na zuwa nan ya ganki sai ya zata da hadin bakina kika yi abinda kika yi, ya sa yan sanda su kulleni in shiga uku" Cikin kuka Khaleesat tace "Toh ya zanyi yanzu Baaba Gaje?" Gaje ta mike ta figi gyalenta a igiya tace "Ta shi mu je" Jikin Khaleesat na rawa ta mike ta bi Gaje suka fita daga gidan, da kafa suka tafi gidan kawar Aunty Farida da ake ce ma Maman Fu'ad, bayan sun shiga gidan Gaje tayi mata bayanin duk abinda ke faruwa, Maman Fu'ad tunda ta rike ha
a har gaje ta gama bada labari bata iya tace komai ba, Gaje tace "Don haka ki rufa mana asiri Sadiyah ta kwana gidanki zuwa gobe a ga abinda hali zai yi" Maman Fu'ad ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat, gwalo ido tayi ganin jinin da ya kwanta idonta tace "Me ya samu idonki?" A hankali Khaleesat tace "Marina yayi" Maman Fu'ad ta saki salati tace "Mari??
Har sai da jini ya kwanta maki a ido? ga lebenki ma a fashe?
A'a gaskiya tsinanne ne wannan mutumi" Gaje ta rike ha
a tana kallon idon Khaleesat sai kuma ta fashe da kuka tace "Yanzu wannan har mijin aure ne in ba don Ali ya cuceki ba, dubi fa tafin hannunsa a fuskarta?" Maman Fu'ad tace "Da kyar ma in baya shaye shaye wannan, gaskiya duk yanda za ayi a raba auren nan domin ceto yarinyar nan daga halaka, yanxun nan zan kira farida kuwa" Gaje ta rufe bakinta da sauri tace "Ki kirata kice mata me?
Rufa mana asiri ba wanda yasan tana nan, ina me tabbatar maki kilan yanzu an tafi da Awdul din police station, kinga ai dole ya kai yan sandan gidansu Khaleesat don wanke kansa su tabbatar matarsa ce, in kuma yayi haka ai za a bazama nemanta ne a gari" Maman Fu'ad tace "Ba komai Gaje, ki tafi kawai ki kyaleta a nan kar su je can gidan naki baki nan" Gaje ta mike da sauri tace "Don Allah ki bata ruwan zafi in kina da shi tayi wanka" Maman Fu'ad tace "Kar ki ji komai Gaje" A haka Gaje ta bar gidan, yanda Khaleesat taga daren jiya wannan daren ma haka ta gansa, ga ciwon kai, ga ciwon ido, ga zazzabi duk ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, she don't even know who to speak to at this point.