← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 191

Sashe 63

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar Inteesar taji a hankali tace "You are Beautiful Khaleesat" Khaleesat ta
an kalleta sai kuma ta mayar mata da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace "Sosai fa" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "And you too Inteesar" Inteesar tayi dariya tace "A'a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba" Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace "Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa" Inteesar tace "Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a lagos ne in kin je?" Khaleesat tace "Zan
an yi kwana biyu a can in sha Allah" Inteesar tace "Akwai sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will meet with you there" Murmushi Khaleesat tayi tace "Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya" Inteesar ta tashi ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado tace "You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later" Khaleesat tace "Alright, thank you so much" Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo dakin, Inteesar ta wara ido tace "Waow is all that ur hair Khaleesat?" Khaleesat dai ta mata murmushin karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace "Bari in baki Hair net" Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace "Nagode sosai" Washegari karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau, Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar's care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge.

Karfe sha biyu saura suka sauka garin Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Ina wayar da na baki?" Jakar hannunta ta nuna masa tace "Yana ciki, na sa silent ne" Driver seat ya bude ya shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba, ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata
aso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta, bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat, yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace "Ya ake ciki?" Daga daya bangaren mutumin yace "Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja yanxu haka" AJ yayi shiru kafin yace "Ohk, i will get back to you nagode" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi
asa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace "Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da apartment uku self contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa, ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace "Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai" AJ ya daga kansa ya kalleta yace "Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?" Aunty Farida tace "Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da barina wancan Unguwan na dawo nan" Ajay dai yayi shiru idonsa a kasa, Aunty Farida tace "Kuma ba unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo" Ajay yace "Toh shikenan, jikinta da zafi ne?" Aunty Farida tace "Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta min magunguna in siyo mata" Ajay yace "Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip ayi mata karin ruwa" Aunty Farida tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid" Ajay ya
an yi murmushi yace "Bari in je in dawo dai" A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya harhado mata magunguna da drip da allurai.

Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar kafafuwanta, cikin fada take cewa "Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata?

Er talakawa?
Chapter 63 · 0% Book details