← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 191

Sashe 78

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ni wallahi ban yarda wa ennan samarin basu san inda Khaleesat take ba, kina fa ganinsu kin ga 'ya yan masu kudi, dubi suturan da suka sa wa, ji motocinsu, sannan kalli fatarsu kalan ta yan hutu, in fa muka yi sake Shatu bakin ciki ne zai kashe mu a gidan nan muna ji muna gani" Mama Shatu tace "Ke ma dai wallahi kin fiye gaggawa, sai kace kin manta me Malamin yace mana, duka duka ba yau muka kai masa kudin ba, to mu zuba ido ya fara aiki mana tukun" Mama Zubaida tace "Duk da haka dai gwara mu ma mu dinga yin namu ta bayan fage Shatu, kada mu sakankance mu bar malami da aiki shi kadai, ya kamata tun wuri mu san yanda za mu yi mu ankarar da Abdul abinda ke faruwa a gidan nan, don gaskiya na sha jinin jikina da wa ennan zaratan samarin, ke ki ga tulin kudin da suka ba Islam, sannan kalli uban kayan abincin da suka jibge jiya daga karshe don walakanci aka biyo mu da kwano uku uku da taliya bibbiyu da man gyada da manja, sai maggi leda bibbiyu ga mayunwata, ke kiji wai yau Zahra'u ce da tsam mana kayan abincin da aka jibge mata, bayan haka Allah kadai yasan nawa suka bata a daki tunda ba gaya mana zata yi ba, ga Nenne ma a gaban mu aka bata rafar kudi yan dubu dubu, anya bamu shiga uku ba Shatu?

Ni fa jikina yayi sanyi hankalina ya tashi, meye hadin su da Khaleesat din da har suke wannan hidima haka a kanta, mu ga 'ya yanmu a zube har yau babu mataya sai talla suke, ni fa wallahi ko tsirara zan yi yawo gwara inyi da dai Zahra'u da zuri'arta su ji dadi a duniya" Mama Shatu tace "Yanxu dai Gwaska za mu samu ya raka mu gidan su Abdul din tunda yace yasan gidan uban sa, nasan Abdul din zai taka ma yan iskan burki har ma ya bamu makudan kudi fallasa asirin abinda ke faruwa da mu ka yi" Mama Zubaida tace "Atoh dai tun wuri my gaya masa abinda ke faruwa, zuba ido ba namu bane wallahi, amma sai dai jibi kenan za mu je gidansu Abdul din don Gwaska ya tafi dambatta daxu uwarsa ke gaya min yaje kai kaya can" Mama Shatu tace "Ai jibin kamar gobe ne, kin ga gobe dama mu gama girkin mu da wuri mu tafi inda wannan matar ta mana kwatance daxu a gidan Malam" The next day wajen karfe biyar da rabi na yamma Sha'awa tayi sallama bakin kofar dakin Umma dake yi ma yan biyun ta gyaran gashi, babu kowa gidan don duk yan matan gidan basu dawo talla ba, kananun yaran kuma sun tafi gantali, tun Sha'awa bata shigo dakin Umma ba take cewa "Umma yanxu Ladingo ke sanar min an sako Gaje, wai daxu taje unguwan taga ana ta shiga gidan yi mata jaje" Umma ta sake gashin Noor ta mike da sauri tace "Da gaske Sha'awa?" Sha'awa tace "Wallahi kuwa Ladingo bazata min karya ba Umma, tace Gaje dai ta dawo gida ga yan unguwa na ta tururuwan shiga yi mata jaje tun daxu" Umma ta jawo Hijab dinta tace "To bari in je gidan Allah ya sa da gaske ne dai" Sha'awa tace "Da ina da kudin mota ai da mun je tare Umma, kusan kwanan ta biyar fa a kulle, don ma akwai kanwarta da zata kula da jikokinta tunda uwarsu na can Libiya ta tafi aikatau, ubansu kuma yayi watsi da su, banda haka da yaya makomar jikokin nan nata fisabilillahi?" Umma bata tanka ta ba ta gama saka hijab dinta ta daura nikab ta dau purse zata fita, Noor da Islam suka marairaice wai za su bi ta, ganin in ta tafi su kadai zata bari a gida yasa tace su saka hijab gaba daya, haka nan duk suka saka Hijab suka fita daga dakin Umma na biye da su, kusan kullum sai Umma taje gidan Gaje sau biyu ta duba ko ta dawo amma sai taga akasin haka sai dai ta samu kanwarta Iya a gidan, jiki a sanyaye take juyawa ta koma gida don Iya na ganinta take fara masifar ita ta saka er uwarta a uku, Umma zata fita gidan tare da yan biyunta sai ga su Mama Shatu da Mama Zubaida sun shigo wujiga wujiga da su, kana ganin fuskokinsu kasan a gajiye suke likis, ga wuyan hijabinsu duk yayi jagab da zufa, kafafuwarsu kuwa kamar wa enda suka dawo daga gona, Umma dai tayi masu sannu da zuwa kawai ta fita daga gidan su Islam na biye da ita, ai ko tana isa gidan Gaje taga da gaske an sako Gaje, Gaje na ganin Umma tayi kamar bata ta
a saninta ba a duniya, yanda take amsa gaisuwa da jajen masu shigo mata haka ta amsa ma Umma kamar ranan ta fara ganinta, ita dai Umma na zaune tayi shiru ta ma rasa me zata ce, su Islam na zaune gefenta, Gaje bata sake kallon direction dinta da yaranta ba, duk wanda ya shigo haka take sanar masa yanda Maman Fu'ad ta ci amanarta tace ma yan sanda ita bata ta
a ganinta ba ma balle wata Khaleesat, In tayi bayanin sai ta rushe da kuka tace "Ban ta
a tunanin Sadiyah zata min butulci haka ba duk alakar da ke tsakanin mu wai bata ta
a gani ba, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutumin yau kawai, duk kyautata ma yarinyar nan da nake amma ta barni ni kadai raina a cikin matsalar da na tsoma kaina" Ita dai Umma tayi tagumi tana sauraron duk abinda Gaje ke cewa.
_Thanks sooo much for the birthday wishes everyone, Allah ya saka da alkhairi_
*As usual yau akwai discount na littafin Halysaah daga yanxu har zuwa gobe karfe goma na safe, the book will be 300 naira, via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence through 07087865788*
Thank you sooo much everyone.
Chapter 78 · 0% Book details