← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 191

Sashe 131

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin san fa bazan yi hakan da gan gan ba, don Allah kiyi hakuri, wallahi yayi escaping mind dina ne situation din dake at hand, ko fada Housemate din naki yayi maki ne?" Khaleesat ta girgiza kai trying to sound ok tace "A'a ni fa kaina ne ke min ciwo amma ba wani abu ba, gida ma nake son zan tafi yanxu" Shiru Safiyyah tayi trying to be sure of wanda take hangowa nesa da inda suke zaune, can ta kalli Khaleesat....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
S-BORNO INCENSE AND MORE.

Muna Saida turarukan wuta masu Kamshi dakuma kama gida, ba iya su kadai muka tsaya ba, muna saida kayyakin gyaran jiki wanda babu ruwanki da zuwa gyaran jiki zaki gyara jikin ki gida cikin sauk
i, idan kina son turaren kabbasa mai kama jiki da Kaya Hajiya ta kwantar da hankalin ki, ba Kaya kawai zai kama ba har kujerar da kika zauna sai ta kama Kamshi da yardar Allah, turarukanmu sune kamar haka.

FARCE
HAWEE
GABGAB
DORUT AFTER PERIOD
KAJIJI
Halut oud
White oud Nawwar, Sandal bange
Dollar
Wardrobe balls
SANDAL BALLS
COTTON INCENSE
HAIR INCENSE
CURTAINS INCENSE
BATH MIST
MOPPING MIST
MATAN MAIDUGURI
CHADIAN KULECCAM
SUDANESE KULECCAM
TOILET SPRAY
ROOM SPRAY.

BANGAREN GYARAN JIKI MUNADA READY TO USE DILKE, HALAWA, Dilka Soap.

MUNA BADA SAYAN D
aya ko sari kan farashi mai rahusa, ina mai tabbatar miki babuke babu nadama sayan kayanmu, gidan ki yayi Kamshi, labulayenki suyi kanshi, hatta bangon gidan ki sai yayi kanshi, muna zuwa ko wani gari
don yin gyaran jikin Amarya.
08093772168
Karku manta munada mayukan gashi masu Kara tsawon gashi zasu gyara miki gashi yayi laushi yayi tsantsi,Sannan yayi tsawo in two months.

Muna tura kayan mu duk inda mutum yake, location dinmu Maiduguri ne. 08093772168
HALYSAAH 62
Sau daya Khaleesat ta kallesa ta dauke kai bayan tayi convincing kanta ba wajensu yake tahowa ba, Safiyyah tayi kasa da murya tace "Ni ban ma ta
a ganinsa a school din nan ba sai yau, gwara Housemate dinki shi dama ya saba zuwa ya same mu a nan sanda muke Exam, he is coming toward us fa" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba amma can kasan ranta ita ma tayi mugun mamakin ganinsa a department dinsu, how did he even know spot din da suke zama da Safiyyah, sai kawai tayi assuming hanya ce ta biyo da shi ta nan din, har ya iso inda suke zaune Khaleesat bata daga kai ba but she is surprise, Safiyyah na kallonsa tana murmushi tace "Good afternoon Ya Junaid" Ba tare da ya kalleta ba yana kallon different direction yace "Evening, can you excuse us...

I want to have a word with ur Coursemate" Safiyyah dai bata fasa kallonsa ba tana gyada kai tace "Sure, why not...." Sai kuma ta dau jakanta ta mike tana kallon Khaleesat tace "Zan je wajensu Nora, if you are looking for me ina can..." Khaleesat ta gyada mata kai kawai, daga haka Safiyyah ta bar wajen, ita dai Khaleesat mamaki ma yasa ta kasa kallon Ajay dake tsaye kanta, he wants to have a word with her?

To me zai ce mata da zai biyota har department din su, duk da under same faculty suke amma ko da wasa bata ta
a haduwa da shi a school ba in ba few days ago ba da suka shigo da Jay, ta kalli wayar da yake mika mata fuskarsa babu yabo babu fallasa, she was surprise, why is he giving her his phone? bata amshi wayar ba ta daga kai ta kallesa a karo na farko, ganin yanda ya daure fuska ya sa ta mika hannu ta amshi wayar tana kallon screen din, sosai gabanta ya fadi ganin hoton da suka yi da Aymaan jiya a get together, ta dinga kallon hoton babu ko kiftawa, gashi ba hoto daya ba ba kuma biyu ba, can ta kalli a ina yaga hoton sai taga a Instagram ne, bata san sanda ta gyara zama ba zuciyarta na bugawa sosai, Instagram kuma?

Me ya kai hoton Instagram? ta shiga uku, ita da ko a screen din wayarta bata ta
a saka hotonta ba balle aje ga WhatsApp ko kuma facebook uwa uba Instagram, gaba daya hankalinta yayi mugun tashi ta kasa cewa komai, da kyar ta daga kai ta kallesa ta ga wani irin kallo yake mata, ta sauke idonta gabanta na ci gaba da faduwa ta kasa cewa komai, fixge wayarsa yayi daga hannunta yace "So you came back fully prepared to party in Baltimore Right?

You came back to mingle with jobless guys following them to party up and down, Har kin ma mance abinda ya same ki, but wait...

Baki ta
a zuwa islamiyya bane ko kuma kin je kin yi skipping classes?

Ko kuma bayan mijin da kika ce a kyaleki kina son zama da shi ya sake ki baki zauna kin tambayi makusantan ki what next ba?

Kawai saboda kina jin kanki on a different level yanxu shi yasa kika kama hanya kika tafi cikin kattin banza masu shaye shaye da sunan get together, har ki tsaya gefen wannan crook guy din ayi maku hoto kina dariya" Khaleesat ta kasa daurewa ta fashe da kukan da tun safe take son yi bata samu kwakkwaran reason din yin sa ba, shiru yayi yana kallonta irin kallon mamakin nan, after a minute ya zauna inda Safiyyah ta tashi amma bai ce mata komai ba, ita kuma bata fasa kukan da take ba kamar an aiko ta, tayi me isarta don kanta ta hakura ta fara goge idonta tana sauke ajiyar zuciya, sai a sannan ya kalleta yace "Ohk i understand, kin dawo America ne kiyi abinda ranki yake so ba kuma kya bukatar wani yace zai yi questioning din ki ko kuma yayi correcting din ki" Wani sabon kukan ta fara yi kamar ana tunzurata, ya mike trying to control himself yace "Get up" ganin taki tashi ya hade rai yace "Baza ki tashi ba?" A hankali ta mike tana ci gaba da goge hawayen dake zuba idonta tana shesshekan kuka, babu yabo babu fallasa yace "Mu je" Bata masa musu ba ta fara bin sa har sannan tana goge hawayen idonta, after almost 10 minutes walk suka iso inda yayi parking motarsa, yana bude motar ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Ni ban ce ma Safiyyah zan tafi ba" Ya mata wani irin kallo yace "Baza ki ce mata ba, get in the car" Bata ce komai ba ta zaga ta bude gaban motar ta shiga, bata ta
a shiga motarsa a America ba sai ranan, har suka isa Apartment dinta babu abinda yace mata, bayan yayi parking without looking at her yace "Leave my car" Sauke idonta tayi, ta bude motar a hankali ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Don Allah tunda ka san sa kayi masa magana ya goge hotona a Instagram" Ya jefa mata wani kallo yace "Zan gaura maki mari, ni na hada ku nayi maku hoton da zan ce masa ya goge?" Daga haka yayi Reverse yayi zoom off daga Neighborhood din, wasu sabbin hawaye suka cika idonta ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofar apartment dinta ta bude ta shiga, zaunawa tayi a parlor ta fara tunanin to ko shi ma Housemate dinta ya ga hoton ne a Instagram bayan status din Safiyyah, bata ta
a jin haushin Safiyyah irin yau ba, Allah kadai yasan mutane nawa ne suka ga hoton nan daga jiya zuwa yau, ta goge idonta ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta fara kiran Safiyyah, yana fara ring Safiyyah ta daga tace "Ya tafi ne in fito?" Trying to be calm Khaleesat tace "Kin ga Safiyyah kije kiyi ma wannan mutumin magana ya cire hotona a Instagram, who does that?

Ta yaya daga hoto zai je yayi posting a Instagram kamar mun san juna from anywhere da shi?

Meye hadina da shi da zai min haka?

Har wani dogon magana muka yi da shi da har zai dau hotona tare da shi yayi posting a Instagram dinsa?" Muryarta na rawa ta kare maganar, Safiyyah tace "Innalillahi, Instagram yayi posting hotunan?

Kinsan ni ba wani damuwa da IG nayi ba, kuma fa Aymaan ban ta
a ganin yayi posting mace a Instagram ba, sai gashi yayi posting na ki, amma how did you know his Handle da har kika ga yayi posting din ku?" A fusace Khaleesat tace "Ina ruwana da wani handle dinsa, kawai daga haduwa ko maganar minti daya ban yi da mutum ba ya kama hotona yayi posting duk duniya su gani, is he even okay?

Ko ba shi da hankali ne?

To wallahi ki je kiyi masa magana ya goge min hotona" Safiyyah tace "Ni ma dai nayi mamaki gaskiya, wallahi ban ta
a ganin yayi posting mace ba sai gashi yayi posting din ki, kar dai shi yasa Ajay ya zo wajen ki yau?

Don definitely za su iya sanin juna kilan ma suna following juna, kinsan akwai association na Nigeria student a makarantar mu dole ma za su sun san juna,
an Deputy governor ne fa Aymaan, he is also popular on IG" Takaici ya sa Khaleesat ta katse kiran ta jefar da wayarta kan kujera, wani mugun haushin Aymaan
da Safiyyah ta dinga ji a ranta, da tana da numbersa babu abinda zai hanata kiransa ta gaggaya masa magana, ko an gaya masa ita irin wa ennan matan ne da har zai yi posting din ta duniya su gani, Abdul ne ya fado mata, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, don babu uban da ya kai sa zama active a Instagram gashi da uban followers, wa ma ya sani ko yasan Aymaan din, sosai taji hankalinta ya tashi ta jinginar da kanta da kujera wasu hawayen na zuba idonta, bata ta
a jin Safiyyah bata kyauta mata irin yau ba, da kyar ta mike ta dau jakarta da waya ta wuce sama.
Chapter 131 · 0% Book details