← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 191

Sashe 187

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai in shi ne bashi da lafiya, ni kin ji alamar bani da lafiya?" Khaleesat ta
an ta
e baki tace "Toh ai shikenan, bye...." Zata katse wayar, Calmly taji yace "Kar ki kashe min waya Malama"
*Halysaah is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa bello Jiddah* Ur evidence via 0708786578
https://chat.whatsapp.com/DtKRIBCkfHoGuMzWcuq87V?mode=ac_t
HALYSAAH 86
Khaleesat tayi shiru jin abinda yace, can ta tallabi chin dinta tana jiran jin maganar da zai yi da yace kar ta kashe masa waya, ganin shima shirun yayi babu kuma alamar zai ce komai ta langwabe kai tace "Karar min da katin za ka yi?" Taji bai tanka ta ba, after some seconds ta turo baki tace "Sai da safe" A nan taji yace "Ke..." Dariya ya bata, amma ta hade rai tace "Ban gane ba, kawai kira fa nayi ince maka ya jiki nothing more" Kallon screen din wayarta tayi jin shigowar sako taga katin dubu ashirin ya tura mata, zaro ido tayi ta bude baki tana kallon amount din, bata san sanda tayi dariya ba tace "Ni nace maka bani da kati da zaka turo min har na 20k?" Taji bai tanka ta ba, tace "Hummm" A hankali tace "Tohm Nagode Allah ya saka da alkhairi, thank you soo much" He was still not saying anything, ta langwabe kai tace "Zan iya kashewa yanxu?" Sai a sannan taji yace "Ai sai katin nan ya kare" Bata san sanda tayi dariya ba sosai tace "Wanda ka turo min yanxu ko kuma katin da nake da shi kake nufi" Yace "I don't know for you" Tace "To ai ko nawa ma zai iya yin 3 hours bai kare ba, wanda ka turo min kuma ban san awanni nawa zai yi ba" Jin bai ce komai ba ta ajiye wayar ta sauka daga saman gadon ta tafi gun boxes dinta ta bude zata saka kayanta cikin wardrobe, sai kuma ta koma ta dauko wayar taga he is still on the line, ta langwabe kai a hankali tace "Ni fa aiki zan yi wallahi, should I cut the call?" Taji yace "Ke" Ta
e baki tayi ta ajiye wayar ta koma ta ci gaba da abinda take yi, ta dau lokaci me tsayi tana ta gyara kayanta bata sake komawa ta duba wayar ba, aka bude kofar dakin Aunty Farida ta shigo rai bace zata fara mata mitar abinda Nenne tayi yanxu a parlor, Khaleesat tayi saurin yi mata alamar tayi shiru tana nuna mata wayarta dake kan gado, Aunty Farida ta juya ta kalli wayar, Khaleesat ta karasa saman gadon ta dauko wayar tana kallon screen din taga bai fa katse ba har lokacin, mamaki hakan ya bata, da gaske katin yake don karar wa kenan, ta kai wayar kunne tace "Hello, ga Aunty Farida nan za ku gaisa" Taji yace "Ohk" mika ma Aunty Farida wayar tayi ta koma ta ci gaba da abinda take yi, sun kusa 10 mins suna magana da Aunty Farida har abun ya bata mamaki ashe yana bude baki yayi magana me tsawo haka dai, daga karshe suka yi sallama da Aunty Farida ta mika ma Khaleesat wayar ta fita daga dakin, Khaleesat ta kai wayar kunne tace "Sai da safe" Yace "Ai ban
ona katina ba Malama" Ta hade rai tace "Toh sai cajina ya kare bayan ba wani magana muke yi ba" Yace "Na hanaki magana?" Kallon screen din wayar tayi taga minti nawa aka dauka all this while, zaro ido tayi ganin miss calls din Jay a saman screen din wayar, da sauri tace "Kaga Housemate dina yana ta kira ban sani ba kuma" Yace "Ni na hanaki sani?" Zata yi magana taji ya katse wayar, ajiyar zuciya ta sauke ta zauna gefen gado tayi dialing number Housemate, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai dauka ba, ajiye wayar tayi hoping zai yi returning call dinta amma har bayan minti goma taga bai kira ba, ta kalli agogo dake nuna karfe sha daya dai dai, sake kiransa tayi bai daga ba, Khaleesat ta dauko kayan baccinta ta saka don tayi wanka tun wajen karfe takwas da rabi, Hijab ta daura a kai ta fita zata je tayi ma Umma sai da safe, ba a dau lokaci ba ta dawo daki ta kwanta tana duba wayarta hoping Jay ya kira amma taga akasin haka, sosai taji ta damu, to ko dai yayi bacci ne, gashi sanda ya kira ji zai yi she is on another call, sai yayi tunanin tana ganin kiran nasa bata
aga ba, sosai jikinta yayi sanyi ta rasa yanda zata yi, Aunty Farida ce ta shigo dakin tace "Har kin kwanta ne Khaleesah" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, Aunty Farida ta zauna gefen gadon tana kallonta tace "Yana kiran ki ne dama Junaid" Khaleesat tace "A'a ni na kirasa bashi da lafiya nayi masa ya jiki, Housemate dina ya gaya min he is sick" Da damuwa Aunty Farida tace "Ayyah, to Allah ya basa lafiya, ai ban sani ba da na tambayesa ya jikin" Khaleesat dai bata ce komai ba, Nan Aunty Farida ta hau bata labarin abinda Nenne tayi daxu, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don abinda ya tsaya mata a rai daban, har daga karshe aunty farida tayi mata sai da safe ta fita wajen karfe sha biyu da minti
aya, Khaleesat ta jawo wayarta a sanyaye ta kunna data ta bude WhatsApp, dai dai sanda Jay yayi updating Status with Ajay's picture, wishing him a Happy Birthday, tayi masa reply tace "Baka ga kirana ba?" After some minutes ya maido mata sako
yace "Just woke up now" Kasa rubuta masa komai tayi jin abinda yace, after some minutes tace "Toh shikenan" Ya maido mata da reply din "Good night" Bata sake ce masa komai ba ta kashe data tayi kwanciyarta zuciyarta babu dadi.

Da asuba bayan Jay ya dawo masallaci ya nufi part din Ajay don ko masallacin ma bai je ba, kwance ya samesa har ya koma bacci bayan yayi sallan sa a daki, Jay ya kalli drugs din da ke ajiye kan beside drawer da ruwan gora, ya karasa kusa da shi ya kai hannu forehead dinsa to feel his temperature, yaji his temperature is normal, although sau uku yana shigowa part din nasa cikin dare to check up on him, a zuwansa na karshe ne ma yaga Mai martaba a dakin shi ma, bude ido Ajay yayi bayan Jay ya kai hannunsa goshinsa yana kallonsa, Jay yace "Good morning Bruh, wishing you more fruitful years ahead" Ajay har ya mance yau ne ranan zagayowar haihuwarsa, juyawa yayi, yayi kwanciyar rub da ciki ya mayar da idonsa ya lumshe without replying him don bacci yake ji saboda maganin da ya sha, Jay ya juya ya fita daga dakin, Bangaren Maminsa ya tafi yayi sallama yana tsaye kofar dakinta ta amsa sannan ya shiga, har lokacin tana zaune saman darduma rike da counter, ya zauna yana kallonta ya gaisheta, da murmushi fuskarta tace "How was ur night Dear?" Jay yace "Alhamdulillah" Mami tace "Jiya na shiga part dinka wajen karfe sha daya naga kayi bacci" Jay bai ce mata komai ba, don idonsa biyu ba bacci yake ba sanda ta shigo, shi bai ma yi bacci ba sai kusan karfe daya da rabi jiya don gaba daya baccin kaurace masa yayi, Mami tace "Hadiyah ma wai nan da sati biyu zata dawo ko?" Jay yace "Ohk..." Don shi bai ma sani ba, after some seconds a hankali yace "Pls Mami Ina son maki magana ne amma don Allah ki fahimce ni, zan shiga damuwa idan kika yi misinterpreting dina cause kece mutum na farko da nake saka ran zata fara fahimta ta bayan Mai martaba, I need you to consider my points plss Mami" Yana kai wa nan ya daga kai ya kalleta yaga kallonsa take with full attention don har taji hankalinta ya tashi ganin damuwar da ya bayyana karara a fuskarsa cikin kankanin lokaci, shiru yayi bai sake cewa komai ba ya sauke idonsa, Mami ta kwantar da murya tace "Kana da wani a duniyar nan da zaka gaya ma damuwar ka da ya wuce ni ne Jawwad?

Why is it taking you so long to voice out what the issue is?

Kusan wata biyu kenan kana min nuku nuku ka ki gaya min menene matsalar, ko ka ta
a min wata magana ne kaga ban baka goyon baya ba ko da kuwa bana son abun nan son?

I don't think there is anything I can't do for you, ka kwantar da hankalinka ka min bayanin menene ke faruwa" a hankali Jay yace "Ohk, dama Mami gaskiya ni yanxu ina da warce nake so zan aura, na duba abubuwa da yawa naga i and Hadiyah are not compatible, dama ita din zabin ku ce ba zabina ba, a wancan lokacin saboda inyi biyayya yasa na amince ban yi ma kowa gardama ba, yanxu kuwa i have my choice Mami kuma ina sonta sosai, ki yi hakuri Mami ban san yanda zaki dau wannan zancen ba, amma goyon bayan ki shine kwanciyar hankalina...." Shiru ya
an yi na few seconds har sannan kansa na duke yana kallon kasa, a hankali ya ci gaba yace "Amma kuma i have no issue marrying them both saboda gudun abinda zai je ya dawo considering our relationship with Hadiyah is in this family, in dai za a amince min ni na yarda zan hada su duka....
Chapter 187 · 0% Book details