← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 191

Sashe 96

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kai na mace ne?" Bata jira cewarsa ba ta bar wajen ta shige kitchen ya bi ta da kallo, Tuttular da shayin tayi a sink sannan ta juye sauran irish din da kwai da farfesun duk ta cakudesu waje daya tace "Gasu nan ki kai ma karnuka, in kuma kwadayin ki ya ja ki kika ci ke kika jiyo" Mai aikin ta risina ta amsa tace "Toh Hajiya" Sai da Momy ta jirata har ta dawo bayan ta kai ma karnukan can cage dinsu sannan Momy ta dau breakfast din Abdul ta kai masa kan dining din tace "Ga naka nan" Daga haka ta juya ta bar wajen, dai dai shigowar Godiya gidan, da fara'a Momy ke mata sannu da zuwa Abdul ya dauke kai kamar bai ganta ba don ya tsani matar with passion, tun asali dama baya gaida ta, Haka Momy ta ja ta zuwa sama tana cewa "Mu je ki ga surkar tawa ku gaisa" Da ido Abdul ya bi su har suka haura sama, Momy na isa kofar dakinta ta bude da makulli suka shiga, Khaleesat dake gyara gadon Momy ta mike tsaye tana kallonsu, Momy na murmushi ta kalli godiya tace "Kin ganta" Da fara'a sosai Godiya tace "Maa sha Allah, ai ko ga ta kamar balarabiya Maa sha Allah, sannu amarya, ya sunanki?" Momy na murmushi tace "Sunan Baabata gareta, Hauwa sunanta" Khaleesat ta zame kasa ta sauke idonta ta gaida Godiya, Godiya ta karasa kusa da ita ta dafata tare da
agota ta zaunar da ita gefen gadon Momy tace "Lafiya lau diyata, ya bakunta?" Khaleesat bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Momy na kallon Khaleesat tace "Kin sha tsumin da nace ki sha kuwa?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Na sha" Momy tace "To maa sha Allah, Allah ya maki albarka Mamana, zuwa anjima sai ki kara sha kin ji" Khaleesat tace "To" Bayan few minutes Momy da Godiya suka fita dakin, Momy ta sake kulle kofar da makulli sannan ta cire makullin suka tafi wani daki dake sama, bayan sun shiga Momy ta kulle kofar tana kallon Godiya tayi murmushi tace "Duk tayi amfani da abubuwan babu gardama godiya, iya na jarkan nan ne kawai ya rage yanzu" Godiya ta zauna gefen gado tace "To madallah, shi ma Abdul din duk kinyi yanda aka ce kiyi da na sa?" Momy tace "Kwarai kuwa" Godiya tayi wani murmushi ta bude handbag dinta ta ciro wani babban laya bakikirin da shi ga er karamar kwado a jiki ta mika ma Momy tace "To aikin karshe kenan wannan Hajiya, Malam ya ce ki samu inda kika san baza a ta
a tono sa ba ki binne a cikin gidan nan" Momy ta zauna gefenta tana murmushi ta amshi layan tace "To laya nawa na binne gidan nan ba a tono ba godiya, ai wannan karamin aiki ne a wajena don ba sabon abu bane" Godiya tace "Yauwa, bayan kin binne Malam yace ki basa yarinyar kawai, wallahi yace min in har ta wuce sati biyu Abdul bai rabu da ita ba to bazata wuce sati biyar ba a gidansa" Fara'ar fuskar Momy ya bace tace "Har sati biyar Godiya?

Ni da yace min sati daya kacal a waya" Godiya tace "Halan bai gaya maki irin abubuwan dake
an dan ki bane?

Da yaya ma aka samo kansa har asirin nan yayi tasiri?

Ai abubuwan
an Abdul sun fi karfin wani asirin wallahi kiji in gaya maki" Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "An ta
a gaya min haka da dadewa wallahi, don ni akwai malamin da yace min ma yanda asiri ke cin ubansa shi sai an wahala asiri zai ci sa" Godiya tace "To wallahi Malam sai da ya tura masa aljanu don ma ki ji Hajiya, aikin nan sai da Malam ya hada da wasu malaman don aiki ne me wahalan gaske yace min wallahi" Momy tace "To ni fargabana kada fa in mika masa yarinya ace asirin nan bai ci ba abinda muke gudu ya afku mu shiga uku Godiya" Godiya tace "Sai kace yau Malam ya fara maki aiki?

Ai da aikin bai yi ba kinsan bazai boye mana ba, sai dai ya kara mana lokaci yayi wani sabon aikin fa, dama yace in na yarinyar ya ci shine zai sa na Abdul din ma yayi tasiri sosai" Momy tace "Haka ya ce kam" Godiya tace "Don haka zuwa gobe ki basa ita kawai su tafi an gama aiki sai jiran result, kuma ina me tabbatar maki zaki sha mamaki" Momy na murmushi tace "Toh shikenan godiya, nagode sosai, zan tura masa cikon dubu dari biyar dinsa anjima" Da yammacin ranan bayan Momy taga Abdul ya fita gidan tayi maza ta aiki mai aikinta kasuwa saboda tayi amfani da daman ta ha
a rami a garden din gidan ta binne layan da Godiya ta kawo mata, bayan mai aikin ta tafi Momy ta zaga zuwa garden din gidan ta samu spot me kyau ta fara ha
a rami da wuka, bayan ta haka yayi zurfi yanda take so sannan ta jefa layan ta mayar da
asan wajen ta dau wani dutse ta dora dai dai wajen don kada a ga alamar an tono kasa, tap ta bude don wanke hannunta da wu
an da tayi using, Khaleesat ta karasa bakin window din dakin Momy jin
aran bude ruwan pampo, in ta gaji da zaman dakin dama jikin window take zuwa ta tsaya tana kallon waje, ta tsaya jikin window din tana ta kallon Momy dake ta wanke hannunta bayan ta wanke wu
an, bayan ta gama ta kara komawa kusa da dutsen tana seta sa da kyau ta yanda ko da wasa baza a ga tonannen
asa ba, sai kuma ta mike ta fara tsinko doddoya dake Garden din, sannan tayi using wu
an hannunta ta yanki pumpkin leaves isasshe bayan ta gama ta bar garden din tana rike da ganyayyakin hannunta, babu abinda Khaleesat ta kawo a kai don tunaninta ganye Momy taje diba a garden din, Momy na kai ganyayyakin kitchen sai ga su Meemah sun dawo daga shopping din da ta aikesu su yi ma Khaleesat, dariya Momy ta dinga yi a parlor ganin wasu shegun abayoyi masu saukin kudi da suka kwaso ma Khaleesat irin wanda ake dinkawa a kano, ga wasu shegun dogayen riguna su ma masu arha, hatta inner wears da suka siyo duk very low quality ones ne, babu wani abu na arziki da suka siyo ma Khaleesat, Momy na ci gaba da dariya tace "Duk maida su cikin ledojin kawai na yafe ganin wannan tarkace haka karima, amma baku da kirki yaran nan" Aunty Karima na dariya ta maida kayan cikin leda ta kulle tace "Su ne dai dai er talakawa ai Momy, da so kika yi ki ga abayan dubu hamsin zuwa sama?

Ai ita Meemah ma en gwanjo ta so mu je muyi selecting mata kawai" Dariya kawai Momy take, ita kuwa Meemah danna wayarta kawai take don duk wani abu da ya shafi Khaleesat ko kadan baya bata dariya, she just can't wait taga irin rabuwan da Abdul zai yi da Khaleesat don shine babban abinda ke gabanta yanxu.

Wajen karfe takwas da rabi Momy na zaune parlor da Abdul tana ta yi masa hira, shi dai wayarsa kawai yake dannawa baya responding kamar ma bai san me take cewa ba, Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da gudu tace "Na'am Hajiya?" Momy tace "Zaki ga Kankana da na yanka a kitchen ki dauko ki kai ma Mamata a sama" Mai aikin tace "To Hajiya" Juyawa tayi ta koma kitchen sai ga ta ta dawo rike da bowl din kankanan tana kallon Momy cikin ladabi tace "Amma Hajiya dakin a kulle yake" Momy tace "A'a a bude yake tun daxu, ki je ki kai mata" Bayan mai aikin ta tafi ta kai water melon din ta dawo ta tafi kitchen ta ci gaba da aikin da take, Momy ta dau wayarta tace "Bari in inyi waya da Alhaji, daxu na ga kiransa ina kitchen wallahi" Shi dai Abdul bai ce mata komai ba har ta shiga dakin dake downstairs ya bi ta da kallo...

Bayan minti biyu ya mike ya nufi stairs direct ya tafi bangaren Momy, yana bude kofar dakin Khaleesat dake zaune saman darduma bayan ta idar da sallah ta gama duk addu'o'in da zata yi ta juya ta kalli kofar, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Abdul, ya karasa cikin dakin babu yabo babu fallasa yace "Ta shi mu je shopping...." Khaleesat da gabanta ke faduwa ta nuna masa ledan da Momy ta kawo mata daxu duk da bata duba kayan ciki ba cikin sanyin murya tace "Ai Momy ta sa an min shopping din, ka gan su
can ma" Ya hade rai yace "Kee...

Get up nace, i am not asking for ur opinion" Ta sauke idonta ta mike tsaye da kyar ta dauke darduman tana linkewa, sosai taji hankalinta ya tashi, a ranta ta dinga addu'an Allah ya kawo Momy dakin immediately, fixge darduman hannunta yayi ganin it's taking her a whole eternity to fold, ya ajiyesa saman kujera sannan ya kama hannunta suka nufi kofa fuskarsa a daure suka fita daga dakin, Khaleesat dai bin sa kawai take a tsorace, downstairs suka sauka har sannan yana rike da hannunta, babu kowa a parlorn sai mai aiki dake goge goge a dining area, ya dau makullin motarsa da ya bari kan center table, Khaleesat ta marairaice masa cikin rawan murya tace "Ya Abdul Momy fa bata sani ba, kar ta shiga dakinta taga bana nan, kaga babu dadi haka" Wani kallon da yayi mata yasa tayi shiru zuciyarta na bugawa, bata sake gigin ce masa komai ba har suka fita parlorn gidan zuwa parking space, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta bayan ya sa ta shiga motarsa ya shiga driver seat, mai gadi ya bude masa gate ya fice gidan da motar.
Chapter 96 · 0% Book details