← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 191

Sashe 2

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Friday da wuri Khaleesat suka gama lectures dinsu, suna zaune a exact spot din jiya ita da Safiyyah dake waya, sosai Khaleesat tayi nisa tunanin da take har bata san sanda Safiyyah ta gama waya ba, dafa kafadarta da Safiyyah tayi ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, Safiyyah tace "What is wrong Khaleesat, ina ta magana baki ma san ina yi ba, tunanin me kike haka?" Khaleesat ta
an kirkiri murmushi tace "Kawai ina kewar Ummanmu ne da siblings dina" Safiyyah ta girgiza kai tace "Ban yarda ba, there is definitely something that is bothering you" Khaleesat ta kauda zancen tace "Ke da George ne ke waya ko?" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Pls gobe weekend ki shirya mu tafi Virginia Leesat, George is throwing a party for his birthday tomorrow, kuma za mu je Beach, don Allah kar ki ce a'a, we need to take a break and rest our brain, ba ko da yaushe karatu ba kamar mu muka kawo boko duniya...." Khaleesat dake ta kallonta tace "Ke yanzu sai ki kama hanyar Virginia Safiyyah??" Safiyyah ta hade girar sama da ta kasa tace "To menene, it's just a 4 hours ride from Maryland, kamar fa ace daga kaduna zuwa kano shi ma in mota bai yi gudu ba, pls for once ki zama social mana Khaleesat, ke baki gajiya da zama guri daya ne a kasar nan?

Baki gajiya da karatu? ranan Monday fa za mu dawo in sha Allah, kuma babu wanda zai san mun je wani Virginia, dama Ya Mustapha na riga na gama plan din abinda zan ce masa, ke da ba ma ki da wanda zai sa maki ido kike mis using opportunities haka, da mun koma Nigeria fa shikenan, tafiyar nan maza ne hade da mata" Khaleesat ta girgiza kai tace "Lallai...

Ni dai ina baki shawara kar ki je Safiyyah" Safiyyah tace "Bana ma son shawaran, abinda mu goma za mu je" Khaleesat tace "Toh Allah ya tsare hanya ya dawo da ku lafiya" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Baza ki je ba kenan dai?" Ba tare da Khaleesat ta kalleta ba tace "Kema kin san bazan je ba ai" Safiyyah tace "Ke kika sani, mu dai za mu je wallahi" Safiyyah na kai wa nan ta mike tace "Sai ran Monday" Khaleesat na kallonta a hankali tace "Wai tafiya za ki yi?

Da sauran time fa Safiyyah" Safiyyah tace "Aa toh me za mu zauna yi a schl bamu da aji?

Yau kuma kece ke cewa da sauran time duk son ki da komawa gida da wuri?

Ikon Allah" Khaleesat ta kasa cewa komai, ita har ranta take jin ta tsani gidan nata yanzu, she no longer see the home as her comfort zone, and she don't think she can cope staying together with an Hausa Guy under same roof, da ma bature ne ko kadan bazata damu ba kamar yanda ta damu yanxu, har ta taho school bata hadu da sabon Housemate din nata ba da safe, Safiyyah ta
an buda ido ta koma ta zauna tace "Ohh now i remember, wai saboda new House mate dinki?

To wai ke meye damuwarki ne da shi?

Yayi harkan gabansa kiyi naki ne fa a gidan, ko magana in baki son ya maki you just call the cops a maki iyaka da shi, just dial 911 and that's all, balle nasan kilan da kyar aka kukuta masa ya taho makaranta kasar nan to kuwa ina zai tsaya bata lkcnsa akan abinda ba shi ya kawo sa ba, don dai in wani Shege ne shi bazai zauna a shared apartment ba a USA, kuma 'ya yan masu kudin nan sun fi iskanci su kuwa talakawa abinda ya kawo su kawai suke yi, kiyi ta kanki kawai shi ma yayi ta kansa, kar kiyi mamaki ta scholarship ya zo kasar ma" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta kyabe baki tace "Tashi mu je gidan, ni banda Ya Musty bazai yarda ba da ba sai in tattaro in dawo gidan naki ba mu zauna kawai" Khaleesat ta marairaice tace "Plss ki sake masa magana ko zai bar ki mana, ai sanda ya hanaki kinga bamu dade da fara makarantar ba" Safiyyah tace "Kar ma ki bata bakinki mutumin nan bazai yarda ba, tashi mu je in raka ki, in House mate din ma yaga kina wani yin abu a tsorace renaki zai yi wallahi, yi zaki yi kamar kema er gari ce kawai sai ki ga ya fara shakkar ki a gidan" Khaleesat ta mike tace "Kar fa muje kiyi ta Hausa, just pretend we are not Hausa" Safiyyah tayi dariya tace "Kece dai is not Hausa, ni kam Bahaushiya ce cikakkiya kuwa" A haka dai suka bar makarantar suka nufi gidan da Khaleesat take....

Khaleesat ta bude handbag dinta ta ciro makulli ta bude kofar shiga gidan suka shiga parlor Safiyyah na biye da ita a baya, Safiyyah na gyada kai jin wani kamshi da parlon yake tace "Da alama bai dade da fita ba ma" Khaleesat dai bin parlon take da kallo ganin duk reading materials dinsa ne saman kujera ya tula a kai, Safiyyah tace "Kinga don Allah ki saki ranki ki ci gaba da harkokin ki Khaleesat, a Maryland fa kike a Amurka ba Kano Nigeria ba, ki dinga abu irin na wayayyu mana pls" Wani kallo Khaleesat tayi mata ta ajiye handbag dinta tace "Ance maki in bature ne ko wani yare ni zan damu, kawai my issue here is about him being a Hausa Guy, har fa tambayata yayi jiya ko ni bahaushiya ce" Safiyyah tace "Ohh kun ma yi magana kenan...." Khaleesat tace "Ni ban kulasa ba kuma ban nuna masa ni Bahaushiya bace, i will just pretend i am from Morocco" Safiyyah ta dinga dariya har da saukowa daga kan kujera tace "Gashi kuwa an ma fi saninsu da fararen mata kyawawa na ajin karshe, tsaf zai yarda daga can kike, kinga da larabci ya zauna daram a bakinki sai kiyi ta zabga larabci nasan ba lallai yana ji ba, daga haka zai kama kansa yayi zaton ke balarabiyar gaske ce... sai ma Abdul yaji kuna gida daya da Bahaushe kilan Baltimore yayi maku kadan wallahi, shi sa nace ki gaya masa kika ki" Khaleesat ta ajiye jakarta bata sake kallon Safiyyah dake ta dariya ba tayi wucewarta kitchen tana tunanin me zata dafa masu dama ko breakfast bata yi ba ta fita daga gidan, tsaye tayi kitchen din tana kallon cartons din bottle water kusan bakwai wanda duk yafi tsada a state din, sai kuma ta juya ta kalli beverages masu yawa da ya ajiye kan cabinet, ta karasa cikin kitchen din ta bude babban fridge zata dau kwai da za ta dafa masu Noodles, kallon fridge din ta dinga yi ganinsa fully stocked with everything, tun daga tsadaddun drinks kala kala, fresh milk, varieties of fruits, with many eggs, muryar Safiyyah taji a bayanta tace "Kai kai kai, shi ya zuba abubuwan nan a fridge Leesah?" Khaleesat ta juya ta kalleta looking speechless, can dai ta dau eggs din da zata dauka ta kulle fridge din ta tafi inda foodstuffs dinta suke shi ma taga kayan abinci ya siyo, Safiyyah ta rike ha
a tace "Duk a kudin scholarship din yake facakan nan?

Ko dai bashi da hankali ne bai san bin komai ake a sannu a kasar nan ba" Khaleesat dai ta dau Noodles dinta ta bar wajen tana kallon Safiyyah tace "Ga Indomie ki dafa mana, ina son inyi magana da Ummanmu kafin Aunty Sha'awa ta fita kasuwa" Safiyyah tace "Ohk to" Khaleesat ta bar kitchen din ta dau jakarta ta wuce dakinta, WhatsApp dinta ta bude ta shiga contact din makociyarsu Sha'awa tayi mata voice note kamar yanda ta saba a duk sanda take son magana da Ummanta.

Sai kusan karfe hudu na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zuwa gun Lyft din da tayi ordering don tun daxu Cousin brother dinta ke kiranta ganin bata dawo gida ba, Safiyyah ta shige motar ta kulle tana daga ma Khaleesat hannu, sai da Lyft din ya bar wajen sannan Khaleesat ta juya tana tafiya a hankali ta nufi apartment dinta, dai dai apartment din taga mota yayi parking a space din da aka tanadar don parking for that apartment, bata karasa ba ta jingina jikin fence din dake inda take tsaye tana kallon motar ta little space din dake between the wooden fence din, taga ya fito daga motar ta bi sa da ido har ya shiga apartment din yana danna wayarsa, ta fi minti biyar tsaye a inda take, daga karshe tana tafiya a hankali ta karasa apartment din ta murda kofar parlon taji ya kulle, hade rai tayi tana kallon kofar, daga karshe da ta gaji da tsayuwa kawai tayi knocking, sau uku tana knocking sannan ya bude kofar, yana ganinta yace "Hi" ita dai ko kallonsa bata yi ba fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi gefensa ta shiga parlon, direct gun wayarta dake kan kujera ta nufa ta dauka tare da reading materials dinta dake saman kujeran, har zata dakinta sai kuma ta dawo ta tafi kitchen ta dau goran ruwa daya sannan ta nufi dakin, sai da ta bude kofar tayi masa kallon gefen ido taga he is just busy sorting out some textbooks that were inside a carton he came with, har ta shiga dakin nata bai juya ba balle ya kalli direction dinta....

HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
2.....
Chapter 2 · 0% Book details