← Book details Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 191

Sashe 13

Halysaah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdul din ne yace ki taho?" Gaje ta daga hannu sama da sauri tace "Aaaa tace bai ma sani ba" Aunty Farida na kallon Khaleesat da mamaki tace "Ban gane bai sani ba??" Khaleesat ta marairaice ta kauda zancen ta hanyar cewa "Aunty ya jikin Ummanmu?" Aunty Farida ta kamo hannunta suka zauna saman tabarma tace "Ai jikin Umma da sauki sosai Khaleesat, gashi har an sallamemu a asibiti, wa yace maki bata da lafiya ne ma tukun?" Khaleesat da har hawaye ya ciko idonta tace "Aunty Sha'awa" Gaje tace "Lahh ha ila, wato Sha'awa bazata dena munafurci ba ko?

Wato bazata canxa hali ba ko?

Da kaina fa sai da na jaddada mata kar ta gaya maki ko kin mata sako ta wassol don kar hankalinki ya tashi, ashe sai da munafukar ta zaga ta fada maki" Aunty Farida tace "Toh Allah ya kyauta, kwata kwata Sha'awa bazata canza ba" Khaleesat da hawaye ke cika idonta tace "To Aunty ta yaya zan ga Ummanmu yanzu?" Aunty Farida tace "Kar ki damu kiyi zaman ki nan wajen Baaba Gaje, gobe da safe in za mu tafi asibiti sai mu fara biyowa ta nan da Umman tunda asibitin Malam Aminu kano ne" A hankali Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu Aunty" S
ai bayan Magrib Aunty Farida ta bar gidan bayan ta ci tuwon da Khaleesat tayi ma Gaje, sosai Khaleesat taji ta samu rest of mind bayan taji jikin Ummanta da sauki, bayan Isha Gaje ta gyara mata
an lungun da zata kwanta a dakin ta daura mata net din sauro tace "Allah dai ya rabaki da cinnaku" ita dai Khaleesat tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ita matsalarta ma zafi, ko ya zata yi da zafi yau gashi karamin dakin wani
an mitsitsin window ne kawai ke garesa, su bakwai kuma zasu kwana a ciki, Khaleesat ta gama shirin kwanciya don tayi wanka sannan ta shiga net din ta kwanta, ta amshi maficin da gaje ke mika mata ta cikin net din, tun dawowarta sai a sannan tayi subscription ta shiga WhatsApp dinta, Message din Safiyyah dake tambayarta ko ta isa lafiya kadai tayi ma reply, bata yi mamakin rashin ganin message din Abdul ba don she isn't even expecting his message, ajiye wayar tayi ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido, Housemate dinta ne ya fado mata, she have no access to him balle ko godiya ma tayi masa, bata yi tunanin da ta fito zata tafi airport bazai tambayeta phone number dinta ba, ko Airport din ma bata yi tunanin bazai yi offering yace zai kai ta ba, juye juye kawai take yi a net din idonta a rufe, after a while of thinking bacci ya dauketa.

Washegari Khaleesat ta gama yi ma Baaba Gaje duk aikace aikacen gidan, ta hura gawayi ta daura ruwa tayi ma kananun jikokinta wanka sannan ta dama kunu, Baaba Gaje ta fita siyo masu kosai a titi, har karfe goma Khaleesat bata ga Aunty Farida sun zo gidan da Ummanta ba, gaba daya ta damu taga Ummanta, Baaba Gaje tace "To ke sai ruwan ya salance zaki je kiyi wankan?

Ba fa wani gawayin" Khaleesat tace "Zan yi" Daga haka ta mike ta tafi yin wankan, tana fitowa daga wanka taga takalmin da Aunty Farida ta zo da shi jiya a bakin kofa da wani takalmin daban wanda ko ba a fada ba tasan na Ummanta ne, da sauri ta shiga dakin Baaba Gaje taga Ummanta da Aunty Farida a zaune, tsallake Aunty Farida tayi ta tafi gun Ummanta da gudu cike da farin cikin ganinta ta durkusa gabanta ta rungumeta, Aunty Farida tace "Ko dai baki da hankali ne?" Baaba Gaje tace "Toh da sauki dai kam" Ita dai Umman sai kallon Khaleesat take, gaba daya Khaleesat ta ma mance wai Umma bata da lafiya tsabar farin cikin ganinta, a hankali Umma tace "Meyasa zaki biyo hanya Khaleesah?

Abdul din ne yace ki dawo?" Khaleesat ta kamo hannunta cike da damuwa tace "Umma ya jikin?" Umma tace "Naji sauki Alhamdulillah" Khaleesat tace "Aunty Sha'awa tace min ko magana fa baki yi" Baaba Gaje ta rike ha
a tace "Oh ni 'ya su, kun ji er iska ko?

Wallahi Sha'awa da kyar taga annabi, babu yanda bamu yi da ita ko da wasa kar ta gaya maki ba ashe sai da ta zaga ta fada, har ce mata nayi tace maki tayi tafiya ko da zaki buga nata wassol" Khaleesat ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Ni ce na kirata don ina ta magana bata min reply ba" Aunty Farida tace "Ai tsabar munafurci yasa ta gaya maki ba wani abu ba" Khaleesat ta
an yi murmushi ta gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa tace "Amma shi Abdul yasan Umma bata da lafiya shine ko kira ya dubata bai yi ba?" Khaleesat ta sauke idonta kasa tace "Ni fa bai san na dawo ba Aunty" Aunty Farida tace "Wai ban gane bai san kin dawo ba, wa ya biya maki kudin jirgin?" Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallonsu, Sai kuma a hankali tace "Wani ne ya biya min ba Abdul ba" Umma ta kalleta da sauri tace "Wani?" Da mamaki Aunty Farida tace "Wani a ina?" Khaleesat na kokarin mikewa tace "Neighbor dina ne" Umma ta bude baki tana kallonta, sai kuma tace "Ko baki da hankali ne, waye ya biya maki kudin jirgi Khaleesah?" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Gaje tace "Bude baki zaki yi ki mana bayani dalla dalla, waye shi zai biya maki zunzurutun kudi na jirgin da naji ance ya fi miliyan daya?

A ina kika san sa?" Still dai Khaleesat taki cewa komai, Aunty Farida tace "Ke bana son rainin wayo uban wa zaki ma shiru ana maki magana?

Ko baki ji tambayar da ake maki bane?" Umma dai kallon Khaleesat kawai take da mamaki, Khaleesat ta koma baya ta
an sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni fa nace makocina ne ya biya min, kuma ai gani yayi ina ta kuka Ummana bata da lafiya shine ya biya min jirgi in dawo in dubota" Cikin sanyin murya ta kare maganar, Baaba Gaje tace "Atoh dama ai ko ina ana samun na Allah, Allah ya masa albarka, Bature ne ko?" A takaice Khaleesat tace "Um" don bata son ma a ci gaba da zancen, Baaba Gaje tace "Ko da naji, ai sai baturen dama, wani ba
in fata ne zai biya maki jirgi don yana makocinki, ai ko mutuwa uwar taki tayi iyaka ya maki gaisuwa ya kama gabansa, to Allah ya saka masa da alkhairi, abinda ma baturen kudin jirgin ba wani kudi bane a wajensa, ji zai yi kamar naira dubu goma ya kashe fa" Khaleesat na kallon Aunty Farida tace "Aunty yanzu za aje asibitin ne?" Aunty Farida tace "Aa mu har mun dawo daga asibiti sai kuma na gobe in Allah ya kai mu" a hankali Umma tace "Toh da ya biya maki kudin jirgin zuwa wa zai maki na komawa yanzu?

Kinsan dai ko hauka kike baza ki bari Abdul yaji wannan batun ba ki ja mana masifa ko?" Sai da gaban Khaleesat ya fadi, a hankali ta sunkuyar da kanta, ita gaba daya ta ma mance ashe biyan jirgi za ayi a koma, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, yanzu ina zata samu kudin ticket din komawa, she became so weak at once, Aunty Farida tace "Toh shi Abdul din baki ce masa Umma bata da lafiya bane?" Khaleesat da har sannan jikinta yake a sanyaye ta girgiza kai tace "Baya nan ne" Daga haka ta mike ta tafi zata shirya don zanin da tayi wanka ne daure jikinta har a lkcn, Khaleesat na cikin saka kayanta da ta fiddo a akwati 1000 dollar din da Housemate dinta ya bata suka fado mata a rai, ta zaro ido lkci daya taji hankalinta ya kwanta har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tasan probably in ta canza har da 100 dollar din da Safiyyah ta bata kudaden za su iya maidata Amurka, she felt so relieved, nan da nan walwalarta ya dawo, tana jin Baaba Gaje na tambayar Aunty Farida ko kishiyoyin Ummanta sun shiga dubata yau, Aunty Farida tace "Jiya ma basu shigo dubata ba sai yau Baaba Gaje" Baaba Gaje tace "Shegu matsiyata, so fa suka yi ace ta mutu, to shi Malam Alin ya ku ka
arke da shi?

Ya bada kudin?" Aunty Farida tace "Aa ni fa ban bi ta kansa ba Baaba Gaje, dama me ya tsinana kafin in zo kanon? daxu ma aka turo min sauran kudin adashina da nake jira, duk na siya sauran magungunan" Baaba Gaje tace "Atoh dai bai ta
uka komai ba a takaice, shi ma da zaki basa yanxu tsaf zai amshe" Har aka yi azahar su Umma da Aunty Farida na gidan, Umma har tayi bacci ta tashi saboda maganin da take sha, har a sannan da kyar take taka kafarta daya, hannunta dai ya sake ya dawo normal tun a jiya, Khaleesat ta shigo dakin da shinkafa da waken da ta dafa, Baaba Gaje kuma ta shiga makota dubiya, Aunty Farida dai sai bin Khaleesat take da kallo, sosai taga ta kara kyau tayi fresh, duk da dai tana nan a yanda take babu kiba, komawa tsakar gida Khaleesat tayi ta dauko man gyadan da ta soya ta dawo dakin, ta fara zuba ma Umma da Aunty Farida abincin, Umma dake zaune kan darduma tana kallonta tace "Kun fara jarabawan ne?" Aunty Farida tace "Haba dai sun fara jarabawa zata taho?
Chapter 13 · 0% Book details