Sashe 9
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido ya tsira Mata cikin ransa yana saƙa abubuwa iri-iri a kanta, duk da ranar da ya fara ganinta ta yi kwalliya amma sai ya ga kamar yau ta fi kyau.
"Barka da fitowa kyakkyawar Sarauniya!, Ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali!" harara ta zuba masa kafin ta ja tsaki ba tare da ta yi magana ba.
Ci gaba ya yi da cewa "Gaskiya ni me sa'a ne da na sake ganinki a rayuwata, da farko na shiga wani hali na damuwa don na yi zaton shi kenan idanuna ba za su ƙara tozali da Kyakkyawar fuskarki ba, na gode da damar da kika ba ni Leelah!!" Sumayya ce ta ɗaga masa hannu tana cewa "Ya isa !, ba mun zo ne mu saurari Tatsuniyarka ba, Ni a matsayina na Yayar Leelah ya zama dole na tantance ka kafin na bari ka fara ganawa da ita, ƙoƙarinka na cinye Jarabawar shi ne zai sa ka yi nasara". "To Anti! in Allah ya yarda zan yi iya bakin ƙoƙarina domin tsallake wannan Jarabawar, ina Matuƙar son Leelah Anti! zan yi duk iya bakin ƙoƙarina domin na kyautata mata."
tin da ya fara magana idanun Sumayya suna kansa, cikin ranta tana ƙara yabawa da irin baiwar da Allah ya ba shi, ga magana ta kamala daki-daki, duk da ta san Talakan ne amma a wani kuiɓin na Zuciyarta sai ta ji Kishinsa, ji take ina ma a ce ita yake so ko shakka babu ko ba za ta ci ko sisinsa ba za ta yi soyayya da shi ta ragin lokaci, iyakaci watarana ya buɗe ido ya ji an Ɗaureta da wani ta bar shi a nan ƙwadagwas!.
Sirrintacciyar ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Da farko ina son sanin cikakken sunanka da kuma sana'arka, a Sati ko Wata kana samun Kamar nawa?, Menene matakin Karatunka?, sannan me yasa kake son Ƙanwata?"
Gyara tsayuwarsa ya yi gami da yin ƙasa da kai sannan ya fara da cewa "Sunana Aliyu Mahmud, ni ɗan Unguwar Ɗorayi ne, Babana yana Sayar da Atamfa a Kasuwar Rimi, Mamata kuma tana sayar da Goro a cikin Gida, ina da Ƙanwa guda Ɗaya, matakin karatu kuma...am.. abin nan... na dai yi Candy amma in sha Allahu zan ci gaba, sana'a kuma gaskiya ba abinda ba na yi, ina sayar da Rake, sannan ina wankin Mota, kuma idan na samu wani ɗan aiki da za a yi kamar na gini haka ko ɗibar ƙasa ina yi, kuma ba laifi ina samu gaskiya, kuma in Allah ya yarda na kusa fara aikin gyaran Mota ina sa ran shi ne tsayayyen aikina; abinda ya sa nake sonta kuma gaskiya ba zan iya cewa ga Hujja ba, kawai abinda na sani ita ɗin ta cancanta a so ta, Tin da na ɗora idona akanta hankalina ya bar jikina ba na iya ganin komai sai ita, na kasa tunanin komai sai nata, kun san shi So Sarki ne, yana iya riskar Mutum lokaci ɗaya koda ba a shirya ba."
sai da ta ɗan sarata kafin ta kalleshi fuska ba yabo ba fallasa ta ce "Wace irin soyayya kake yi mata? shin kana so ka aureta ne?, idan na ce ka fito a yi Aure yanzu za ka iya??" murmushi ya saki kafin ya ce "Soyayyar gaskiya nake mata ba ta wasa ba, ina sonta da duk Rai da Zuciyata, idan kika ce na fito kin yi mini babbar Alfarma a rayuwata, Allah ne kaɗai zai biyaki Alkairin da kika yi min, Rashin kuɗi shi ne zai ɗan kawo tsaiko a Aurenmu shi ne zai hana a ɗaura shi koda a yau ne, don ni a shirye nake, amma ina da ƙoƙarin neman halak zan yi aiki tuƙuru don na haɗa kuɗin da zan yi komai na Auren a cikin ƙanƙanin lokaci."
"Anti Summy ki bar saurarar wannan sakaran shashashan!!, ni wallahi ko Maza sun ƙare ba abinda zan yi da shi, ni ba zan Auri jinin Talauci ba, ka ɗebo wani Yadi ka saka kamar za ka tafi roron Wake a hakan kake tunanin yin soyayya da ni?" Sumayya ta ce "Relax ƙanwata!, kwantar da hankalinki!" tsaki Leelah ta yi gami da juyar da kanta gefe.
Maganganunta sun doki Zuciyarsa matuƙa gaya, sai dai ba yadda zai yi dole ya jure don yana son goge mata duk wani banzan tunani da yake kanta, sai yanzu ya ƙara gane zuwar mata ma a matsayin me kuɗi har ya Aureta tamkar ya kashe Maciji ne bai sare kansa ba, duk ƴaƴan da za ta haifa masa haka za ta shuka musu irin banzan tunaninta, don haka dole ne ya goge mata tata haddar ya koyar da ita wani Darasin.
"To Malam Aliyu gaskiya ko maki ɗaya ba ka da shi na yin soyayya da Ƙanwata bare kuma Aure!, ka yi haƙuri ka kama gabanka sannan kar ka ƙara waiwayo mu, a matsayina na babba nake baka wannan shawarar don ba na so a yi rabuwar da ba ta Mutunci ba, kar ka ƙara neman Leelah ba kai ba ita in ba haka ba duk matakin da muka ɗauka a kanka kai ka sani don mu ba a kawo mana raini."
Ikilima ta ce "Ai wallahi ni ban so ki ce haka ba Anti Summy, so na yi ki bar mu da shi mu yi masa Bugun Dawa ta yadda ba zai ƙara marmarin tuna Leelah ba, kai in banda babu ƙwaƙwalwa a cikin kanka ka dubeta ka dube ka fa? me gareka? me za ka iya bata? ni wallahi gani nake kai ɗinnan ko kana da Kuɗi ba ka isheni komai ba ka yi min kaɗan, bare kuma ba ka da Abokan rayuwa." Haja ta ce "To ai shi ne fa, ƙarfin hali ne da tsaurin ido irin na Bunsurun Namiji, wallahi mu da kake ganin mu sai mu yi maka tsirara mu koraka gaban tsohuwarka!"
Cikin sauri ya mayar da kallonsa kanta yana mamakin jin abinda ta faɗa, jinjina kai ya yi gami da sakin murmushin Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ai kuwa indai haka ya faru sun jawowa kansu silar bajewar Rayuwarsu, tarihinsu ma da ba za a ƙara ji ba.
"Meye ka tsatstsare Mutane da ido? ka samu ka salallaɓa ka gudu tin kafin na yi maka ihun kwarto!!" Salim ya faɗa cike da iyayi da kwainane.
"Zan tafi amma ga wannan Leelah ki karɓa don Allah!" "Rabi'a ta ce wai kai Maye ne?? uban me za a ci da abin hannunka??"
Ikilima ta ce "To ai shi ne fa, haka kawai ma Mutum ya ciyo wa kansa bala'i don irin waÉ—annan cin abin hannunsu ma masifa ne, sai su yo maka fatalwa a banza" Haja ta ce "Gane min! shi ma bai isheshi ba bare ya bawa wani."
"Ku yi min kyakkyawar fahimta don Allah, kyauta na bayar ba wai don wani abu ba." ya faɗa cikin sanyin jiki, abin nasu yana yi masa ƙuna sosai amma ba yadda zai yi da su sai haƙuri.
"Wallahi Allah zan zazzabga maka mari tinda kai Jaki ne ba ka gane Magana sai duka!!, banza irin matsiyata an gaya maka ba a sonka, kai ba ka isa ba in karɓi abin hannunka, wallahi ka yi kaɗan Ko Ubanka ma Albarka!!, ni ka yi min ƙanƙanta sai dai in da Baban naku za mu kara sai ka je ka turo shi.
"Leelah me ya yi zafi haka? me yasa za ki sako Mahaifina a cikin zancen da ya shafemu??" ya faɗa yana zuba mata idanunsa da suka fara cikowa da ƙwalla, "An sako shi ɗin!! ka yi duk abinda kake ganin za ka iya, banza mara daraja, ni ko a Ɗan aiki ka yi min kaɗan bare Mijin Aure sai dai ka haɗani da Babanka!"
Kafin ya ce wani abu suka yo masa caa!!!! kowa na tsatstsaga kamar tantabarun da suka shekara ba su ci komai ba, sai da suka fige shi tsaf! har da watsa masa ruwan wanki.
Salim da Salma ne kawai ke ƙoƙarin tausarsu suna hanasu duk da shi ma Salim ɗin yakan tofa albarkacin bakinsa, sai dai shi ba zagi ba baƙar magana sai habaici.
Har suka dawo gida Zuciyarsa a dunguzume, idan ya tuna munanan maganganun da suka faÉ—a masa har É—an zabura yake yi, ji yake kamar ya fashe da kuka.
A Parlour suka samu Khushi tana zaune tana Karatu tana ganinsu ta ajiye ta miƙe tana washe baki cikin ƙaguwa da son jin labarin abinda ya faru.
Sai da suka zazzauna Irfan ya ce "Wallahi rashin Mutunci suka kwasa masa masaki-masaki, yanzun haka zazzaɓi ne a jikinsa". da sauri ta koma kusa da shi cikin ɓacin rai ta ce "Ai kuwa indai wani abu ya same shi wallahi duk sai ya same su" Muzaffar ya ce "Ai mun ce za mu ɗauki mataki ya ce a ƙyale su, shi ya sa ni kuma ba zan ƙara cewa komai ba; ni zan zauna wata Ƴar kwalta ta ƙare min zagi ne? ai wallahi ko a mafarki hakan ba za ta faru ba."
Khushi za ta yi magana ta fasa sabida jin ƙarar Paayal ɗin dake ɗaure a ƙafafun Ummansu, cikin hanzari duk suka miƙe tsaye Roshan ya zuba mata idanu yana murmushin farin ciki.
Irfan kuwa ƙasa ya yi da kai ya kasa ko motsawa sabida mugun nauyinta da yake ji.
Baƙin saree ne a jikinta wanda ya sha adon golden, ya yi matuƙar yi mata kyau, hannunta na kan dogon gashinta tana ƙoƙarin ɗaureshi.
Manyan idanunta take rarraba musu tana wani É—an murmushi na gefen baki.
*Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira ÆŠari Uku 300 kacalâ˜ºï¸ Domin Ƙarin bayani 👉🽠09079885632*
*©ï¸INDO*
[11/20, 8:03 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ
*🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
7
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*