← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 35

Sashe 7

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya sa ba wani matsiyacin ba ne" ta faÉ—a tana murmushi cike da jin kanta.
Kiran ne ya ƙara shigowa ta yi saurin ɗauka ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba.
Sallama ya yi mata ta amsa tana ƙara kashe murya, "Don Allah da wa nake magana?" sai da ya ɗan nisa kafin ya ce "Hajjaju ni ne Alin nan? wanda kika bawa aiki kuma ba ki biya shi kuɗinsa ba, Alƙawari bai ce haka ba Hajjaju". wani mashi me dafin baƙin ciki da takaici ne ya soke ƙahon Zuciyarta, sakin muryarta ta yi kamar ba ita ce ta gama karairaya yanzu ba, a hasale ta ce "Uban wa ya baka lambata??, an gaya maka zan ci maka kuɗi ne? aikin banza mutum sai nacin jaraba, ba zan biya ba ma ai guduwa ka yi ba tare da ka kammala aikin ba, da ka san ba za ka iya ba ka ce za ka yi?!" jin sautin murmushinsa ya sa ta zaro ido gabanta ya yanke ya faɗi, "Allah ya sa ba wani Aljanin na nemowa kaina ba" ta faɗa a cikin ranta, har ga Allah abin na shi ya bata mamaki.
"Leelah!!" ya kira sunanta cikin wata irin murya ita ba ihu ba amma sai ratsa ƙwaƙwalwar wanda ya ji ta. Idanunta ne suka ƙara fitowa sarari tsigar jikinta ta tashi bugun Zuciyarta ya ƙara tsananta, "Ina yi da jikina na nemi kuɗi ko yaya ƙanƙantar aiki yake, amma ba zan karɓi kuɗinki ba ko da kin ba ni, ni Mutum ne me girmama na gaba musamman wanda Jininmu ya zo ɗaya!; Leelah na kasa bacci, tin da idona ya sauka akan kyakkyawar fuskarki na kasa samun nutsuwa har sai da na nemo inda zan sameki, amma ina cike da tsoro da firgici don na san Ƴaƴan Masu Kuɗi ba sa saurarar Talaka." "Kutumar uban nan kayyasa!!!!" ta faɗa a burkice, "Kai yanzu kana matsiyaci da kai wanda yake karɓar kuɗi ya yi Gadi shine kake tunanin soyayya da ni?, ka shiga taitayinka wallahi ruwa ba sa'an kwando ba ne! ni na fi ƙarfin Talaka faƙiri irinka ya ce yana sona, duk wanda ya baka lambata ma sai na sa an ɗaureshi!!!" ta ƙarasa maganar tana huci, har ga Allah kawai rufe ido ta yi take masifar nan ba a hayyacinta take ba don ya gama rikita mata lissafi, ita ko kamanninsa ba ta tuna ba kwata-kwata amma sabida shi maye ne wai sonta yake yi.
Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce "Leelah meye aibuna?! Ina neman halak ɗina ne fa ba wai sata nake yi ba, ina nema don na inganta rayuwata da Matar da zan Aura har da ta Iyayena da Ƴar ƙaramar Ƙanwata" ya faɗa yana kashewa Kushi da ke kwance a gabansa ta yi matashin kai da damtsensa ido.

Sai da shiru ya buga wasa na tsawon minti ɗaya ba wanda ya yi magana a cikinsu sannan Leelah ta tattaro duk nutsuwarta ta ce "Malami! ba na son wulaƙanta Mutum, tin muna iya shaida juna ka fita daga rayuwata, ba zan iya Auren wanda sai ya nemo ya kawo za'a ci ba, haba!! ka yi min Adalci mana, na san da Talaka da me kuɗi duk ɗaya suke amma ni ban saba da irin wannan rayuwar Fatara da Talaucin ba, ka nemi daidai da kai ni ma ka barni na Auri ɗan manya daidai da ni." "Leelah wallahi ba na jin zan iya raba kaina da soyaygarki, ki ji tausayina kar Talaucina ya sa ki jefani cikin mugun hali, Zan ci gaba da nema tuƙuru domin na kyautata miki, na yi Alƙawarin ba za ki rasa komai daga gareni ba, don Allah ki faɗa min Inda gidanku yake zan zo na ganki." "Na shiga uku na lalace!!" ta faɗa a cikin Zuciyarta tana kallon ɗakin nasu wanda yake fayau, sauran abokan shawarar tata duk sun fita wajen samarinsu bare su bata abin yi, yanzu dole Zuciyarta ita ce Abokiyar shawararta. "Kin yi shiru!, ko dai za ki ba ni wahala ne kan neman Gidanku kamar yadda kika wahalar da ni wajen samun Lambarki?" "Ina zuwa!" ta faɗa gami da kashe wayar.

nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke yana lumshe idanunsa, zuwa yanzu ya lura akwai ƙaton aiki a gabansa, tsakin da Kushi ta ja ne ya dawo da shi daga Duniyar tunanin da ya leƙa, ido ya zuba mata yana bin ta da kallon tuhuma.
"Ko sayen Mace ake yi kana da Kuɗin da za ka saya amma ka zauna sai Magiya kake yiwa wata Ƴar Matalauta Maƙaryaciya!" "Kushi zan fasa miki baki fa!!, ki dinga ambatonta da girmamawa Yayarki ce ita ma, daga yau Aunty kar na ƙara jin kin faɗi wata banzar magana a kanta!" "Ni ba zan ce mata Aunty ba har sai in ta Darajaka, indai kuwa a ƙasƙance za ta dinga kallonka wallahi ko ka Aure ta ba zan taɓa girmamata ba" ta yi maganar a tsiwace, har cikin ranta haushin Leelah take ji musamman yadda ta ji ta ɗauko hanyar wahalar mata da Ɗan uwa.

*(SADAUKAR!!!... Na Sadaukar da Wannan Littafi nawa ga Aunty HADIZA D AUTA. Ina miƙo gaisuwa da ban girma.*

*Samu Ƴancin karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632*

*©️INDO*[11/19, 10:02 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ

*🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
6

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

FREE PAGE...........

Cikin sauri ta fice daga ɗakin jikinta har rawa yake yi tsabar kaɗuwa, ta fara kasa gane inda kanta yake don kuwa tsaurin idon Aliyu ya yi matuƙar cakusa tunaninta.
Wajen Bishiyar CeÉ—iyar dake tsakar gidansu ta nufa, su Innayi na zaune suna zuba surutu kamar yadda suka saba, Salim, Salma, Baby, Nana, sai Momi.
Tana zuwa ta fara basu labarin abinda ya faru tare da neman shawara, Salim ya tafa hannuwa yana rangaɗa shewa "Ahayyee!!!!, Hajiya Leelah tawa ni ko na Allah, don Allah ki sa Ɗan Buhun Uban nan ya zo Unguwar nan mu yi masa Figar Kazar Kuku, in banda shi sakarai ne ma ai a Matan ma Allah ya yiwa kowa ta shi, ke ai ba ajin Talaka ba ce Auntyna ta kaina!!!, ya ganki kalar Naira ya ƙwallafa rai akan ya zo ya yi soyayya da ke ya ci banza, ƙila ma so yake ya Aureki in kika mutu ya ci Gadon Dukiyarki, wallahi kira shi Ƙofar gidan nan ya gane ke ba ƴar masu Kuɗi ba ce, kuma mu nuna masa mu ba irin Talauci ba ne, kin san Allah ranar zani zan ɗaura in yi ɗamara sai mun yi masa Zagin Tsamar nama, mu shuka masa rashin Mutuncin da har ya Mutu yana girbarsa!!!!" sosai Abinda Salim ya faɗa ya kwanta linkif a Zuciyarta, ba ta ƙara gazgatawa ba sai da ta ji Innayi da Momi ma sun ce haka, daga baya sauran Mutan wajen ma suka goya wa Salim baya.
Yarda ta yi akan za ta ce yazo É—in don haka ta yi saurin komawa ta kira shi.
Lif-lif ta yi da murya ta kwantar da kai kamar ba ita ba, sannan ta ce masa ya zo sai su yi magana, sai da ta bashi full address sannan suka yi sallama, ita kanta har ta ƙagara ranar ta zo yadda za su yi masa rashin Mutuncin kece raini wanda ba zai ƙara marmarin nemar inda take ba.

"Tab gaskiya Shu'uma ce Antin nan taki Khushi, wai ta ce na je Gidansu kuma na san don ta ci Mutuncina ne ya sa ta gayyaceni, na riga na samu labarin yadda suke ketawa Talaka rigar rashin Mutunci, ni ma zan hau layi." "Ni fa ji nake kamar na shaƙeta ta Mutu; duk ta sa ka susuce!" Khushi ta yi maganar har cikin ranta, "Ke! wai ba na hanaki irin maganganun ba? ban hanaki cewar za ki yiwa Mutum abu ba?" "Ka yi haƙuri!" ta faɗa tana murmushi.
ƙwafa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ni kuma dama ai haka nake buƙata, samun lambarta ba zai sa ta yi wani ƙwaƙƙwaran zargi a kaina ba, amma idan na nemo Address ɗinta da kaina dole za ta yi zargina, kin san haka nan Don kin haɗu da Mutum kina Taraba yana Lagos nemar Address ɗinsa zai yi miki wahala indai ba kina da halin yi ba, kin ga kuwa yanzu tinda ita ta kaini da kanta zan samu damar Takura mata hankalina kwance; yanzu za ta gane ni ba irin waɗanda suka saba yiwa rashin Mutunci su kora ba ne, wallahi sai na zamo musu Tamkar Rai shi ne wanda duk jarabar mutum ko'ina aka zagaya ana tare da shi". dariya kawai Kushi take yi don abin nasa dariyar yake ba ta, har ta fara Tausayin Leelah don ta san shi sarai akwai Juriya ta fitar hankali, Yana iya jure yin komai indai har yana son kaiwa gacci akan abinda yake son yi, hakan kuma yana da nasaba da Mugun haƙurin da yake da shi, mara haƙuri kuwa bai iya juriya ba ko yaya aka yi masa abu rashin haƙurin ba zai sa ya jure ba.

Suna gama waya Bilal ya kirata suka ɗora daga inda suka tsaya, shi ne ya mantar da ita Ɓacin ranta akan Aliyu har ta samu ta yi baccin farin ciki, sai dai yana cike da wasu mafarkai wanda ta kasa gane samansu da ƙasansu.

Yau ta kasance ranar Laraba...... Da Misalin ƙarfe 05:00pm suka ba shi ƴancin Zuwa.
Shi kuwa a Unguwar ma yayi Sallar La'asar tare da Irfan da Muzaffar, su a wurinsu abu ne wanda hannu ya iya Ƙafa ta saba, sun saba shiga Unguwanni yawon buɗe ido har da Unguwar da Mota ba ta shiga.
Yau ma gantalinsu suka sha har lokacinsa ya cika sannan suka rabu shi ya yi hanyar Gidansu Leelah su kuma suka ci gaba da baÉ—aÉ—i.

Da yake sanannu ne duk inda ya yi tambaya a hanya ake ɗora shi har Allah ya kawoshi Ƙofar gidan nasu.
Chapter 7 · 0% Book details