← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 35

Sashe 23

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana kwance ya yi bulum! cikin bargo yana ta muzurai, Khushi ta shigo cikin sauri jikinta har karkarwa yake yi, kai tsaye kan gadon ta haye tana kiran sunansa cikin muryarta da ta fara fita daga hayyacinta sabida kuka.
Da ƙyar ya yunƙura ya zauna tare da jingina bayansa a jikin fuskar gado, rinannun idanunsa ya zuba mata yana jin wasu irin allurai na azaba suna sukar Zuciyarsa.
Cikin faffaɗan ƙirjinsa ta faɗa tare da fashewa da wani sabon kukan tana cewa "Roshan Maa ta yi fushi da kai". hannayensa duka biyu ya sa ya rungumota gami da zubawa koɗaɗɗiyar fuskarta ido, Murya a cunkushe ya ce " Na san dole ta yi fushi, amma ba ni take yiwa ba da Haydar take yi; Khushi! Zuciyata tamkar ta ƙone nake ji, ina matuƙar son Leelah, me yasa ta kasa fahimta ta? me yasa ta kasa yarda da ni?, ji nake kamar ba zan iya rayuwa me daɗi ba indai ba tare da ita, ina tsoron na kasa yiwa Salma Adalci idan na aureta, domin Zuciyata da dukkan tunanina ba sa tare da ita."
dogon numfashi Khushi ta ja, ta sauke shi tare da wata zazzafar ajiyar zuciya, cikin muryar kuka ta ce "Zan gayawa Bhaba gaskiya!!, ba zan iya jurar ganinka cikin wannan halin ba!, ko ni da kaina zan iya sama maka farin ciki don ba amfanin wanzuwata a Duniya indai ka rasa shi ina kallo". "Tinda na ce ba za a yi haka ba dole ba za a yi ba, a bakina Bhaba ba zai ji wannan maganar ba, kuma ba na so ya ji a wajenki koda soyayyar Leelah za ta kashe ni; zan iya haƙuri na jure rasata a wannan lokacin amma ina so ki sani ba zan taɓa haƙura da ita ba......."
"Aliyu!!!!!!" Bhaba ya kira sunansa a fusace!!!, a tare zukatansu suka bada bum!!!! duk suka zarowa Bhaba da yake ta huci ido jikinsu na rawa.
ƙarasowa ya yi fuska a murtuke, cikin ɓacin rai ya ce "Dama na san akwai abinda kake ɓoye min Aliyu!!, duk ina Abotar dake tsakaninmu da ka kasa faɗa min gaskiya?? ashe wadda ka ce min ita za ka Aura ba ita kake so ba?, to kana tunanin barinka a cikin uƙuba shi ne mafita??, ashe don haka ka ɓata mana lokaci ka yi zamanka ka ƙi fita ko'ina? ko ba ka san azhar ta kusa ba??, Me yasa kuke son mayar da mu ƙananun Mutane ne?"
Gudun Zuciyarsa ne ya ƙara ninkuwa, girgiza kai yake yi alamar a'a bakinsa na karkarwa, yana son yin magana amma ya kasa.
Khushi kuwa ƙara ɓarke baki ta yi don ta tabbata Bhaba ya ji komai, shi kenan ta faru ta ƙare..............

SHARE FISABILILLAH

*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632*

*©️INDO*[12/6, 11:28 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
15

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

FREE PAGE...........

Neman Duniya an yiwa Haydar babu shi babu labarinsa, ita kanta Maminsa sai da ta fara tsorata don kuwa abin ya wuce Misali. Tin jiya bai dawo Gida ba, duk da hakan ba baƙo ne a wurinta ba amma a yau sai da ta girgiza, har cikin ranta ta yi zaton Maa ce ta sace mata Ɗa, wayarsa an kira fiye da misali amma bai ɗauka ba. Bhaba ya yi faɗa ya yi faɗa har ya gaji, shi dai ya san duk inda ta je ta zo Haydar yana sane ya gudu, kuma ya san ba zai wuce wajen Abokansa na banza ba.

Har ya gaji ya dena kiransa ya tafi wajen Aliyu sai kuma wata Zuciyar ta ce ka ƙara kira.

Haydar yana fitowa daga toilet Alina ta yi saurin miƙewa tana wasu ƴan buntsi-buntsirenta gami da caɓe fuska kamar za ta yi kuka, cikin wata mayaudariyar murya wadda ta san dole sai ya saurareta ta ce "Haydar!! yanzu da gaske Aure za ka yi ka bar ni?, menene abinda ban yi maka ba da za ka gujeni!" ya ɗauka ma in ya juyo zai ga tana kuka sabida yadda ta marairaice murya sai ya gan ta ƙirmisisi.
"Kin san ni ba na ɓoye-ɓoye Alina, na riga na gaya miki gaskiya ni ba son Leelah nake ba, hasalima kawai zan Aureta ne sabi da wani dalili; nema kike yi ki ɓata min rai sai ka ce ke kaɗai ce kika fi sona a cikin Ƴan Matana, kin sani dai jiya da daddare ma wadda ta tayani kwana daban, kin bi kin wani ɗaga min hankali sai kuka kike yi.
kofin da ta gama yin ƴan jiƙe-jiƙenta a ciki ta ɗauka gami da nufar inda yake, miƙa masa ta yi gami da cewa "Dole hankalina ya tashi sabida ni sonka nake yi da dukkan rayuwata, soyayyar ce ma ta sa na banzatar da kowa na riƙe ka kuma na baka dukkan abinda na mallaka a matsayina na ƴa Mace, kar ka manta kai ne Namijin farko da na fara haɗa shimfiɗa da shi, kai ne ka buɗewa duk wani Namijin da nake mu'amala da shi hanya, soyayyarka ce ta jawo min, na san indai ka yi Aure dole za ka rage saurara ta, za ka iya mantawa da ni ma; kar ka za ta ban yarda da kai ba ne, na san rayuwar za ta iya canjawa". ɗan tsagaitawa ta yi kafin ta ci gaba da cewa " na ga kamar ranka ya ɓaci, karɓi wannan ka kora". karɓar kofin ya yi yana zuba mata ido, tausayinta ya ɗan kama shi kaɗan, sai dai ba zai iya yarda ya yi asarar damarsa ba.

A hankali ya kafa kofin a bakinsa, zai fara sha kenan idonsa ya sauka akan wayarsa da ke kan drower tana kawo haske ita kaÉ—ai.
Sai da gabansa ya faɗi da ya tuno Daddynsa, miƙa mata kofin ya yi kafin ya nufi wajen wayar ta shi, cikin sauri ya ɗauki kiran gabansa na faɗuwa.
Rai a ɓace Bhaba ya ce "Ka kyauta Haydar!, ka yi min abinda ka saba, ka muzguna min hankalinka ya kwanta". "Me na yi to Dad??!" "Ba abinda ka yi, na san ba a hayyacinka kake ba ba ka san ƙarfe nawa ba ma yanzu, maza duk inda kake ka kama hanya ka tafi wajen Ɗaurin Auren nan iya ƙaramtar da muka yi ta isa haka Aure kuma ba fashi sai an ɗaura shi ko kana so ko ba ka so". yana gama faɗen haka ya gimtse kiran, zazzafar iska ya furzar gami da lumshe ido, komai ya zo masa da sauƙi don har ga Allah ya ɗauka zai ce masa ya Aurawa Aliyu ita.

Watsar da lamarin Alina ya yi duk da tana ta kai kora da matse lamba, cikin gaggawa ya shirya ya tankaɗo ƙeyarta suka fito tare sannan ya yi hanyar Gidansu.
Ya sha faɗa wajen Mami duk wanda Bhaba ya yi mata sai da ta kusa juyewa a kansa, ransa ya ƙara jagulewa sai ya ji ma gaba ɗaya ya tsani Leelah don ita ya ɗorawa Alhakin komai.

Wani matsanancin kuka ne ya kufce masa, ya shiga rusa abinsa kamar ƙaramin Yaro, sai a lokacin ya iya buɗe baki ya ce "Bhaba ba ita ba ce!, ita har yau ta ƙi karɓar soyayyata, ga shi lokaci ya ƙure Abbi ya ba ni zaɓi biyu, ba yadda na iya shi ya sa na ce zan Auri Salma" "Amma da ka faɗa mana gaskiya ai ka san za mu ara maka lokaci, wai me ya sa ma ba za ka gaya wa Yarinyar gaskiya ba?" "Bhaba ka ƙyaleta kawai, yanzu tayar da maganar nan ma ɓacin rai ne ga Abbi, don Allah kawai a yi komai yadda ya sawwaƙa.
"Roshan yana da gaskiya!!, abinda ya zaɓa kenan kuma shi za mu yi masa!" muryar Maa ce ta karaɗe kunnuwansu, sosai Roshan ya ji daɗin zuwanta.
Bhaba kuwa takaici ta ƙara masa, "Yanzu ɓacin rai shi ne abin so? ki duba ki ga halin da yake ciki fa!!" ya faɗa cike da takaici, murmusawa ta yi kafin ta ce "Ka shirya Roshan! lokaci yana ƙara ƙurewa; Jaan!! abu indai kana son shi koda yana yi maka ɗaci haka nan kake jurewa, a fannin soyayya ne wannan, tana buƙatar nutsuwa, don Allah ka dena damuwa akan komai, ka cika masa muradinsa kawai".
jinjina kai ya yi kafin ya ce "Shi kenan, mu za mu yi gaba sai ya tawo daga baya".
Har ya kusa ficewa daga ɗakin Maa ta tsayar da shi da cewa "Wani hanzari ba gudu ba!! kar da ka manta kai a ɓangaren Haydar kake, kuma ka sa a ranka ba ka haɗa zuri'a da Aliyu da Mutanensa ba!"
Jinjina kai ya yi sannan ya fice.
Sai da Maa ta yi da gaske sannan ta rarrashe su daga shi har Khushi É—in.

Sai da aka yi sallar Azhar sannan aka É—ora da ÆŠaurin Auren, na Haydar aka fara yi sannan aka É—ora da na Aliyu.
Ana kammalawa kowane ɓangare suka watse saniba gudun masu ƙyarto, a hakan ma wasu sun fara gano usulin kamar da ke tsakanin Alhaji Mustafa Naira da Aliyu, abin da ya sa ma waɗanda suka san Aliyu ba su yi saurin ganewa ba shi inkiyarsa daban, Me Sanyi aka fi kiransa, ba kamar Haydar da duk inda ya zagaya da Inkiyar Daddynsa yake amfani ba.

Hankalin Leelah ya kwanta saɓanin Da da ya miƙe tsaye, sabida jinkirin zuwan Ango, da ta ji an ɗaura Auren kuwa sai farin ciki ya turnuƙeta ta kowanne fanni.
Salma kuwa sai hankalinta ya ƙara tashi, gashi yamma ta doso lokacin da za a tsigeta daga gaban iyayenta yana ƙara kusanto ta.
Chapter 23 · 0% Book details