Sashe 19
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin shiru ya sa Abbi cewa "Ka yi shiru kuma?" cikin sauri ya ce "Ita ma Gidansu ɗaya da wadda Haydar zai Aura sunanta Salma". "Haɗa baki kuka yi za ku Aure Ƴan Gida ɗaya kenan?, to Allah ya tabbatar da Alkairi; anya kuwa ba da kaina zan je nema maka Auren ba?" ya faɗa yana dariya, cikin sauri Aliyu ya ce "A'a! tab!! wallahi ban yarda ba, ba za ka je ba". "To sabida me?" sai lokacin ya ankara da kwakyarar da ya kusa yiwa kansa, sassauta murya ya yi ya ce "Abbi tana da kyau ne sosai, ba na so ka ganta ka ƙwace min, waɗanda za su je ɗin ma sai na zaɓa don ba na son harkar snatching."
Abbi ya yi dariya yana cewa "Allah ya shiryeka Abokina!, ai idan ma ban ganta yanzu ba ko ka Aureta zan iya yi maka Alqunut ka saketa; to ba komai duk yadda ka tsara sai ka faÉ—awa Abban naku zan ji daga gare shi."
dariya ya yi gami da cewa "Na fi yarda da hakan, sabida na san ba za ta soka ba indai na riga na Aureta, na gode Abbi, bari in gudu" ya faɗa tare da miƙewa tsaye, "To ba za ka tsaya ka ga Uwar Gidan ba?" "Oh! zan biya sashinta in mun gaisa sai na wuce.
"To Allah ya tsare.
lokacin da ya amsa har ya yi tazara a tafiyarsa.
Ko zama bai yi ba a ɓangaren nata suna gaisawa ya fice cikin sauri-sauri, ya ƙagara ya koma gida ya ɗan samu nutsuwa tin kafin kansa ya yi juyewar da ba zai iya gane ko'ina ba.
Yana shiga ya fara ƙwalawa Khushi kira "Farinciki!!! Farin ciki!! Farin ciki!!!!"
A firfice ta farka daga baccin wahalar da ya É—ebeta tana zazzaro ido.
Har zai wuceta ta É—aga murya ta kira sunansa, juyowa ya yi yana kallonta, ganin yadda ta yi wani kozai-kozai ya sa gabansa ya sake faÉ—uwa.
Kusa da ita ya ƙarasa ya zauna yana tsira mata ido, ita kuwa sai lumshe nata idon take yi tana langwaɓewa. Ya san tana cikin damuwa amma bai bi ta kanta ba ya fara da cewa "Khushi Abbi fa ya ce zai yi min Aure nan da sati uku, kuma kin san Haydar wadda nake so zai Aura, ban san ya zan yi ba, anya kuwa ba guduwa zan yi na bar Ƙasar nan ba?" wararo masa idanu ta yi kamar ba ita ce me nuna jin bacci ba, cikin kaɗuwa ta ce "Kya matlab?" ɗan ƙaramin tsaki ya ja kafin ya ce "Wai ba kin ji abinda na ce ba? Leelah ita ce wadda aka gama maganar Aurenta da Haydar jiya". "Amma shi Haydar ɗin ya san ita kake so ya yi haka? wallahi Allah sai na yi maganinsa, sai na yi masa abinda Auren ma zai fita daga kansa" ta faɗa tana huci.
Cikin yanayinsa na sanyi ya ce "Ba na so!, inda zan yi hakan da na faɗawa Abbi gaskiya, ko kuma in faɗawa Bhaba, ki rabu da shi kawai, ko ya Aureta dolensa ya saketa indai ba ta shi ba ce." kwantar da kai ta yi kan kafaɗarsa gami da sauke wata marainiyar ajiyar Zuciya, a sanyaye ta ce "Roshan Bhai!, na kasa mantawa da Azaan sai tunaninsa nake yi". idanunsa ne suka ƙara girma ya zazzaro su a kanta, "Kina tunanin Azaan?, wai ma ina kika je yau? ina ta so in tambayeki sai na yi karo da abinda ya fi ƙarfina, wai ba na hanaki zuwa wani wurin ba tare da izinina ba? kuma ma ke kaɗai ba tare da kowa ba." "Ka yi haƙuri, na raka Suhailat ne za su haɗu da Saurayinta, ni ma a can na haɗu da Azaan, kuma wallahi ba ni na nemeshi ba, ina cikin shan ice cream sai na ji muryarsa, na ɗauka ma haukacewa na fara yi" ta faɗa kamar za ta yi kuka, "To me ya yi miki da kike tunaninsa?" jim!! ta ɗan yi kafin ta ce "Ya ce yana so na ne amma na ce masa ni ba na son shi; na kasa samun kwanciyar hankali na kasa tunanin komai sai shi". jinjina kai ya yi gami da cewa "Tab! to ki nemi tsari da shi tin kafin ya fara burkita tunaninki, kin san in Maa ta ji labarin nan sai ta datse miki harshe ko?" sharr!!!!! ƙwallar da ta cika idanunta ta samu damar silliɓowa, "Na san faɗa za ta yi shi ya sa na tsorata, ina ga Asiri ya yi min shi yasa ma na kasa mantawa da shi!!" duk da halin da yake ciki sai da ta bashi dariya, sai da ya yi me isar shi sannan ya miƙe yana cewa ''Ki wuce ki kwanta ki bar labarin nan, ni bari na je wajen Maa". da kai ta amsa masa tare da zamewa ta ƙara kwanciya.
Tana tsaye kamar taɓarya, hannayenta goye a bayanta.
Ƙarasawa ya yi kusa da ita yana cewa "Maa tsayuwar me kike yi haka? na ɗauka ma kin yi bacci?" "Kawai ina nazari ne." ta faɗa tare da komawa ta zauna kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon.
Hannu ta miƙa masa gami da cewa "Ajao Beta!" hannunsa ya ɗora kan nata sannan ya zauna kusa da ita. "Akwai wani abinda za ka faɗa min ne?" gyaɗa kai ya yi gami da cewa "E, Yanzu daga wurin Abbi nake, ya ce zai haɗa Auren mu da Haydar, amma ba wannan ce matsalar ba wadda nake so ɗin ashe ita Haydar zai Aura, kuma har an riga an gama magana". Wani shegen kallo ta zuba masa tamkar shi ne me laifin, "Ai kuwa koda ɗaura Auren aka yi sai an warware shi, ba zan lamunta ba!" "A'a Maa, ni dai ba na son duk abinda zai zamo ɓacin rai, ki barshi kawai amma fa koda ya aureta ba zan fitar da rai ba, don ba domin Allah ya Auretan ba, na cewa Abbi zan Auri wata ƴar gidansu, kawai shi kenan a wuce wajen, kuma har yau ina kan bakata sai na koyar da Leelah darasin rayuwa ta yadda ba ta zata ba, don Allah Umma ki yarda da ni, haka nake son yi yanzu". numfasawa ta yi kafin ta ce "Na yarda da hakan, amma a bisa sharruɗaina, muddin ita ma za ta wulaƙanta ka ne kamar yadda Ɗayar take yi maka to fa zan yi abinda ba a so ɗin, koda ka Aureta indai za ta ɓata maka rai ni ma zan ɓata nata." gyaɗa kai ya yi yana cewa "Ni ma na yarda, na san ma hakan ba za ta faru ba in sha Allah; Kawu Mahmud da Abban Irfan da Kawu Rabi'u su nake so su je a yi maganar, don ba na so su san ina da wata alaƙa da Bhaba ko Abbi ko shi kansa Haydar ɗin." mayar da duk mutsuwarta ta yi kansa tare da tambayarsa "To ta yaya kenan? ka san dai in Mutum me hankali ne da zarar ya gansu ya ga sitturunsu zai bawa kansa amsar suwaye ba sai ya tambaya ba." "Irin shigar da nake yi su ma ita za su yi, shi ya sa na zaɓi su Kawu Mahmud na san su kaɗai ne za su iya biyewa shiriritata" ya faɗa yana dariya.
Ganin yana fara'a ya sa hankalinta ya ɗan kwanta, duk da wani gefen na Zuciyarta na ƙara tunasar mata irin rashin Albarkar da Leelah ta yi masa, ga kuma Hajiya Habiba da take shirin tarwatsa masa rayuwa.
Shirya mata yadda komai zai tafi ya ci gaba da yi tana ƙara tunzura shi, tin ba ta saki jiki ba har ta saki ranta ta fara dariya don kuwa wani abin na shi sai ya sa Mutum dariya ko babu shiri.
Kamar yadda Aliyu ya buƙaci a lulluɓewa Bhaba gaskiyar maganar hakance ta faru, ba wanda ya san abinda ke faruwa sai Roshan, Khushi, Maa, sai ɓangaren Haydar da waɗanda suka sa shi.
Bhaba ya so tirjewa a kan sai an je da shi Neman Auren Maa ta yi fir ta ƙi amincewa, ya so fahimtar wani abu a ciki amma sai suka ƙara baibaita lamarin dolensa ya haƙura don ya san rigimar Maa.
Zama ya yi ya tsara wa su Kawu Mahmud duk yadda za a yi kuma suka Amince masa. Irin yadinsa me matuƙar arha ya sayo ya ya sa aka ɗinka musu su saka ranar da za su je. Kawu Mahmud ne ke taya shi yin komai da tsatstsarawa har da irin jirgawar da za a yiwa iyayen Yarinya.
Kwana huɗu kenan da tsayar da maganar Haydar da Leelah. Su Baba na zaune a ƙofar gida suna hira su Kawu Mahmud suka iso. Sallama suka yi musu, suka amsa a Mutunce gami da yi musu bismillah su zauna.
Zama suka yi aka ƙara gaggaisawa kafin Abba ya ce "To! to! to! kuna tambaya ne bayin Allah?" Kawu Mahmud ya ce "A'a mun zo wajenku ne." "Allah ya sa dai lafiya" Baba ya faɗa yana gyara zamansa.
Kawu Mahmud ya faɗaɗa murmushinsa kafin ya fara da cewa "Lafiya ƙalau sosai ma kuwa, ku yi haƙuri mun zo muku kai tsaye kuma mun zo da babbar magana, idan an bamu dama sai mu faɗa." "A'a ba komai, ku faɗa mana muna saurarenku" Baba Jamilu ya faɗa yana saita zamansa don jin me ke tafe da su ɗin.