Sashe 20
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bayanin abinda ke tafe da su suka yi musa, da cewa Kawu Mahmud shi ne Mahaifin Aliyu, lafiyayyen bayaninsu ya bayar kamar yadda suka tsara, daga baya ya kora musu da cewar sun zo nema wa Aliyu Auren Salma ne.
Baba Habu yana shirin cewa sai sun yi tunani a kai Baba ya ga ba fa'idar hakan tinda Yaron an riga an san shi, don haka ya ce sun Amince, duk ranar da aka shirya kawai a zo a yi maganar Aure.
Godiya sosai su Kawu Mahmud suka yi nan aka ƙara caccafkewa.
Baba Usama ne ya kawo shawara akan a haÉ—a bikin rana É—aya da na Leelah in har iyayen Aliyun sun shirya. Dama abinda suke nema kenan, nan kuwa suka yi caraf da zancen suka amsa.
Haka aka ajiye magana an riga an haɗe Auren da na su Leelah, har su Baba sun faɗi Sadaƙin da suke so.
Haka suka tashi daga zaman kowa abin ya yi masa daÉ—i.
Ta ɓangaren su Baba ma ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, addu'arsu ɗaya Allah ya tabbatar a yi su huta da Gore-goren Mutane na cewar sun tara Ƴaƴa sun ƙi Aurar da su.
Koda maganar ta shiga cikin Gida babu wanda bai yi mamakin jin ta ba.
Haka aka dinga cira zancen kamar sun samu nama.
Wasu sun yi wa Salma murnar samun Miji, wasu kuwa baƙin ciki suke tayata don gani suke yi ita ba tsararsa ba ce, don dai ma ita ba halinta ba ne mugun son Duniyar nan.
Hankalinta ya yi bala'in tashi, haka ta dinga kuka tana cewa ita fa ba ta son shi ba za ta aureshi ba tinda Ƙanwarta yake so.
Sai da Baba Habu ya yi mata nasiha gami da nusar da ita ya kwantar mata da hankali sannan ta Amince kuma ta saduda ta manta da komai, ta ƙarɓi ƙaddararta da hannu bibbiyu.
SHARE FISABILILLAH
*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira ÆŠari Uku 300 kacalâ˜ºï¸ TuntuÉ“i Lambar Waya👉🽠09079885632*
*©ï¸INDO*
[11/30, 6:53 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
13
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
F-P..........
Tin daga ranar aka fara shirye-shirye ta ko'ina ba kama hannun Yaro.
Maa ma ta tashi tsaye tana shiri tuni ta gama yaÉ—awa Danginta da Abokan Kasuwancinta.
Ta ɓangaren Bhaba ma ba zama, yanzu ya fi mayar da hankali akan shirye-shiryen Auren fiye da Kasuwancinsa. A ɓangaren su Momi da su Baba Habu ma kowa ƙoƙarin yadda zai rufawa kansa Asiri yake yi, musamman Baba Habu shi da babu wanda zai yiwa Salma kayan Ɗaki sai shi.
Roshan kuwa yana cikin tara ahu, sai dai ba ya nuna wa kowa damuwarsa, a zahiri fara'a yake yi sosai, amma idan ya keɓe har zazzaɓi yake yi. Khushi ce kawai ta san halin da yake ciki, duk ta bi ta rikice ba ta walwala ko kaɗan.
Ana saura Sati ɗaya bikin Maa ta tafi India don ƙara yin wani shirin. Ba don Aliyu take yin wani abun ba sai don Salma wadda ta amince ta jingine farin cikinta ta karɓe shi, hakan ya sa ta samu kyakkyawan gurbi a Zuciyar Maa, kuma ta sha Alwashin yin komai domin ta faranta mata.
A fannin su Leelah kuwa abin sai wanda ya gani.
A memakon ta kame kanta sabida an riga an yi Baikonta sai ta ƙara tashi tsaye wajen Yaudarar Samari da aske musu Aljihu kamar yadda Momi ta tsara mata, a cewarsu a nan za su haɗa kuɗin da za su yi duk wata burga da bajinta.
Shi ma Baba Usama gorin da Momi ke yi masa ya sa shi fafutukar neman kuÉ—i ta ko'ina, duk inda ya je neman bashi sai a hana shi sabida kowa ya san ba shi da sana'ar ma bare a sa ran zai samu wataran ya biya.
Sai da kyar ya samu wani Alhaji ya ce zai dinga yi masa gadi sannan ya ba shi rancen kuÉ—in, in lokacin biyansa ya yi sai ya cira a kuÉ—insa da haka har su fanshe.
Haka nan ya amince duk da yana ganin kamar ba zai iya aikin ba amma a wannan karon ba yadda zai yi.
A ɓangaren su Salma, kuɗin da take tarawa na Wanki da Gugar da take yi su Umma ta ciro ta yo mata ƴar sayayyar kayan Kicin, su kofi su robobi da ƴan filetai da sauransu, sai fannin ɗan turaren wuta da Humra.
Sai Dilka da Leelah ta dage sai an yiwa Salma kamar yadda ita ma aka yi mata. Da farko Salman ta ce ba ta so sai da ƙyar suka shawo kanta ta yarda sannan aka fara ɗan mulka mata.
Ba laifi abin ya karɓe ta fatarta ta canja sosai, sai dai ba wani can ba don kayan haɗin Dilkar ma ba wasu na kirki ba ne.
Leelah kuwa ta ƙara zama kamar balarabiya ta ƙara ja ta yi sulɓi sai ƙyalli take yi, ita da yake abin nata ya shafi tsadaddun sabulai da mayukan bilitin.
Su Sumayya da su Rabi'a ma an tashi tsaye ana shirin yadda za a samu samari a bikin, a cewarsu a wani wurin ma sun nema bare abu ya zo gidansu.
Su Rabi'a har da Mama ake yin shirin, ta ciyo bashika su ma sun tara na samari an zo ana shirin abubuwan bajintar da za a yi.
Kowa ya zuba ido ya ga yaya Baba Habu zai yi wajen yiwa Salma kayan É—aki. Sai dai abinda ba su sani ba me Zuciyar yi Allah ba ya hana shi.
Yau Biki ya rage saura kwana biyar. Gidan tuni ya fara zama gidan biki, waɗancan su shigo waɗannan su fita. maƙota sai gangankon zuwa ganin Leelah ake yi don labari ya zagaye ko ina Ɗan gidan Alhaji Mustafa Naira za ta Aura.
Ita kuwa sai yauƙi, iyayi, kwainane, ƙafafa, fasa kai, fariya, duk ta haɗa wuri ɗaya.
Salma kuwa wasu kiranta suke yi kyakkyawa Matar Talaka, ita ma labari ya zagaye ko'ina cewar wani faƙiri za ta Aura. Sam abin ba ya damunta don ta sa a ranta kwanciyar hankali kawai take buƙata ba kuɗi ba.
Yau ana zaune sai ga Mata kici-kici da Akwatuna ba zato ba tsammani sai ganin su aka yi sun shigo.
Momi ta yi matuƙar jin haushin bazatar da suka yi mata, don ta so ta yi musu abin da za ta burgesu, wani abin da ya ƙara dugunzuma Zuciyarta ganin shegen kallo na banza da wofi da raini da suke jifansu da shi daga gidan har Mutanen cikinsa.
Kowa na gidan abin ya taɓa Zuciyarsa don ba sa son raini kwata-kwata. su Sumayya har sun fara shirin mayar da raddi suka fasa sabida akwatunan da aka gama shigo da su gabaki ɗaya suka canja musu lissafi.
Saiti biyu ne masu guda huɗu sai ƴar ƙarama, in an haɗa duka Takwas kenan har ƴan ƙananun goma.
Tuni kowa ya fara santi da sambatu akan lefen. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da Mata ana ta shewa da guɗa gami da yiwa Momi da Ƴarta kirari.
Ƴan kawo lefe kuwa ana gama shigo da su ko zama ba su yi ba suka juya suka bar musu gidan.
Hakan bai dame su ba su dai kawai sun ci gaba da Shagalinsu.