← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 35

Sashe 2

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MC Kuwa tuni ya ƙara ruɗa wajen da surutai kamar wanda aka yiwa allurar hauka.

Tattausar ajiyar Zuciya ya sauke wadda ta kusa tawowa da hawayensa, shi dai ya san Ba dai Abokinsa ya ba shi Kunya ba.
Kai tsaye wajen Irfan wanda yake binta da ido ta nufa, sai da ta isa gabansa sannan ta saki murmushin da ya ƙara bayyanar da ainahin kyaunta, cikin zazzaƙar muryarta ta ce "Ka yi haƙuri Yayana yana Uzuri ba zai samu zuwa ba." "Ba komai, iya ganinki da na yi ma ai ya biyani, ki temaka mini ki yiwa kowa bayanin abinda ke faruwa don kuwa duk wurin nan shi ake jiran gani." nisawa ta yi kafin ta yi magana cikin yanayin shagwaɓa "Ka san ba na son sa idon Mutane Irfan Bhai" "Na sani temaka mini za ki yi Chotti Bahen" ya yi maganar yana kwaikwayon tata maganar har da shagwaɓar, dariya ta yi kafin ta ce "To ka rakani sai ka fara gabatar da ni." amsawa ya yi sannan suka nufi wajen da MC yake.

Leelah da ke tsaye ta riƙe Ƙugu wani baƙin ciki ya tokare mata Zuciya, ita da take shirin cusawa Irfan Soyayyarta ya ƙi saurararta sai wata me jan kunne. Ali ne ya dubeta kafin ya ce "Hajjaju a zauna mana" "Kai ba zan zauna ba" ta faɗa a masife, ya yi dariyar Yaro ba Mutum ba sai ya girma kafin ya ci gaba da sa hankali akan Irfan da Ƴar Indiyarsa.
Bayan ta gabatar da Uzurin Yayanta ta bayar da kyauta tana shirin miƙawa MC Microphone Azaan ya dakatar da ita ta hanyar tare mata hanya yana binta da wani shegen kallo da babu komai a cikinsa sai zallar ƙwalama gami da iskanci.
"Me ya sa za ki fito a irin wannan daren??, 11:37PM fa ai na ɗauka Mamarki ba ta barinki gantali yadda kike da tsaurin halin nan." Dakakkun idanunta ta watsa masa kafin ta ce "Ba ruwan wani da lokacin fita da shigata, bani hanya." "Ba za ki wuce ba har sai kin bani amsar tambayoyina, ko kuma daga nan in wuce da ke guest house ɗina mu kwana tare.... Tasss!!!! ta wanke shi da wani kyakkyawan Mari me ratsawa har cikin ƙwaƙwalwa. tuni wurin ya ɗau ihu da shewa don kuwa abin ya burge Mutane tamkar a film suke kallonsu.
Azaan kuwa jin ana yi masa dariya ya ƙara fusata shi, sauke hannunsa ya yi daga kan kumatun yana cewa "Ni kika mara???" cikin ɗaga murya ta yadda har Microphone ɗin yana amsawa ta ce "Na Mareka How dare you!!!!" shu'umin murmushinsa ya saki ba tare da ta ankare ba sai jinta ta yi a cikin ƙirjinsa ya yi mata wata muguwar matsa, ta buɗe baki za ta yi magana ya rufe bakin nata da nasa, sai da ya kai a ƙalla 3 minute yana kissing ɗinta sannan ya saketa yana ƙara wararo mata tsayayyun idanunsa.... ita ma kallonsa take yi ya yinda Zuciyarta ke wata muguwar tafarfasa...... gefen mayafinta ta sa ta goge bakinta hakan bai wadatar da ita ba don haka ta taƙarƙare ta ƙwalla ihun cewa "Rochaaaan!!!!!!!!!" Sai da kowa na wajen ya firgita, aka ƙara zazzaro ido ana kallonsu, Azaan kuwa sai da numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya ci gaba da gudana, Idan ya tsaya jayayya da kansa ma akan cewar bai tsorata ba ya ɓatawa kansa lokaci, tuni zuciyarsa ta fara bada Darrr!! darr!!!!! tana tsalle. Ba ihunta ne kawai ya tsorata shi ba jin sunan da ta ambata.............

*PAID BOOK, 300 ONLY*

*INDO*
[11/19, 10:00 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ

*🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
2

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

.........Zuwa yanzu ya gane dole akwai wata ƙullalliya.

Cilak!! ya ɗauketa gami da rungumeta tsam a cikin faffaɗan ƙirjinsa, cikin gaggawa ya nufi hanyar fita.
Da ido Azaan har ma da Irfan suka raka shi Zukatansu cike da saƙe-saƙe da mamaki iri-iri.

Leelah ɗoki da son ganin abinda ke faruwa a gabanta ya sa ta yi saurin juyawa don ta karɓe ƴar jakarta daga hannun Bodyguard ɗin nata ta turmutsa gaba. Turus! ta tsaya ganin babu shi babu alamunsa sai Jakarta tata a kan Kujera. Ɗan ƙaramin tsaki ta yi kafin ta ɗauku jakar ta shiga cikin jama'a wanda suka yi cako-cako suna kallon lamarin me kama da wasan kwaikwayo.

Sai da ta yi Free sannan ta ji wasu na cewa ai ya ɗauketa sun fita, wasu kuma suna mamakin ashe Aliyu Naira Yazo to me yasa ya ɓoye kansa?.
Takaici da baƙin ciki duk ya isheta, gashi ba ta ga dramar da aka yi ba ba ta ga Aliyun da ake ta faɗe ba, gashi Bodyguard ɗinta ya tsallake ya barta.

Sai da suka dangana da Tsadaddiyar Motarsu sannan ya direta. Dama jira take yana direta ta tirji ƙasa ta juyo kansa a masife ta ce "Dama abinda ka ɗaukoni a yi min kenan??, ka ɗaukoni ne don a tozartani a ci zarafina a idon Duniya?? ; wallahi sai na ɗauki mummunan mataki akan Azan ɗin nan! har shi Irfan ɗin" "Ki yi haƙuri Khushi! da na san Azaan zai zo wajen nan kin san ko ni ba zan zo ba bare na kawok....." katse shi ta yi cikin tsawa "Ka sani mana!!!! babban me laifi kai ne!!, in da ba ka ɗaukoni ba babu wanda zai wulaƙantani, kuma kana kallo amma ko ka yi magana, sai da ya tuntsirar min da madarar Mutuncina!!!." kamar zai yi kuka ya ce "Ba haka ba ne, ki dena ganin laifina..." "Kai ne fa ka haɗa Taron nan! kuma akan me za ka ce ba ka san wanda zai zo ba??" zuwa yanzu ɓacin ransa ya ƙara ninkuwa fiye da Da, tabbas da me saurin hannu ne ba abinda zai hana shi sharara mata maruka ko za ta dawo hayyacin.

Sai da ta gama figeshi tsaf sannan ta zumɓuri baki ta shige Mota, ƙaratan Mazan da suke taka mata baya ma suka shiga. Ɗaya a mazaunin Direba ɗaya a wajen ɗan zaman banza.
Jiki a sanyaye ya ja ƙafafunsa da suka fara nauyi ya shiga Motar.

Cikin mutsuwa Direban ya fara ja suka hau Titi.
Ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya dubeta cikin Muryarsa me matuƙar sanyi da sanyawa me sauraro nutsuwa ya ce "Sai Faɗa kike yi min akan laifin da ban aikata ba Kuchi!!, ko Irfan bai cancanci wannan hukuncin ba, na baki haƙuri kin ƙi haƙura, na gaya miki ba ni da laifi kin ƙi yadda, Kaise!?" faɗawa ta yi jikinsa gami da fashewa da matsanancin kuka tana cewa "Meine vah nahi pyaar karthi hoon wallahi!"
Bubbugar bayanta ya shiga yi cikin sigar rarrashi ya ce "Mujhe bahoot khed hai Kushi!"
banza ta yi masa ta ci gaba da rera baitin kukanta wanda yake ƙara soya masa Zuciya.

Waya ya É—auka ya tura kira cike da sa ran wanda ya kira É—in ya É—auka.........

"Gaskiya ba ka kyauta min ba Azaan, me yasa indai aka haÉ—a lamari da kai sai ka tarwatsashi sabida Allah?" Irfan ya faÉ—a cikin rauni tamkar zai fashe da kuka.
A gadarance Azaan ya ce "Ina ruwanka? kai na yiwa??" "Amma ai tarona ne ko??, ni na tara Mutane kuma ka zo ka tozartani, wallahi Allah kar ka ƙara yi min irin wannan; in banda Akuyanci irin naka a bainar nasi za ka dinga haiƙewa Yarin......." a tsawace ya ce "Dalla ina ruwanka ne Ɗan Iya!!!?, she's my sister and my wife, to meye naka a ciki? Faɗan cikin gida ne idan na ƙara jin bakinka a ciki wallalhi sai na saɓawa Tunaninka; Idiot!!!!!!!" yana kaiwa nan ya doka wani lafiyayyen tsaki ya nufi hanyar fita, tawagarsa suka rufa Masa baya.

Da ido Irfan ya bi shi Zuciyarsa na wani irin tsalle gami da turiri. Sai a lokacin ya ji ihun da wayarsa take ta zurmawa, jiki a saɓule ya ɗauki kiran tare da yin shiru don bai san da wace kalma zai fara yi masa magana ba........ "Ban zaci haka ba Irfan!, ka san ko hanya ba na haɗawa da Azaan don me za ka gayyace shi Taron da ka san zan zo??, ka ga yadda ya tsinka igiyar Mutuncin gidanmu akan idon Duniya; ni wallahi yanzu damuwata ma idan Umma ta sani komai akanmu ni da kai zai ƙare, Yanzu ga wannan ita ma sai jaraba take yi min ga kukan Masifa, haka za ta dinga tijara har sai ta sa wanda bai sani ba ya sani; ka dena irin wannan, gwara kawai ka ce min kar na zo zai fi sauƙi akan wannan tozarcin da ka yi min!." sai da ya kai matsaya sannan Irfan ya numfasa, a sanyaye ya ce "Wallahi da ka san irin suyar da Zuciyata ke yi da ba ka zargeni a kai ba, ni ma fa Kushi Ƙanwata ce , in aka tozartata tamkar ni aka tozarta bare kuma a ce a Taron da ni na haɗa shi; na yi masa magana kuma ya ce kar na ƙara shiga zancenku na cikin gida ne, to yaya zan yi??" "Amma ai ka san zan zo me yasa za ka nemeshi??" "Na rantse da Allahn da raina ke hannunsa ba ni bane Roshan!, Ari ne ya gayyatoshi wallahi." tsaki ya ja kafin ya ce "Ta tabbata sai na ci Uwar Arin nan kenan!, Yanzu indai Umma ta sani duk wata ƙura akanmu za ta ƙare wallahi" jikinsa ne ya ƙara yin sanyi luɓis, cikin karyewar Zuciya ya ce "Roshan ba zan yi haka da gangan ba wallahi, Ina matuƙar Sonta kuma ina Matuƙar Kishinta na fika jin zafin abinda ya yi mata wallahi Roshan!!" "Me??? Irfan wai Kuchi ɗin?!!" cikin kaɗuwa ya jefa masa tambayar, kasa magana ya yi sai gyaɗa kai kawai da ya yi, da zarar ya yi magana zai iya rushewa da kuka don haka ya kashe wayar ya mayar da ita muhallinta.

Haka Taro ya watse kowa na tofa albarkacin bakinsa, da yawansu cewa suke yi dama abin bai tsaya iya nan ba, don kuwa su burgesu aka yi.
Chapter 2 · 0% Book details