← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 35

Sashe 32

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136

*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632*

*©️INDO*
[12/13, 11:53 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
20

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

Azaan, yana zaune kusa da ƙafafun Mammi ya ɗora kai a kan cinyarta yana ɓarza kuka kamar wanda bincike ya tabbatar masa gobe zai Mutu. "Mammi wannan ne karon farko da kika kasa samar min farin cikina, Aliyu da Haydar kowa ya samu abinda yake so amma ni kin gaza yi min komai, yanzu fa Khushi ko ganinta ba na samun damar yi sabida Aliyu ya ƙara ninka tsaro a kanta". shu'umin murmushinta wanda ba a iya fassara shi ta saki kafin ta ɗora hannu kan kwantacciyar sumar kansa ta fara yamutsa ta gami da shafawa, cikin maganarta me cike da gadara ta ce "Kar ka ga kamar ban damu da kukan nan naka ba Arjun!, yana matuƙar taɓa Zuciyata kuma yana ƙara tunzura ni bisa cimma wani ƙuduri nawa wanda ke lulluɓe a cikin naka Ƙudurin; kai ma ka kusa mallakar naka farin cikin, kwanan nan zan kawo maka Khushi har Ɗakina a matsayin kyautar da zan yi maka ta Birthday, na yi jinkiri ne kawai sabida Uwar su ta wuce duk yadda kake tunani, amma lokacin kukanka ya zo ƙarshe".
Kuka ya ci gaba da yi yana bayyana mata irin tunani barkatai da yake yi akan Khushi, sai dai ya kasa bayyana mata wani kuiɓin na Zuciyarsa yana shirin ɗarsa masa Dafin sonta. Sai da ta yi da gaske sannan ta rarrashe shi, tashi ya yi ya wuce sashinsa Zuciyarsa a dugunzume.

Aditya Buddha Daddynsa da ke zaune a gefe yana jin su sai lokacin ya samu damar tambayar ta manufar ta ta yin haka, cikin harshensa wato Hindi, da Yaren ta mayar masa da amsa bayan ta murmusa "Ina son shuka wa Moonath baƙin cikin da suka shuka min a rayuwa, ina son muzguna musu kamar yadda suka muzguna min; na lura Arjun ya yi nisa a cikin sonta amma ni ba hakan nake so ba, da zarar ya idar min da nufi na zan nesanta shi da ganinta, zan yi masa iyaka da ita, iya abinda nake buƙata shi ne raba ta da martabarta ta ƴa mace ta hakan ne kawai zan iya samun damar tarwatsa maƙiyana". murmushi ya yi tare da ba ta jinjina ba tare da tsoro ko shakkar ɓarnar da take shirin yi ba.

Mutsu-mutsu kawai yake yi a kan gadon, gabaki ɗaya ya kasa samun nutsuwa, suyar da Zuciyarsa take yi har ya shafi gangar jikinsa, shi ba zazzaɓi ba amma jikinsa ya ɗauki zafi raɗau!. damuwa da ƙunci sun zamo Abokan mu'amalarsa wai a hakan ma don yana ƙoƙarin kawar da su ta hanyar ci gaba da rayuwarsa faran-faran da mutane. Abubuwa da yawa sun yi haɗin gwiwa suna kawo masa sara da suka cikin fusata da son yaƙarsa, har yau bai dena jin zafin raba shi da Leelah da Haydar ya yi ba, haka zalika mugun furucin Mammi da ke yi masa sukuwa a Ƙwaƙwalwa da Zuciyarsa, ga baƙar ƙiyayya ta Zahiri da Haydar da Mahaifiyarsa ke nuna masa, ga Babban Amininsa wanda ya ɗauka tamkar ɗan Uwa ya kamu da son Ƙanwarsa wadda a yanzu hankalinta ya bar gangar jikinta sabida faɗawa tafkin son Azaan.

https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx

Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136
Chapter 32 · 0% Book details