Sashe 22
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sai da kyar aka lallaɓa ta ta zauna Mardiyya Yayar Abokin Salim ta yi mata kwalliyar Yaya Isuhu ya biya dubu biyu.
Ɗan Leshinta ta ɗauka ta maƙala ta koma bakin Gadon Umma ta ƙyafe, nan ma ta ce ko ƙofar takashi ba za ta je ba.
Ko da aka tashi tafiya Partyn Leelah ba yadda ba ta yi da ita ba a kan ta je ta ce ita fa ba ta san zancen ba, dole kowa ya haƙura ya bi ta da na Mujiya.
Leelah an sha kyau kamar ba za a Mutu ba, Yau jinta take tamkar a Ƙofar shiga Aljannah.
Kamar buɗar ido cikin ƙanƙanin Lokaci gidan ya zama ba kowa sai Umma da Momi, sai Salama, kowa ya ɗaware wajen Perty, har Inna da Mama cewa suka yi ba su ga ta zama ba.
Lokacin da suka dawo tuni Salama ta yi sahu tara a baccinta, sai da ta ji hayaniyar masu bayar da labarai sannan ta farka.
Wasu kusan kwanan zaune suka yi sabida tsabar surutu da mayar da yadda aka yi.
Tin sassafe Leelah ta sola wanka ta shirya cikin haɗaɗɗen Lesi kalar fari sai adon fulawa golden, mayafi golden da takalmi golden ta ɗora a kai, ta sha make'up na garari. Ta yi mugun kyau ko ɗan hassada ya ganta sai ya yaba ko ya yi shiru. Taku take irin na ƙasaita da jin kanta, yau girman kan nata ya ƙara girma don kuwa ba kowa take saurara ba, wasu ko kallon arziki ba ta yi musu.
Salma kuwa tinda ta tashi take jin gabanta na faɗuwa ba gaira ba dalili, gabaki ɗaya sai ta shiga damuwa ta nemi wuri ta tsakure ta fara sharɓa kuka.
Sai da ƙyar Umman Nabila ta lallaɓa ta gami da kwantar mata da hankali sannan ta shirya ta. Cikin lefenta Umman Nabila ta duba ta ɗauko wata shadda ƴar madaidaiciya kalar blue black, ɗinkin doguwar riga ne ya sha kwalliya tin daga sama har ƙasa, duk da ba wata me mugun tsada ba ce amma ta yi bala'in kyau da ɗaukar hankalin me kallonta.
Da rarrashi da lallaɓi ta saka ta don kuwa cewa ta yi Atamfar da Babanta ya ɗinka mata ita za ta saka, sai da kyar suka shawo kanta.
Ko Hoda ƙin yarda ta shafa ta yi bare ta zauna a yi mata make up.
Komawa ta yi can ƙuryar ɗan fulillikin Gadon Umma ta maƙale, sai ka leƙo ka koma ma indai ba ka mayar da hankali ba ba za ka san tana wajen ba.
Wasu irin tunani masu kama da mafarkai ne suke yi mata yawo a cikin kai, yau ne karon farko da ta fara jin rashin yarda da Aliyu har cikin ranta, haka kawai take jin tamkar ba da Zuciya É—aya zai Aure ta ba, ga wasu abubuwa da take gani da zarar ta rufe idanunta. Mayar da hankali ta yi kan Addu'a don ita ce maganin kowane irin rikici.
Biki ya yi Biki!, ko ina ya cika maƙil da ƴan uwa da Abokar arziki da ƴan sa ido da ƴan gulma, ko'ina ka zagaya kayaniya ake yi kamar a tashi Gidan.
Kowa farin ciki da murna yake yi, mafi yawanci kowa na maƙale a wajen Leelah da Mominta, tsoffi ne masu gudun hayaniya suke gangarowa wajen Umma su zauna sai danginta waɗanda suka zame mata dole, su kuwa dama ba yawa ne da su ba.
Kayan Abincin da aka haÉ—o da su a Lefen Leelah su aka zauna aka tsara girki na Æ´an ÆŠaurin Aure.
Abincin Æ´an biki kuwa Baban Salma aka bari da É—awainiya, shi ya shiga ya fita ya nemo É—an Geronsa aka markaÉ—o aka dama kunun safe, sannan ya nemo Æ´ar shinkafarsa ta hausa ya ce a dafawa Æ´an ÆŠaurin Auren Salma.
An sha turnuƙu a bakin Murhu, inda ɗaukar film za a yiwa abin sai dai Searise don ya fi ƙarfin a dunƙuleshi waje ɗaya.
Maza ma ba a barsu a baya ba, da Matasa da Magidanta na Unguwar da Yara, duk sun taru a ƙofar gidan Alhaji Usama sunan da bai taɓa amsawa ba Alhaji, yau mafi yawanci da shi ake kiransa. Abu ɗaya ne bai yi musu ba ƙarancin abinci don cewa suke yi kamata ya yi sai sun ci sun ture tinda Bikin na Manya ne.
Ƙarfe 10:00am Motar Gidan Abinci ta sauka a ƙofar gidan, nan fa aka ƙara tara ƴan kallo. Sai da ƙyar waɗanda suka kawo ɗin suka samu Baba Usama suka sanar da shi Alhaji Mustafa Naira ne ya yi order ya ce a kawo nan Gidan.
Farin ciki a wajen Baba Usama kasa ɓoyuwa ya yi, haka ya dinga ɓanshare haƙora kamar an ba shi tallar Makilin.
Sai da Momi da danginta suka yi da gaske sannan suka tseratar da Abincin daga farmakin Mutane.
Momi ta yi guɗa ta ƙara ya fi gaban ƙirgawa, tinda ta yi tozali da rantsatstsen Abinci kala-kala har da wanda ba ta taɓa gani ba kuma duk na bikin ƴarta sai ta ƙara tirewa, ji take ina ma da turmin zani ta goye Leelah ta yi rawa.
Haka aka ci gaba da hada-hada kamar ranar idi, sai dai a wajen majiÉ“anta Amare kallo ya fara komawa sama, Æangaren Haydar Æ™arfe 10:00am daidai aka yi da su za a É—aura Aure, a É“angaren Aliyu kuma 11:00am, gashi yanzu an buÉ—i ido 01:00pm har ta wuce babu labarin kowane É“angare.
Haydar na kwance kan makeken gadonsa yana shaƙar bacci, Budurwarsa Alina tana zaune kusa da shi daga ita sai pant da bra, ta zuba masa idanunta wanda suke nuna alamar kukan da ta mazga, abubuwa da yawa take rayawa a Zuciyarta, tabbas don dai ya ce mata ba son Leelah yake yi ba bayan an yi Auren zai saketa da ba abinda zai hana ta tarwatsa Auren ko ta halin yaya ne ko da kuwa hakan na nufin za ta kashe Leelah ɗin.
A hankali ya fara buɗe idanunsa wanda suka yi bala'in nauyi, yana buɗe su ya ɗora a kanta, bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba.
Zazzaro ido ta yi a razane, sam ba ta yi zaton farkawarsa a wannan lokacin ba, ta so sai yamma liƙis ko dare zai farka ta yadda dole lokacin an fasa ɗaurin Auren, musamman da ta ga ya yi wannan murmushin me kama da na gayya ko mugunta sai jikinta ya ƙara yin sanyi.
Yunƙurawa ya yi ya zauna kafin ya janyo towel ɗin da ke kusa da shi ya ɗaura a ƙugunsa, ido ya zuba mata kamar yadda ita ma ta zuba masa, wani irin kallo suke yiwa juna me cike da ma'anoni masu yawa.
Anya kuwa zan iya bari ya je a É—aura Auren nan?, gaskiya dole na samo mafita, dole ne na sa ya koma baccin nan, dole ne na san abin yi. Ita da Zuciyarta suke shawarwari.
Shi kuwa tunani yake yi dole ne ya yakice ta ya fita don ba zai bari damarsa ta kufce masa ba, indai har bai halacci wurin Ɗaurin Auren ba Bhaba zai iya sauya akalar komai ta koma kan Aliyu, wani gefen kuwa dariyar mugunta yake yiwa Alina, duk ta bi ta susuce akan Kishinsa shi kuwa sam ba ya jin zai iya yin kishinta don ita ba komai ba ce gare shi face abar ƙore ƙishi.
Miƙewa ya yi cikin rashin ƙwarin jiki ya nufi toilet domin watsa ruwa.
Tana tabbatarwa ya shige ta tashi ta ɗauko ƴar jakarta tare da lemon da ta san yana sha da cup, tsiyayawa ta yi a cup ɗin sannan ta ciro wasu ƴan ƙwayoyi a Jakarta ta ɗauki guda uku ta watsa a ciki, komawa ta yi ta ƙyafe tana ƙissima irin kyakkyawar tarba me jan hankali da gusarwa da za ta yi masa in ya fito.