← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 35

Sashe 28

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Salama Alaikum, Farar Mace Alkyabbar Mata, Barbela me Fari daga Allah, Macen da ake kira Sa'a ba me neman Sa'a ba, duk wanda ya Aureki ya wuce raini!!!!" Salim ne ke maganar yayin da ya kutsa kai cikin Gidan. Turus!! ya tsaya yana kallon Aliyu wanda ya yi wujiga-wujiga idanunsa sun yi ƙulu-ƙulu, fashewa ya yi da dariya gami da cewa "Ikon Allah ba ya ƙarewa a Duniya, yau ga abin mamaki Me Gari Gwauro, Talaka da Mata Huɗu!!!, to kai in ba Karambani ba me ya kai Doki Mahauta??".
Aliyu ya ce "Sannu da zuwa, wallahi Wutar ce ta ƙi kamawa". Salim ya ce "To wai kai tsaya!, ina kai ina shiga tsarar Mata?? ko an gaya maka a banza suke girkawa ka ci?, Mace fa ba sa'ar kwaikwayonka ba ce ehe!!!" "Aliyu ya ɗan yi dariya gami da cewa "Gaskiya dai kunna Wutar akwai wahala, na yi zaton zan iya ne, kuma fa na iya kunna wuta don har girki ina yi, kawai dai Gawayin ne ba shi da kyau".
Salim ya sa dariya da shewa yana cewa "Ahahahayye!!!! aikin banza harara a duhu, to ai yanzu in kana tunanin da sauƙi sai ka dena, ƙila kai ta icce ka iya kunnawa ka san an ce kowane tsuntsu da Kalar Kukansa, yanzu sai ka tashi ka bawa Mata Filinsu don wannan ba huruminka ba ne kawai dai karambani ne irin na Ƙartai!!".

Aliyu zai yi magana sallamar su Umman Nabila ta katse shi, sannu da zuwa ya shiga yi musu cike da girmamawa. Su kansu sun yi mamakin ganinsa a haka amma ba su ce komai ba, gaishe su ya yi suka amsa gami da shigewa ciki.
Salim ya ce "To wai kai tana ina??" "Tana ɗaki tana bacci". "To wallahi durƙusa ka ci gaba da kunna Wutar nan a to!, Salama ba ta baccin Rana tinda Allah ya sa yau ta rintsa ba ka isa ka tasheta ba" "To ai inda zan tashe ta da tin kafin ka zo zan tashe ta Ƙanina!" Salim ya taɓe baki gami da cewa ''Hum-um!! wai kai na yi maka kama da Jarirai ne da za ka dinga kirana ƙaninka?, Aunty Salma fa na san ta girmeka kai dai akwai ka da tsaurin Ido, ni daga yau ma Yaya Salim za ka dinga Kirana a to!!" ya ƙarasa maganar tare da buga cinya yana yin fari da ido.
Aliyu ya ce "In kana so sai in ce maka Yayan amma fa ka san dai ni Yayanka ne tinda har na zama Mijin Yayarka, ba ka ji ana cewa Kowa Iya ta Aura Baba ne ba?? to ai kamar haka ne". "Cab!! ai kuwa ni ban yarda da wannan izalar da ba Gemun ba" ya faÉ—a yana mummurguÉ—a baki.
Sokanabe suka ci gaba da yi basu san ma wutar ta kama ba sai daga baya suka lura ta ruru kamar za ta ci babu. Aliyu ya washe baki yana cewa "Da ka ce ban iya ba! gashi yanzu idonka ya gani yadda na kunna ta ko Yayar taka ma albarka" "Hakacin!!!, haka na gani a Jarida, wallahi kawai Arashi ne, Allah dai ya dubi idanunka da suka sha hayaƙin nan suka yi luƙu-luƙu ya bawa Wutar izinin kamawa amma ba don ka iya ba."
"Na dai rabaka!, yanzu bakin tsanya ya mutu, in ni ne kai ma ba zan ƙara cewa uffan ba sai bayan kwanaki" Aliyu ya faɗa tare da nufar Kicin don ɗauko Tukunya.

https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx

Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136

SHARE FISABILILLAH

*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632*

*©️INDO*
[12/10, 7:46 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
18

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

FREE PAGE...........

"Ke haka ake yi kin bar ɗan Mutane sai azabtuwa yake yi da hayaƙi?? me ya jaza miki bacci yanzu da ranar Allah?" Baba Zuwaira ta faɗa fuska ba alamun wasa. tsilli-tsilli ta yi da ido ta rasa abin cewa, sai yanzu ma ta tuna wai ta bar Aliyu yana shirin kunna wuta.
Umman Nabila ta ce "Allah Sarki bawan Allah, gaskiya da alamunsa yana da tausayin Mace, ai ba kowa ne zai zauna kunna miki wuta ke kuma ki yi bacci ba".
Yaya Rahina ta ce "Wallahi fa ni ma haka na gani, ke dai da yardar Allah kin samu Miji mai hankali, don haka ki rungumi abinki hannu bibbiyu kar ki bari zigar Mutane ta yi tasiri a kanki, yanzu martabar Ƴa Mace ita ce Gidan Mijinta ba zaman sakarcin da Ake yi a Gudanku ba." Umman Nabila ta watsa mata daƙuwa tana cewa "Uwaki!, ina ruwanki da zamansu, Aure ai sai lokacin ya yi ko?" Baba Zuwaira ta ce "Ke barta ta faɗi gaskiya, ai hakan suke, ni dai na kasa yarda ma da imanin wannan Ƴa Sumayya, dukkansu ma Yaran nan Girarsu a tsaitsaye kamar nonon Namiji". Dariya suka sa Yaya Rahina ta ce "Kina da gaskiya Baba Zuwaira, daɗina da ke fa akwai iya zaro magana!"
Ta taɓe baki tana cewa "A to!" Hira suka ci gaba da yi kowa na tofa albarkacin bakinsa, Salma tuni ta sallallaɓa ta fice don ganin Aliyu da Girkin nasa a halin da suke ciki.

Suna zaune suna gyaran Kayan Miya shi da Salim ta fito tana ta muzurai, daga gefe ta durƙusa cikin sanyi ta ce "Ka yi haƙuri bacci ne ya kwashe ni". "To ai ni na ce zan yi ko?" "To amma yanzu ka bari in yi, ga Nabila can ma na san za ta taya ni". amsawa ya yi tare da zare jikinsa ya tashi, bayan gajiya dama so yake ya bar musu Gidan don su fi samun damar sararawa.
Sallama ya yi mata sannan ya tafi.

Salim ya gyara zama yana cewa "Yawwa, gwara da ya tafi ya bamu sarari don wallahi cikina cike yake taf da labarai ko wurin sa Abinci babu". Dariya ta yi tana cewa "Allah Mutumina!! ai gaskiya na ji daɗin ganin ka, ban zata za ka zo ba ai" "Haba dai ke ma kin san ai ni da ke tif da taya ne, Amana ai ta fi ƙarfin wasa, ni wallahi a kan Abin Duniya ba zan ƙi zuwa gidanki in je gidan Leelah ba, Uwar me za ta ba ni?"

"Daɗina da kai bakinka ba sakata shi yasa kuke yawan faɗa da Momi" Ta faɗa tana harararsa, taɓe baki ya yi gami da cewa "Ai wallahi na fi ta gaskiya kuma; jiya fa sai ƙarfe ɗaya saura suka dawo Gidan nan, kin ga Inna da Mama yadda suka dawo zani a hannu?, Umma Rakiya sai fyace majina take tana ƙarawa wai AC ya sa ta mura, ni kuwa na ce Allah ya ƙara, wallahi duk haushi suke ba ni, shi ma Shegen Mijin nata mai kama da Guntun Man Kitso, ke ni ai jiya na ga tijara ganin Idona". da sauri Salma ta ce "Kai dena zaginsa don Allah" "To a na me??" ya faɗa yana zaro idanu, "Sabida Yayan Ali....." saurin cin burki ta yi tana zaro ido wuƙi-wuƙi kamar ta yiwa Sarki Ƙarya, "Ƙarasa mana, Ya-ya me??" waskewa ta yi ta ce "Sabida Yayanka ne, sannan kuma sunan su Ɗaya da Mijina". wani farrr!! ya yi da ido kamar wanda aka jonawa wutar lantarki, cike da iyayi da feleƙe ya ce "Wa?! Allah ya huwaɗe ya zama Yayana, ke ni fa wallahi ko Hasan da Usaini muka fito ni da shi ba abinda zai hana ni Zaginsa, Ɗan Butar Duma!!". "To ai sai ka ci gaba ɗan rainin hankali" ya ci gaba da cewa "Oho dai, ina ba ki labari ai burin Mama ya cika su Rabi'a sun yi samari sun fi kala ashirin in gaya miki, shi yasa dama ta shiga ta fita ta fito da su rass!! kar ki ga yadda idanunsu suka ƙara buɗewa wallahi" Salama ta ce "Kai haba!!, ni fa wallahi da ma Auren su suka yi su huta, wai su ba sa tunanin Zalumtar Samarin nan da suke yi Zunubi suke ɗauka?" watsa hannuwa ya yi gami "A to!!!!, ni ma dai abinda nake gani kenan, sai dai mu ce Allah ya kyauta, wai kin san yau ma suna can suna dodon zuwa Gidan Leelah? ai in gaya miki da aka ce za a zo nan yau ma cewa suka yi su fa Gidan Leelah suka nufa, na ce Ala raka taki gona mu dama ba nemansu muke yi ba". murmusawa kawai Salma ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Ci gaba ya yi da kawo mata labarai wasu ta kula wasu kuma ta yi dariya ko murmushi.

Sai yamma Liƙis sai ga su Umma Rakiya tinjin-tinjin tare da Yaya Hasiya da Yaya Badi'a.
Ba su wani daÉ—e ba su Umman Nabila suka tashi tafiya suka rankaya suka bi su.

Ita kaÉ—ai ta ci gaba da zazzare ido a Gidan har bayan Magrib sosai sannan Aliyu ya dawo yana zuwa suka wuce ba tare da jira ba.

Ƴan Biki tinda suka dawo suke zuba Tijara a kan Leelah ta wulaƙanta su ta yi musu rashin Mutunci, waɗanda suka ƙara kwana a Gidan sai da suka raba dare suna yamaɗiɗi da zancen. Momi sai hura hancika take yi don ita ba ta ga laifin Leelah ba, a cewarta matsayi matsayi ne in aka fi ka an fi ka.
Salim kuwa ya yi dariya har ya godewa Allah, duk inda ya zagaya jefar musu magana yake yi, sai da Suka ritsa shi da masifa suka kusa yi masa na jakkai sannan ya haƙura da maganar ya koma gefe ya dinga tuntsira dariya.
Chapter 28 · 0% Book details